Ɗan wasan Madrid, Isco, na shirin ƙulla yarjejeniya da Barcelona

A karon farko cikin kusan shekaru 15, ana shirin samun sauyin sheƙar ɗan wasa kai tsaye tsakanin manyan abokan hamayya a gasar La Liga, wato Real Madrid da Barcelona FC.

Rabon da a ga irin wannan sauyin sheƙa dai tun shekara ta 2007, lokacin da Javier Saviola ya koma Real Madrid daga Barcelona.

A halin yanzu kuma ɗan wasan tsakiyar Real Madrid, Isco Alcaron, ke shirin sauyin shekar zuwa Camp Nou.

Tuni dai aka tsegunta cewar har ma Isco ya gana da kocin Barcelona Xavi Hernandez.

Ɗan wasan mai shekaru 29 a yanzu shi ne na 5 a matakin muhimmanci tsakanin ’yan wasan tsakiya na Real Madrid da suka haɗa da Toni Kroos, Luka Modric, Federico Valverde, da kuma sabon ɗan wasa Eduardo Camavinga, abin da ya sa a kakar wasa ta bana, wasanni 9 kawai Isco ya buga a ƙarƙashin kocinsa Carlo Ancelotti, wanda ga dukkanin alamu ɗan wasan baya cikin tsarinsa.

A cikin watan Yunin shekarar nan yarjejeniyar Isco za ta ƙare da Real Madrid, lokacin da ake sa ran zai koma Barcelona.

Wasu majiyoyi a Spain sun ruwaito cewar, dama can Isco Alcaron magoyin bayan Barcelona ne na bugawa a jarida, tun ma kafin ya ƙulla yarjejeniya da manyan abokan hamayyarsu a shekarar 2013.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *