2023: Babban kuskure ne mu miƙa mulki ga ‘yan Kudu, cewar Hon. Kwacam

Daga AISHA ASAS a Abuja

Jigo a jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, kuma shugaban ƙungiyar yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, wato Movement of North East Organization Forum, Hon. Alhaji Abdulrahman Buba Kwacam, ya bayyana cewa babban kuskure ne ga ‘yan arewa su zaɓi mutumin da wata jam’iyya ta tsayar daga kudancin ƙasar nan da nufin zamewa shugaban ƙasar Nijeriya a zaɓe mai zuwa na 2023.

Kwacam ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya kira a gidan sa da ke Abuja ranar Alhamis ɗin makon jiya, inda ya nuna tsananin damuwar sa dangane da yanayin da arewacin ƙasar ke ciki, na kashe-kashe da tashe-tashen hankulan da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a dukkan sassan arewacin ƙasar.

Tun da farko dai, Hon. Kwacam ya bayyana maƙasudin da ya sa suka kira taron manema labarai shine don su fargar da al’ummar Arewa su kuma tashe su daga barci tare da yi musu nuni da bala’in da ke tunkarar yankin musamman idan aka yi la’akari da babban zave mai ƙaratowa.

Ya ce ya kamata al’ummar arewacin ƙasar nan su san abinda ke musu ciwo da kuma tantance irin mutanen da ya kamata su jagorance su a ƙasar, domin “ba talaka ba ne a gaban masu mulki,” a cewar sa, inda ya yi kira ga talakawa da su ƙaurace wa ‘yan siyasar da ke ba su dubu ɗaya ko ɗari biyar su sayar da ‘yancin su na shekara huɗu. Kwacam ya gargaɗe su da su yi hattara, domin a cewarsa “guba ta fuskanci Arewa, kuma gubar nan ba ta tsaya ga ƙauye ba kaɗai, za ta shiga birane matuƙar hankalin ‘yan Arewa bai dawo jikin su ba,” a cewarsa.

“Ya kamata mu faɗa wa kan mu gaskiya, mu daina yaudarar kanmu don biyan buƙatarmu, da kuma jefa wasu bayin Allah cikin bala’i a cikin ƙasar nan.

“Kowa ya san halin da muke ciki na tashe-tashen hankula yau a arewa da kuma yadda babban zaɓe ya ƙarato, wanda ba talaka ba ne a gaban, sannan ba Arewa ba ce a gaban mu gaskiyar magana.

“Saboda haka ina son in tabbatar wa da ‘yan uwana ‘yan siyasa musamman shugabanni, wato malaman addini da sarakunan gargajiya da sauran talakawa waɗanda ba su san ‘yancin su ba.”

Hon. Kwacam ya ƙara da cewa bala’in da ya tunkaro Arewa a yau, ya wuce min sharrin, zaman lafiya ya ƙaura, wanda kuma zai iya mamaye dukkan jihohin yankin matuƙar ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

“Mun mun san abinda ya faru da mu a Arewa maso Gabas, mun san tashin hankalin da muka gani. To shi ya sa muke ta bayani domin mutane su san abinda ke ɓoye a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya. Saboda haka idan ba mu yi hankali ba, babu jiha ɗaya da za ta rage a Arewa, ya kamata kowa ya san wannan.”

A ci gaba da bayaninsa, Kwacam ya yaba wa Shugaban Ƙasa Mujammadu bisa jajircewar sa, inda ya ce “ba za a san alfanun Buhari ba sai ranar da ya bar mulki.”

“A yanzu mu muke da Shugaban Ƙasa, kuma duk manyan muƙaman da muke da su ‘yan Arewa ne, amma ba a kawar da matsalar tsaro ba. To me muke zato idan mulki ya bar hannun mu ya koma Kudanci alhali Arewa tana cikin mawuyacin hali. Wallahi ko mu yarda ko kada mu yarda, duk wani Musulmi da Kirista a arewacin ƙasar nan sai ya bar gidan sa,” inji shi.

Gogaggen ɗan siyasar ya yi nuni da cewa, ba maganar siyasa ake yi ko APC da PDP, ko kuma ɓangaranci, inda ya nuna rashin amincewar sa kan mulki ya koma Kudancin ƙasar; har yana bayyana wanda ke goyon bayan haka a matsayin “maras hankali da tunani.”

“Mu ba yara ba ne, muna da hankali muna kuma da tunani, ƙasar nan tamu ce, ba mu da wani wuri da ya wuce Nijeriya. Idan ni Ina da kuɗin da zan ɗauki ‘ya’yana da matana in bar Nijeriya, Ina da ‘yan uwa da ƙanne da abokai. Kowa haka yake da su. Ba za mu dinga saka al’ummar ƙasar nan cikin masifa da bala’i ba. Idan babu su ta yaya za mu iya gudanar da mulkin, wa za mu mulka?

Saboda haka, ya ce dole ne a tashi tsaye, idan har talaka zai iya haƙuri ya je ya yankin katin zaɓe, ya yi haquri da ƙishirwar da yake ji, ya je ya sayi kati don ya tura wa Shugaban Ƙasa Buhari a wancan lokacin, to ya zama wajibi a yanzu ma ya jajirce don ceto Arewa daga bala’in da take ciki a yanzu.

Kwacan da yake ƙara nuna tsananin ɓacin ransa kan yadda arewacin ƙasar ya zama sansanin kashe bayin Allah, ya ce ba za su tsaya suna ganin ana sayar da rayukan mutane su yi shiru ba.

“Mu ba ‘yan iska ba ne, ba za mu dinga sayar da rayukan ‘ya’yan mu da ‘yan uwanmu a banza a wofi ba don biyan buƙatar mu,” inji shi.

Da ƙarshe ya sake jaddada goyon bayan sa tare da yin kira ga ɗaukacin arewacin Nijeriya da su ƙaurace wa zaɓen duk wani ɗan Kudu a kowace jam’iyya ya fito, inda ya yi nuni da cewa, “yanzu fa ɗan mu ne da ‘ya’yan ne suke kai, amma an gagara shawo kan matsalolin da ke addabar Arewa. Kuma kar ka ce wasu ne daban, a’a da ‘ya’yan mu ake yi. To mulkin nan ya bar Arewa ya koma Kudu. To ka isa ka fita ka faɗa wa shugaban ana kashe mutum a Kaduna, Katsina, Zamfara ko Sakkwato ko a Borno?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *