A ganina ƙungiyoyin marubuta ba su da wani tasiri – Hafsat Rano

“Akwai bambanci tsakanin rubutun fim da na zube”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Rubutu babbar baiwa ce da ba kowa ke samunta ba, sai wasu ƙalilan daga cikin mutane. Ko su ma marubutan za ka tarar kowa da irin hikima ko basirar da yake da ita wajen zalaƙar sarrafa harshe da fikirar jawo hankalin mai karatu, da riƙe tunanin sa har sai ya kammala karanta saƙon da ake son isar masa. Hafsat Kabir Umar da aka fi sani da Hafsat Rano daga Jihar Kano na daga cikin irin marubuta ýan baiwa da Allah ya yi wannan babbar kyauta. Tun tana yi a ɓoye ba a sani ba a gidansu har aka gano abin arziƙin da take ɓoyewa, zuwa lokacin da ta samu cikakken goyon baya daga ahalinta, har dai gashi yanzu da tauraruwarta ke haskawa. Tana cikin zaratan mata marubutan nan da ake yi wa laƙabi da Zafafa Biyar, saboda ƙwazon su da basirarsu. Wakilin Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya zanta da wannan matashiyar marubuciya kan rayuwarta da abin da ya bambanta rubutunta da na sauran marubuta mata na yanar gizo! Ga yadda hirar tasu ta kasance.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

HAFSAT RANO: Assalamu alaikum wa rahmatullah. Sunana Hafsat Kabir Umar, wacce aka fi sani da Hafsat Rano a kafafen sada zamunta. Ni marubuciya ce. Matar aure, kuma uwa.

Ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice?

An haife ni a garin Kano a Unguwar Hotoro. Na yi karatuna na firamare da na sakandire duk a nan Hotoro. Daga nan na tafi Jami’ar Bayero inda na samu digirina na farko a fannin nazarin halittu, wato Bsc Applied Biology. Na yi Diploma a vangaren sarrafa na’urar Kwamfiyuta. A ɓangaren addini kuma, na yi karatun Islamiyya, kuma har ma na yi sauka.

Yaushe ki ka fara sha’awar rubuce rubucen Hausa?

Na fara sha’awar rubuce-rubucen Hausa tun karatu a matakin Sakandire a shekarar 2011, lokacin ina rubutawa a littafi. Sai dai ban yi nisa sosai ba na dakatar, sai a 2016 na fara rubutu na sosai, sakamakon fara amfani hanyar zaurukan sada zumunta, inda na rubuta littafi na farko, ‘Guguwar So’.

Waye ya fara nuna miki abin da ya kamata ki yi a farkon rubutunki?

Gaskiya babu. Sai dai akwai marubuta biyu da na karanta littattafan su a lokacin, waɗanda suka zamar min kamar wani madubi ko tsani na fara rubutuna. Waɗannan marubuta kuwa su ne, Jamila Umar Tanko, da kuma Afrah Bhai. Gaskiya na amfana sosai da rubuce rubucensu, kuma hakan ya taimaka min wajen fara rubutuna.

Ko za ki ƙara mana bayani kan abubuwan da suka ja hankalin ki ga rubutun su?

Littafin Jamila Umar na ‘Yarena Addinina’ a lokacin shine ya ja ra’ayina, na fara rubuta nawa a takarda ni ma, sai dai ban kai ga ƙarasawa ba na watsar saboda ban samu goyon baya daga gida ba, sai daga baya bayan an fara na online a sannan na karanta ‘Ýar Talakawa’ na Afrah Bhai. Labarin ya yi matuƙar daɗi ya kuma ja hankalina sosai, har ni ma na samu damar yin nawa. Duka littattafan sun yi daɗi, haka kuma sun faɗakar.

Wanne ƙalubale ki ka fuskanta a farkon zaman ki marubuciya?

Gaskiya babu wani ƙalubale da na fuskanta a farkon fara rubutuna, sai dai daga baya na fuskanci matsala ta ido sosai wadda har ta yi min sanadiyyar fara amfani da tabarau.

Kawo yanzu littattafai nawa ki ka rubuta?

Na rubuta littattafai guda goma sha biyu. Huɗu na kyauta ne sai takwas na kuɗi. Littattafan su ne, ‘Guguwar So’, ‘Farin Cikina’, ‘Alƙawari Bayan Rai’, ‘Ruhi Ɗaya’, ‘Sauyin ƙaddara’, ‘Ɗaurin Goro’, ‘Abinda Ke Cikin Zuciya’, ‘Mabuɗin Zuciya’, ‘Halin Girma’, ‘Rayuwar Mace’, ‘Sanadin Labarina’, sai kuma ‘Rumbun Ƙaya’.

Kin tava buga littafi, ko ke ma a online ki ke fitar da littattafanki?

Ban taɓa bugawa ba. Iyaka online ne kawai nake fitarwa.

Wacce riba ki ke samu dangane da rubuce rubucenki?

Alhamdulillah! Gaskiya ribar da na samu dangane da rubutu ba za ta ƙirgu ba, sai dai kawai mu yi hamdala ga Allah. Alhamdulillah. Na yi imanin idan har ka gyara ka tsaftace rubutunka to, tabbas za ka ga alherin haka. Babu shakka rubutu sana’a ce mai kyau. Sannan za ka haɗu da mutane da yawa masu nagarta, wannan kaɗai ma nasara ce babba!

Yaya mu’amalarki take da masu bibiyar littattafanki? Kuma ta yaya ki ke sanin ra’ayinsu kan littattafanki?

Akwai kyakkyawar mu’amula tsakani na da makaranta littattafaina. Domin dai dole sai da su sannan rubutun zai tafi yadda ya kamata. Idan har baka da kyakkyawar mu’amula da makaranta to, babu amfanin ma yin rubutun gaba ɗaya gaskiya. Sannan ina sanin ra’ayoyin su ne hanyar abin da ake cewa a sashin tsokaci, sai kuma ta hanyar kiran waya da wasu ke yi da kuma tura saƙo.

Kin taɓa yin wani rubutu da ya zama miki alaƙaƙaƙai wanda ba za ki manta da shi ba?

A’a, Allah ya tsare ni, gaskiya ban taɓa ba.

Wanne irin nau’in rubutu ki ka fi mayar da hankali a kai tsakanin soyayya, zamantakewa, almara, ko rayuwar auratayya?

Ko’ina ina taɓawa, babu waɗanda da bana tavawa. Domin shi marubuci a duk lokacin da ya ɗora alƙalaminsa domin yin rubuta, zai iya tava kowa da komai, matuƙar ɓangaren da zai yi rubutu a kai mai amfani ne da faɗakarwa ga al’umma.

Yaya mu’amalarki take da sauran marubuta ýan’uwanki? Kuma su wanene aminanki da ku ka fi mu’amala tare?

Alhamdulillah! Akwai kyakkyawar alaƙa tsakani na da sauran ýan’uwana marubuta, sai dai nafi mu’amula da mutane huɗu waɗanda nake da kusanci sosai da su a harkar rubuta. Akwai Miss Zozo, Billyn Abdul, Safiyya Huguma da Mamugee.

Waɗannan su ne na fi kusanci dasu sosai a cikin marubuta kuma muka fi mu’amula da su a kodayaushe. Har ma wani ƙawancen haɗakar rubutu muka shirya, wanda har muke wa kan mu laƙabi da Zafafa Biyar.

Wanne goyon baya ki ke samu daga iyalinki game da rubutun da ki ke yi?

Alhamdulillahi, yanzu kam ina samun goyon baya ɗari bisa ɗari daga ɓangaren iyayena har da maigidana, kuma suna matuƙar taimaka min da bani ƙwarin gwiwa, har ma su taimaka min da abinda ya shige min duhu.

Shin kina da aure? Yaranki nawa?

E, ina da aure da yara biyu, mace da namiji!

Menene ra’ayinki game da ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da yaɗuwar rubutun batsa?

Alhamdulillah! Wannan wata hanya ce da za ta taimaka ƙwarai wajen daƙile ire iren waɗannan rubuce rubucen da wasu marasa tsoron Allah suke yi saboda neman suna. Babu yaƙi da yaɗyuwar rubutun batsa ƙuduri ne mai kyau kuma muna goyon bayan hakan ɗari bisa ɗari.

A ina ake iya samun littattafanki? Ko kina amfani da manhajojin sayar da littattafai?

E, ana iya samu. Akwai a manhajar Arewabooks da muke ɗora littattafanmu za ka iya samu na ta hanyar binciken sunana #hafsatrano ko sunan ɗaya daga cikin littattafaina. Sannan za a iya samun littattafaina ta manhajar WhatsApp kai tsaye ta lambobinmu da muke amfani da su.

Ta yaya za a samu haɗin kai da cigaba a tsakanin marubutan online?

E, to! Duk da kasancewar yanzu marubutan online sun yi yawan gaske da zai yi wahala sosai wajen samun hadin kan kowa da kowa. Sai dai ina ganin kamar idan kowa ya ajiye bambancin raayinsa da ƙungiyarsa ya zo a haɗa ƙarfi wajen daƙile ɓatagarin marubuta, sannan a samar da wani shugabanci da zai riƙa bibiyar marubutan saboda duk wani abu da babu shugabanci za ka ga yana tafiya ne ba bisa ƙa’ida ba, ina tunanin idan aka yi hakan za a samu haɗin kai sosai sannan za a gyara harkar rubutun musamman saboda gaba.

A wacce ƙungiyar marubuta ki ke?

Bani da ƙungiya a halin yanzu gaskiya, duk da dai muna rubutu mu biyar a tare har kuma muna kiran kanmu da Zafafa Biyar, sai dai ba ƙungiya ba ce. Na dai taɓa zaman Ƙungiyar Haske Writers Association a shekarun baya.

Wanne tasiri ƙungiyoyin marubuta suke da shi, wajen inganta rubutun mambobinsu?

A ganina ƙungiyoyin marubuta ba su da wani tasiri gaskiya.

Wacce shawara za ki bai wa matasan marubuta da ke sha’awar fara rubutun adabi?

Su tsarkake alƙalaminsu. Sannan su bi komai a sannu ba tare da sun saka dogon buri ba.

Shin kin taɓa sha’awar rubutun fim? Wanne bambanci ki ka lura da shi tsakanin rubutun zube da na fim?

E, tabbas! Ina da sha’awar rubutun fim. Bana mantawa musamman na ware lokaci a baya domin sake samun sani game da yadda rubutun yake da kuma ƙa’idojin da suke tattare da shi. Daga baya ne na watsar da abin na mayar da hankali na kacokam a kan rubutun zuben. Amma babu shakka akwai bambanci sosai tsakanin rubutun zube da na fim, don tsarin rubuta su ma sam ba ɗaya ba ne. A rubutun fim ana buƙatar ka fitar da komai daki daki yadda masu kallo za su ga komai a zahirance ba kamar rubutun zube ba da ba komai ne yake buƙatar bayyanawa ba.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Wani Hanin Ga Allah Baiwa ne!

Na gode.

Alhamdulillahi. Ni ma na gode.