Al Mustapha ya shawarci Yahaya kan matsalar tsaron ƙasa

Daga AISHA ASAS

Manjo Hamza Al Mustapha (Mai murabus) ya shawarci sabon Babban Hafsan Hafsoshi, Manjo Janar Faruk Yahaya, da ya kawo ƙarshen Boko Haram cikin taƙaitaccen lokaci.

Al Mustapha, wanda shi ne tsohon shugaban tsaro ga tsohon shugaban ƙasa marigayi Janar Sani Abacha, ya bayyana hakan ne ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce wajibi ne Yahaya ya gaggauta kawo ƙarshen ta’addancin da ya yi sanadiyyar hasarar rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasa.

A cewarsa, “Jinkiri wajen kawar da Boko Haram wani babban koma baya ne ga Nijeriya. Mafi alheri ga ƙasa, shi ne hanzarta kawar da su.

“Gaggauta kawar da su abu ne mai muhimmanci ga ƙasa saboda yaƙin ba kamar irin yaƙin da aka sani ba ne, Nijeriya za ta farfaɗo idan aka yi haka.

“Ni na san hakan abu ne mai saɓuwa saboda na ɗan yi nawa bincike a kan haka.”

Al Mustapha ya ci gaba da cewa, “Yahaya ƙanenmu ne, na yi masa addu’a tare fatan alheri dangane da samun muƙamin nasa.

“Na yi magana da shi na kuma aika masa da saƙon tes kan samun nasara. Akwai hanyoyin samun nasara da dama a gare shi wajen daƙile matsalolin da suka addabi ƙasa.”

Al Mustapha ya shawarci sabon shugaban sojojin da ya haɗa kai wajen yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da sa’ar fatattakar ‘yan ta’adda da ta’addanci a faɗin ƙasa.

Ya ce a saninsa, tun somawa zuwa yau Boko Haram sun shafe shekara 20. Ya ce muddin ana son kawar da irin wannan matsalar tilas ya zamana ana da cikakken bayani kan harkokin ‘yan ta’addan ciki da waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *