Amurka ta fusata da hukuncin WTO na ba Chana damar sanya mata haraji

Amurka ta bayyana takaicinta dangane da hukuncin Hukumar Kasuwanci ta Duniya da ya sahalewa Chana damar iya lafta mata harajin dala miliyan 645 kan cinikayyarsu a kowacce shekara.

WTO ta bai wa Chana damar ɗaukar fansa wajen karɓar harajin har na dala miliyan 645 kan hajojin da Amurkan ke shigar mata da su ƙasar a duk shekara, hukuncin da ke biyo bayan rikicin kasuwancin da manyan ƙasashen biyu mafiya ƙarfin tattalin arziki suka jima suna yi da junansu.

Wasu bayanai na nuna cewa an kai ga wannan matsaya ne bayan tafka doguwar muhawara a mabanbantan lokaci da ya kai ga sahale wannan mataki.

Sai dai bayan tsayar da adadin harajin, Chana ta nemi hukumar sasanta rikicin kasuwanci ta shiga tsakani don daƙile duk wata barazana da ka iya sauya hukuncin na harajin dala miliyan 645.

Tuni hukumar kasuwanci ta Amurka ta bayyana matuƙar damuwa a hukuncin da ta kira mai cike da rashin adalci tare da bayyana aniyarta ta samar da mafita.

Tun a shekarar 2012 ƙasashen biyu suka fara taƙaddama kan harajin, ko da yake zuwan Donald Trump mulkin Amurka ya mayar da taƙaddamar zuwa gagarumin rikici ta yadda ɓangarorin biyu suka riƙa musayar manyan haraji tsakaninsu.