Amurka ta haramta wa wasu ‘yan Nijeriya biza saboda yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Ƙasar Amurka ta sanar da kafa wa wasu ‘yan Nijeriya takunkumin biza bayan da ta zarge su da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa.

Ƙaramin Sakataren Amurka, Antony Blinken ne ya bayyana hakan ranar Laraba.

Blinken ya ce akwai yiwuwar wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa a haramta musu shiga ƙasar baki ɗaya.

Ya ce, “Muna ƙoƙarin ganin mun mara wa dimokuraɗiyya baya a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

“A yau, ina sanar da hana biza ga wasu ‘yan Nijeriya saboda yi wa tsarin dimokuraɗiyya zagon ƙasa a zaɓen ƙasar na baya-baya nan,” in ji shi.

Amurka ta ce, haramta bizar ta shafi wasu ne amma ba duka ‘yan Nijeriya ko Gwamnatin ƙasar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *