An gano yaron da Sanata Ekweremadu da matarsa suka yi safara zuwa Birtaniya don cire ƙodarsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An samu wata shaida dangane da yaron da tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya da matarsa Beatrice, da ake zargi da yin safararsa zuwa ƙasar Birtaniya don cire ƙodarsa.

Idan za a iya tunawa dai jami’an ‘yan sandan ƙasar Birtaniya sun damƙe tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Ike Ekweremadu tare da mai ɗakinsa Beatrice akan yunƙurin cire sassan jikin yaro.

Kazalika, sashen ƙwararrun ‘yan sandan ƙasar sun miƙa waɗanda ake tuhumar zuwa kotu a birnin Landon don gudanar da bincike. 

Yaron wanda ba a san sunansa ba, ba kuma a ga hotonsa ba, wakilin Arise TV, Adeyemi Akinsaya a ranar Alhamis 23 ga Yuni 2022 ya bakanɗo wani abu daga yaron da aka yi safarar shi zuwa Birtaniya. 

A cewar Akinsanya, ƙaramin yaron ɗan kimanin shekara 15 wanda aka ɗauko shi daga Legas, Kudu maso Yammacin Nijeriya.

Kamar yadda ya ambata a Tiwita; “Ekweremadu da matarsa Beatrice dukkansu sun gurfana a kotun Majastare da ke Uxbridge bisa tuhumar yin safarar ɗan adam da kuma cire sassan jikin mutum.

“Yaron da aka yi safarar ɗan kimanin shekara 15 a duniya wanda Mista Ekweremadu da Beatrice  suka yi safarar shi zuwa Landon tun daga Legas, Nijeriya.

“Kotu ba ta bayar da belin Ekweremadu ba, saboda haka zai cigaba da zama a tsare har zuwa ranar 7 ga Yuli, 2022.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *