An kama kayayyakin fasaƙwauri na sama da milyan N100 a Katsina

Daga UMAR M. GOMBE

Jami’an Hukumar Yaƙi da Fasaƙwauri ta Nijeriya, sun yi nasarar kama kayayyakin fasaƙwauri da harajinsu ya kai milyan N101,027,350 wanɗanda aka shigo da su cikin ƙasa ta ɓarauniyar hanya a jihar Kastina.

Daga cikin kayayyakin da jami’an suka kama a ranar Alhamis da ta gabata har da motoci guda 14 da harajinsu ya kai milyan N91,592,500, haɗa da kayan abinci da sauransu waɗanda harajinsu ya kai N9,434,850.

Da yake bayani yayin taron manema labarai a babban ofishin hukumar na yankin Katsina, Shugaban Riƙo na Kwastam na Katsina, DC Dalha Wada Chedi, ya jaddada aniyar Hukumar Kwastam da na jami’anta wajen ci gaba da mara wa halastattun harkokin kasuwanci baya da kuma tara wa ƙasa kuɗaɗen shiga yadda ya kamata.

Haka nan, baya ga faɗakar da al’umma game da irin nauyin da ya rataya a kan hukumar tasu, Chedi ya buƙaci jama’a da su gabatar da kansu ga hukumar domin cin moriyar damarmakin kasuwanci mai tsabta da ake da su a maimakon mu’amala da harkar fasaƙwauri.

Ya ƙara da cewa, hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da fatattakar harkokin fasaƙwauri a faɗin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *