An kuɓutar da ɗaliban Zamfara daga hannun ‘yan fashin daji

Kimanin ɗalibai 70 na Makarantar Sakandare da ke Ƙaya cikin yankin Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara aka ceto daga hannun ‘yan bindiga a ranar Lahadi.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 1 ga Satumba rundunar ‘yan sandan Zamfara ta tabbatar da an yi garkuwa da ɗalibai 73 a jihar.

Sai dai, a ranar da aka kwashi ɗaliban ba da jimawa ba biyar daga cikinsu suka kuɓuta.

Lamarin da ya sanya gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya ɗauki matakin rufe dukkan makarantun firamaren da sakandaren jihar.

Tare kuma da kafa dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a wasu ƙananan hukumomi 14 a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *