An nemi matasa da su zama masu kyawawan ɗabi’u a Nijeriya

Daga DAUDA USMAN a Legas

An nemi matasa da su kasance jakadu nagari, kuma su zama masu kyawawan ɗabi’u don kasancewa manyan gobe.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin Sarkin Al’ummar Hausawa mazauna garin Ibafo, Ƙaramar Hukumar Owode a Jihar Ogun, wato Alhaji Shehu Usman Ɗanyaro yayin da yake zantawa da wakilin mu bayan an sauko daga Sallar Idi a makon jiya.

Sarkin ya nemi matasa da sauran al’ummar Hausawa mazauna garin na Ibafo da jihar bakiɗaya da su zama masu kyawawan halaye da ɗabi’u nagari, domin a cewarsa hakan ya zama darasi ga yara matasa ƙanana masu tasowa a matsayin su na yara manyan gobe.

Haka zalika, Ɗanyaro ya yi amfani da damar, inda ya aike da saƙon barka da sallah ga kafatanin al’ummar Musulmin Jihar Ogun da Nijeriya bakiɗaya, inda ya yi kira ga Hausawa da Yarabawa da sauran ƙabilu da su kasance masu assasa zaman lafiya ba tare da tsangwama ko kyarar juna ba.

Ya kuma yi kira ga al’ummar ƙasar nan da su cigaba da yi wa Arewa da Nijeriya bakiɗaya addu’o’in zaman lafiya da don samun cigaba mai ma’ana a lungu da saƙon ƙasar.

Kazalika ya hori matasa da su kasance masu kare mutuncin kansu da mutuncin yankinsu da ƙasarsu, inda ya ce kowa ya fita zaɓe idan lokaci ya yi don zavar ingantattun shuwagabanni masu kishin ƙasa da al’ummarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *