An yi jana’izar Alaafin na Oyo

Daga WAKILINMU

A ranar Asabar aka yi jana’izar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III a mahaifarsa Oyo.

An binne basaraken ne a harabar fadar masarutar.

Marigayi Lamidi Adeyemi ya rasu yana da shekara 83.

Adeyemi ya rasu ne da safiyar Juma’ar da ta gabata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Afe Babalola da ke Ado Ekiti.

Da safiyar Asabar aka zo da gawar marigayin Oyo inda aka gudanar da wasu tanade-tanade na gargajiyaarsu kana daga bisani aka binne ta.

Bayanai sun nuna marigayin ya kasance sarki mafi daɗewa a kan karagar mulki inda ya shafe shekara 52 a matsayin sarki.

A ‘yan lokutan baya-bayan nan, an samu rashe-rashen fitattu a Jihar Oyo da suka haɗa da tsoffin gwamnoni, Sanata Isiaka Ajimobi da Chief Adebayo Alao-Akala da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *