Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
An bayyana cewa ana daf da buɗe Jami’ar KHARAN ta Khalifa Sheikh Ishaqa Rabi’u a Jihar Kano.
Jami’ar dai ita ce ta farko a Nijeriya da aka assasa ta da nufin bunƙasa karatun Alƙur’ani Maigirma da nazarinsa da kimiyyarsa wacce aka yi wa laƙabi da Jami’ar KHARAN wacce Marigayi Kadimul Ƙur`an Khalifa Sheikh Ishaqa Rabiu ya gina ta kuma ana daf da fara karatu a cikinta tsakanin ƙarshen shekarar nan zuwa farkon shekarar 2023.
Kamar dai yadda Malam Anwar Sheik Ishaqa Rabiu ya bayyana a lokacin taron saukan kammala saukan karatun Alƙur’ani Maigirma na shekara, da ake yi a masallacin Khalifa Ishaqa Rabiu duk shekara wanda aka yi sauka 2666 da nufin neman zaman lafiya a Kano da ma Nijeriya baki ɗaya, kamar dai yadda shi Malam Anwar ya bayyana a ranar Asabar da ta gabata.
Har ila yau ya ƙara da cewa wannan jami’a da Khalifa ya gina kafin wafatinsa, burinsa shi ne karantar da Alƙur’ani Maigirma amma kuma kasancewar jami’a na da dokokin kafawa dole ta kasance da sauran ilimoma da za su taimakawa fahimtar Alƙur’ani daidai da yadda tsarin jami’a yake a ko’ina cikin duniya, amma dai akwai wata cibiya da aka tanada a wannan jami’a wadda aikin ta shi ne nazarin Alƙur’ani zalla domin gano duk wata kimiyya da fasaha da sauran ilimunmuka da ke cikin Alƙur`ani Maigirma, domin amfanin duniyar mu ta yau daga falala da ilimin da ke cikin wannan gagarabadau a cikin littatafan duniya baki ɗaya.
Shi ma a jawabinsa Alhaji Yusuf Ishaqa Rabiu ya ce su dai a wannan gida kullum banda gudunmawar da su ke bayarwa wajen bunƙasa harkar kasuwanci da cigaban tattalin arziki da sauransu a Kano da Nijeriya baki ɗaya.
“Addu’a ta neman zaman lafiya a jihar mu da ƙasar mu na daga cikin babbar gudunmawa da gidan Khalifa Sheik Ishaqa Rabiu ya ke bayarwa a tsawon shekaru masu yawa,” inda kuma ya buƙaci hukumomi su ma su yi abin da za su iya na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a wannan ƙasa mai albarka.