APC ta lashe kujeru 23 a zaɓen Majalisar Dokokin Ekiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 23 a zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar.

Jam’iyyar SDP ta lashe kujeru biyu a mazabar Ekiti ta Gabas 1 da Ise/Orin, yayin da kujerar a Ido/Osi 1 ba ta cika ba.

Jam’iyyar PDP dai ba ta samu nasarar lashe zaɓen ba kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar a ranar Lahadi.

Shugaban sashen wayar da kan jama’a masu kaɗa ƙuri’a, Temitope Akanmu ne ya fitar da sakamakon zaɓen a madadin Kwamishinan Zaɓe (REC), Farfesa Ayobami Salami.

INEC ta ce, mazaɓar jihar Ido/Osi 1 ba ta cika ba saboda ratar da ake da ita, kuma akwai buƙatar a sake gudanar da zaɓe a rumfunan zaɓe uku kafin wanda ya yi nasara ya fito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *