Editor

9513 Posts
Gwamnatin Kano ta rushe shataletalen Gidan Gwamnati

Gwamnatin Kano ta rushe shataletalen Gidan Gwamnati

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf, ta ci gaba da aikin rusau da take gudanarwa a cikin garin Kano, Inda a ranar Talata da daddare aikin rusau ɗin ya dira kan shataletalen da ke daura da Fadar Gwamnatin jihar. Bidiyon lamarin da ya karaɗe gari, ya nuna yadda motar rusau ɗin ta yi rugu-rugu da randabawul ɗin. Rusau da Gwamnatin Abba Kabir Yusurf ta Jam’iyyar NNPP ke ci gaba da yi a jihar na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ɓangarorin da ke ganin dacewarsa da kuma masu ganin rashin kyautatuwar hakan,…
Read More
Yanzu lokaci ne na yi wa Zamfara aiki bilhaƙƙi, cewar Gwamna Dauda ga ‘yan majalisar jihar

Yanzu lokaci ne na yi wa Zamfara aiki bilhaƙƙi, cewar Gwamna Dauda ga ‘yan majalisar jihar

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga sabbin 'yan Majalisar Dokokin jihar da su haɗe kai da yin aiki tare don cigaban jihar. Lawal ya yi wannan kira ne yayin ganawar da ya yi da sabbin mambobin majalisar a zauren Majalisar a ranar Talata. A ranar Talata ta wannan makon aka rantsar da 'yan majalisar Jihar Zamfara karo na bakwai. Sanarwa da mai bai wa Gwamna Dauda shawara kan lamurran yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Laraba ta ce, Hon. Bilyaminu Ibrahim Moriki ne aka zaɓa a matsayin…
Read More
Buhari: Komai ya yi farko, akwai ƙarshensa

Buhari: Komai ya yi farko, akwai ƙarshensa

Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI Kamar yau ne muka cika da murnar rantsar da Shugaba Buhari a matsayin sabon Shugaban ƙasar Nijeriya a shekarar 2015. Wasu sun zuba ruwa a ƙasa sun sha, don murna. Wasu sun yi wanka da kwata don murna. Wasu sun yi tattaki tun daga Legas zuwa Abuja don murna. Wasu sun yi yanke-yanken dabbobi irin su shanu da raguna da kaji, gwargwadon dai ƙarfin mutum. Wasu sun yi rawa da waƙa a titi don kawai murnar rantsar da sabon Shugaban ƙasa Buhari a 2015. Tun a farkon shekarar mulkinsa wasu suka fara dawowa daga rakiyarsa. Wasu…
Read More
Sunusi Lamiɗo Sunusi Sarki ne da babu kamarsa: Martani ga Aliyu Ammani a kan rubutunsa ‘soma fiffiken tururuwa’

Sunusi Lamiɗo Sunusi Sarki ne da babu kamarsa: Martani ga Aliyu Ammani a kan rubutunsa ‘soma fiffiken tururuwa’

Daga HARUNA BIRNIWA Ina farawa da sunan Allah maɗaukakin sarki, tsira da amincinSa su tabbata ga Annabinsa Muhammadu salLahu alaihi wa sallam. Shi sha'anin Sarki Muhammadu Sanunsi II gobara ce daga kogi, kashe ta sai Allah. Girman Hasada ko tsoron kada Allah Ya yi masa rawani sau biyu har ya cikasa tarihin kakansa Sir, Muhammadu Sanusi (I) da ya mulki Kano kuma ya zama Khalifan Shehu Tijjani ba zai hana Allah yin ikonsa ba. Taɗiya da sare gwuiwoyin mabiya ba zai yi tasiri ba a wannan lokacin, Kano ta numfasa kuma ta amince yave ya fi sabo armashi. Wai ma…
Read More
Mutum 100 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara

Mutum 100 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara

Daga BASHIR ISAH Aƙalla mutum 100 aka ruwaito sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Litinin a Jihar Kwara. Bayanai sun ce hatsarin ya auku a yankin ƙauyen Egbu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Patigi a jihar. An ce hatsarin ya auku ne a lokacin da waɗanda iftila'in ya rutsa da su a lokacin da suke hanyar komowa gida daga bikin aure da suka halarta a Jihar Neja mai maƙwabtaka da jiharsu. Tuni Gwmnan jihar, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana alhini da ta'aziyya ga 'yan uwan waɗanda suka rasu a hatsarin. Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga…
Read More
Sbugaban Majalisar Dattawa ya ziyarci Tinubu bayan rantsar da shi

Sbugaban Majalisar Dattawa ya ziyarci Tinubu bayan rantsar da shi

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ziyarci Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja. A ranar Talata sanatoci suka zaɓi Akpabio na Jam'iyyar APC daga Jihar Akwa Ibom tare kuma da rantsar da shi a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa zubi na 10. Akpabio ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 66 inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Abdullazeez Yari na Jam'iyyar APC daga Zamfara, wabda ya samu ƙuri'u 43.
Read More
‘Yan Majalisar Zamfara sun zaɓi sabon shugaba

‘Yan Majalisar Zamfara sun zaɓi sabon shugaba

Daga BASHIR ISAH 'Yan Majalisar Jihar Zamfara sun zaɓi Honorabul Bilyaminu Isma’il daga Ƙaramar Hukumar Zurmi a matsayin sabon Shugaban Majalisar ba tare da hamayya ba. Kazalika, sun zaɓi Adamu Aliyu Birnin Magaji daga Ƙaramar Hukumar Gummi a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar. Sun gudanar da zaɓen ne a ranar Talata a zauren majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar.
Read More
Gwamnan Ondon ya tafi jinya a ƙetare

Gwamnan Ondon ya tafi jinya a ƙetare

Daga BASHIR ISAH Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya fara hutun jinya na kwana 21 a ƙetare. Akeredolu ya miƙa wa mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, ragamar mulkin jihar ya zuwa lokacin da zai dawo daga jinyar tasa. A cikin wasiƙar da ya aika wa Majalisar Dokokin jihar, Akeredolu ya bayyana cewa, Aiyedatiwa zai yi riƙon ƙwarya game da shugabancin jihar har zuwa lokacin da zai dawo. Kakakin Majalisar Jihar, Olamide Oladiji, ya ce wasiƙar ta nuna ya zuwa 6 ga watan Yuli, 2023 Akeredolu zai koma bakin aiki. A cewar Mr Oladiji, “Hutun wanda ya fara aiki daga 7 ga…
Read More
Hon Kalu ya zama mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai

Hon Kalu ya zama mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai

Daga BASHIR ISAH 'Yan Majalisar Wakilai ta Ƙasa sun zaɓi Hon Benjamin Kalu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai. Kalu ɗan Jam'iyyar APC ne mai wakiltar Mazaɓar Bende daga Jihar Abia. Kuma ya samu zama Mataimakin Majalisar ne ba tare da hamayya ba. Tuni Akawun Majalisar, Sani Tambuwal, ya rantsar da Kalu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai don kama aiki. Kalu ya gaji Idris Wase ne wanda ya riƙe matsayin a Majalisa ta tara.
Read More
Bana babu hawan Babbar Sallah a Masarautar Zazzau

Bana babu hawan Babbar Sallah a Masarautar Zazzau

*Sarkin zazzau zai tafi ƙasa mai tsarki Masarautar Zazzau, ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, LLD, ta ba da sanarwar cewar, ba za a gudanar da hawa ba yayin Babbar Sallah mai zuwa. Hakan zai faru ne sakamakon tafiya aikin Hajjin da Sarkin Zazzau zai yi don sauke farali, in ji sanarwar da masarautar ta fitar a ranar Talata. A cewar sanarwar, "Ba za a yi hawan Sallah Babba ba, kamar yadda Maimartaba Sarkin Zazzau ya saba jagorantan Hawan a duk shekara. "Maimartaba Sarkin Zazzau na yi wa kowa fatan Alhairi, da fatan za a…
Read More