Editor

9513 Posts
Tajuddeen Abbas ya zama shugaban Majalisar Wakilai

Tajuddeen Abbas ya zama shugaban Majalisar Wakilai

Daga BASHIR ISAH Majalisar Wakilai ta zaɓi Tajuddeen Abbas, na Jam'iyyar APC a matsayin Shugaban Majalisar. Abbas ya taki wannan matsayi ne bayan da ya doke abokan hamayyarsa, Aminu Jaji da Ahmed Idris Wase. Yayin da Abbas ya samu ƙuri'u 353, Aminu Jaji ya samu uku, haka ma Jibrin Wase. Baki ɗaya, ƙuri'i 359 aka kaɗa a zaɓen. Abbas shi ne ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Zariya a Majalisar Wakilai ta Tarayya.
Read More
An rantsar da Sanata Barau a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

An rantsar da Sanata Barau a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Daga BASHIR ISAH Zaɓaɓɓen sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Jibrin Barau, ya lashe zaɓen mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa. Sanata Dave Umahi ne ya zaɓi Sanata Barau don takarar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, sannan Sanata Salisu Mustapha ya mara baya. Akawun majalisar ne ya bayyana nasarar da Jibrin Barau ya samu. Tuni dai aka rantsar daSanata Barau a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa a majalisa ta 10.
Read More
Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa

Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa

Daga BASHIR ISAH An zaɓi ɗan takarar Shugaban Majalisar Dattawa na Jam'iyyar APC, Godswill Akpabio, a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa. Akpabio ya lashe zaɓen da ƙuri'u 63 inda ya doke Sanata Abdulaziz Yari wanda ya tsira da ƙuri'u 46. Akawun Majalisar Tarayya, Sani Tambuwal, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen. Tambuwal ya ce sanatoci 107 ne suka kaɗa ƙuri'a. Sanata Ali Ndume ne ya zaɓi Akpabio don takarar Shugaban Majalisar, yayin da Sanata Adeola Olamilekan, daga Jihar Ogun, ya mara masa baya.
Read More
Waɗanne mata ne maza ba sa so?

Waɗanne mata ne maza ba sa so?

Daga AMINA YUSUF ALI A wannan mako za mu kawo muku mata da suka zama baragurbin mata waɗanda duk macen da ta kasance cikinsu, abar gudu ce a wajen mutane. Idan ba ta ɗauki matakin gyara ba. Mace mavarnaciya/al-mubazzara: Ita ce macen da ba ta da tattali da kaffa-kaffa da kayan gida idan mai gida ya kawo. Irin waɗannan mata ba ƙaramin shaqa wa maza baƙinciki suke a zukatansu ba. Musamman maza marasa ƙarfi masu ƙoƙarin ganin sun sauke haƙƙin iyalansu. Ta hanyar ƙuƙutawa su sayo dukkan abinda ake buƙata na gida. Musamman a wannan lokaci na tsadar rayuwa. Namiji…
Read More
Marigayi Haruna Kundila: Mutumin da ya fi kowa arziki a Kano kafin zuwan Turawa

Marigayi Haruna Kundila: Mutumin da ya fi kowa arziki a Kano kafin zuwan Turawa

Daga IBRAHIM HAMISU A cikin waƙar Marigayi Malam Sa'adu Zungur (1915 - 1958) mai taken Arewa Mulukiya ko Jamhuriya, ya ce, "Ya Sarki Alhaji Bayero, Ga ’yan birni da Kanawiya. "Tun Bagauda na saran Kano, Suka fara fataucin dukiya." A tarihi, jihar Kano ta kasance cibiya ta siye da sayarwa, ma'ana kasuwanci. Tarihi ya kuma bayyana cewa jihar ta haifi manyan mutane masu ƙarfin arziki da dama waɗanda suka yi shuhura da kafa tarihin da ba za a manta da su ba. Ba a iya wannan qarnin ba ne kawai jihar Kano ta samu manyan masu arziki ba, Allah ya…
Read More
Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

A ranar Asabar 10 ga Yunin 2023 ne ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa ta gudanar da taronta na ƙarshen shekara, inda ta gayyaci dukkanin shugabanni a matakin ƙasa da jihohi. Taron, wanda ya gudana a babban zauren taro na Kannywoo TV da ke Tudun Yola a cikin birnin Kano, ya kafa babban tarihi a masana'antar shirya finafinan Hausa. Babban abin da ya fi ba wa mahalarta taron sha'wa, ciki, har da wakilan kwamitin Amintattu da na kwamitin ayyuka na musamman da tsare-tsare, shi ne yadda Shugaban Ƙungiyar Dr. Ahmad Muhammad Sarari ya ɗauki lokaci wajen bayyana ayyukan ci gaba da mulkinsa…
Read More
Ranar Dimokuraɗiyya: Akwai aiki babba a gaban Nijeriya – in ji Atiku

Ranar Dimokuraɗiyya: Akwai aiki babba a gaban Nijeriya – in ji Atiku

Daga BASHIR ISAH Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa, akwai babban aiki a gaba kafin dimokuraɗiyyar Nijeriya ta samu cigaban da ya kamata. Atiku ya bayyana haka ne a cikin saƙon Ranar Demokradiyya ta bana da ya isar wa 'yan ƙasa a ranar Lahadi. Ranar Dimokuraɗiyya rana ce da aka ƙayyade domin 'yan ƙasa su duba su ga cigaban da aka samu a dimokuraɗiyyar ƙasa. Wazirin Adamawa ya ce, kamata ya yi 'yan Nijeriya da suka shaida mulkin soja a ƙasar su yaba da samun dimokuraɗiyya…
Read More
Zamfarawa mazauna Kano sun yi taro a karon farko

Zamfarawa mazauna Kano sun yi taro a karon farko

Daga MUHAMMAD MUJITTABA a KANO Ƙungiyar Zamfarawa mazauna Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Kabir Ibrahim Gusau, ta gabatar da gagarumin taro wanda ya haɗa da ɗimbin Zamfarawa mazauna Kano daga sassa daban-daban na ƙananan hukumomin Kano har da maƙwabtan jihohi. Taro ya gudana ne a ranar Asabar a Birnin Kano. A jawabinsa, Shugaban Ƙungiyar Alhaji Kabir Ibrahim Gusau ya ce maƙasudin wannan taro shi ne sa da zumunci a tsakanin waɗannan al'ummar Zamfara mazauna Kano da kuma qundirin tallafawa juna ta fuskoki daban-daban na rayuwa da kuma yunquri na ganin al'ummar Zamfara mazauna Kano da ma sauran jahohi sun haɗa kai…
Read More
Za mu taimaka wa gwamnati da motocin bas 100 saboda cire tallafin mai – DAPPMAN

Za mu taimaka wa gwamnati da motocin bas 100 saboda cire tallafin mai – DAPPMAN

Ƙungiyar Dillancin Man Fetur a Nijeriya ta 'Depots and Petroleum Products Marketers Association of Nigeria' (DAPPMAN) ta yi alƙawarin samar da manyan motocin bas 100 don tallafa wa yunƙurin gwamnati na cire tallafin man fetur. Da take magana bayan ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu ranar Laraba, shugabar ƙungiyar Dame Winifred Akpani ta ce suna goyon bayan matakin gwamnati na cire tallafin 100 bisa 100. Akpani ta ce motocin ƙirar gida ne kuma masu amfani da iskar gas maimakon fetur. "Cire tallafin mai ba ya nufin tsawwala farashinsa ko kuma rage yawansa a tsakanin 'yan Nijeriya," in ji ta. "Magana ce…
Read More
Ranar Dimokuraɗiyya: Ku ƙara haƙuri da halin da ƙasa ke ciki, ina jin abin da kuke ji, cewar Shugaba Tinubu ga ‘yan Nijeriya

Ranar Dimokuraɗiyya: Ku ƙara haƙuri da halin da ƙasa ke ciki, ina jin abin da kuke ji, cewar Shugaba Tinubu ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri game da halin da suka tsinci kansu sakamakon cire tallafin mai, yana mai cewa, yana jin abin da ‘yan ƙasar ke ji. Tinubu ya yi wannan roƙo ne a ranar Litinin da safe a jawabinsa ga ‘yan ƙasa albarkacin Ranar Dimokuraɗiyya ta bana. Bana shekara 30 kenan cib da samuwar wannan rana ta “June 12”, wadda ta samo asali sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a shekarar 1993. Zaɓen da aka tabbatar da marigayi Chief Moshood K. Abiola, shi ne wanda ya lashe…
Read More