10
Jun
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta ce Felicien Kabuga, da ke fuskantar tuhuma bisa zargin yana da hannu a kisan kiyashin Rwanda cewa ba shi da isasshiyar lafiyar da zai fuskanci tuhuma. Kotun ta ce za ta yi amfani da wata dokar wacce za ta yi kamanceceniya da shari’ar da ake wa Kabuga mai shekaru 80, amma ba za ta yanke masa hukunci ba. Alƙalai a kotun da ke Hague sun ce Kabuga, wanda ake ce-ce-ku-ce kan takamaiman ranar haihuwarsa, da wuya ya sake samun isasshiyar lafiya a nan gaba. An yanke shawarar ne bayan likitoci sun gano…
