Editor

9513 Posts
Benzema ya koma Al-Ittahad ta Saudiyya

Benzema ya koma Al-Ittahad ta Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Karim Benzema ya koma Al-Ittihad kan yarjejeniyar kaka uku, in ji wata majiya daga ƙungiyar ta Jeddah, wadda ta sanar da kamfanin dillacin labarai na AFP. Ranar Lahadi Real Madrid ta sanar cewar tsohon ɗan wasan Faransa mai shekara 35 zai bar Santiago Bernabeu, bayan shekara 14 da ya yi a Sifaniya. Idan har ta tabbata cewa Benzema ya koma Saudiyya, to zai taka leda tare da tsohon ɗan ƙwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo mai wasa a ƙungiyar Al Nassr. Ronaldo ya koma Saudiyya da taka leda daga Manchester United a watan Janairun 2023, bayan da…
Read More
Zan yi bakin ƙoƙari wajen kawo cigaba a ɓangaren kasuwar tattasai a Legas – Aminu Musa

Zan yi bakin ƙoƙari wajen kawo cigaba a ɓangaren kasuwar tattasai a Legas – Aminu Musa

Daga DAUDA USMAN a Legas Sabon shugaban kulawa da cigaban kasuwancin tattasai, atarugu da shambo a Kasuwar Mile 12 dake Legas, Alhaji Aminu Musa, ya bayyana cewar zai yi iyakar ƙoƙarinsa wajen kawo cigaban kasuwancin tattasai, tarugu da shambo a Legas. Alhaji Aminu Musa ya yi wannan tsokaci ne a ofis ɗin sa dake kasuwar Mile-12 a Legas a lokacin da yake karvar baƙuncin waɗansu daga cikin 'yan kasuwar waɗanda suka zo taron walimar taya shi murnar zama sabon shugaban ɓangaren tattasai, tarugu da shambo. Aminu ya ce yana yi wa kowa fatan alheri dangane da wannan al'amari, da fatan…
Read More
Burin mu al’ummar Kano su samu ci gaba a gwamnatin Abba Gida-Gida – Lawan & Sons

Burin mu al’ummar Kano su samu ci gaba a gwamnatin Abba Gida-Gida – Lawan & Sons

Daga MUHAMMAD MUJITTABA A Kano An bayyana cewa al'ummar Kano masu kishinta da son ci gabanta babu wani abu da suke buƙata daga sabuwar gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf wato Abba Gida-Gida domin ita Kano cibiya ce ta kasuwanci da noma, ilimi da sarauta sune ginshiƙai da Kano ke tafiya akan su a shekara da shekaru, don haka duk wata gwamnati da ta zo burin al'ummar Kano a samu cigaban kasuwanci da sauran fannoni na rayuwa da Kano ta ke kan su. "Don haka babban burinsu a cewarsu shi ne gwamnatin Abba ta samar musu da abubuwan cigaban al'ummar Kano…
Read More
KEDCO ta kai tallafin kayan abinci da na karatu a gidan yara na Kano

KEDCO ta kai tallafin kayan abinci da na karatu a gidan yara na Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki KEDCO ta kai tallafin kayan abinci da kayan karatu a gidan yara wato (Nasarawa Children Home) da ke unguwar Nasarawa da ke Kano a ranar Asabar wanda ya yi daidai da ranar yara ta duniya. Da yake jawabinsa yayin miƙa kayan, Babban Manajan Daraktan KEDCO, Alhaji Ahmed Dangana ya bayyana cewa maƙasudin zuwan shi ne sanya farin ciki da murna ga a zukatan yaran domin yawancinsu ba su samu ni'imar da Allah ya bai wa waxanda ba sa gidan ba. Ya ƙara da cewa "mun zaɓi ranar 27 ga Mayu,…
Read More
Kano: Allah Ya yi wa Sheikh Nasir Muhammad Nasir rasuwa

Kano: Allah Ya yi wa Sheikh Nasir Muhammad Nasir rasuwa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A ranar Larabar da ta gabata Masarautar Kano ta sanar da rasuwar Limamin waje, Masallacin Juma'a na Fagge, kuma Waziri Murabus a Fadar Kano, Sheik Nasir Muhammad Nasir. Babban Limamin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya inda ya bar duniya da shekara 80. Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya jagoranci sallar jana’izar Marigayin wadda aka gabatar da misalin ƙarfe tara na safiyar Alhamis a Fadar Sarkin Kano. Mai martaba sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero yana daga cikin manyan mutane da suka halarci jana’izar haɗi da sauran manyan mutane da…
Read More
Gwamnati ta ba da hutun bikin Ranar Dimokuraɗiyya

Gwamnati ta ba da hutun bikin Ranar Dimokuraɗiyya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 12 ga Yuni a matsayin ranar hutun gama-gari ga ma’aikata albarkacin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2023. Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr. Oluwatoyin Akinlade ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis. Sanarwar ta ce, “Albarkacin wannan rana, ana gayyatar ‘yan Nijeriya da abokan Nijeriya su zo su shaida nasarorin da aka cimma da kuma hanƙoron makoma nagari ga dimokurax'ɗiyyar ƙasar. Babban Sakataren ya yi amfani da wannan dama waken taya ‘yan Nijeriya murnar bikin Ranar Dimokuraɗiyya na wanna shekar.
Read More
Sanata Okonkwo ya rasu yana da shekara 63

Sanata Okonkwo ya rasu yana da shekara 63

Daga BASHIR ISAH Fitaccen ɗan siyasar jihar Anambra kuma tsohon ɗan Majalisar Tarayya, Sanata Annie Okonkwo ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 63 a duniya. Rasuwar tasa na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki kaɗan kafin rantsar da ɗansa, Hon. Uche Harris Okonkwo, a matsayin mamba a Majalisar Wakilai ta ƙasa. A halin rayuwarsa, Okonkwo ya yi sanata mai wakiltar Anambra ta Tsakiya a Majalisar Dattawa. Majiyarmu ta ce marigayin har ya soma murmurewa daga rashin lafiyar da yake fama da shi bayan samun kulawa a wani asibitin Amurka. Amma daga bisani jikin nasa ya sake rikicewa…
Read More
Cire tallafin mai: Gwamnoni sun yi wa Tinubu mubaya’a

Cire tallafin mai: Gwamnoni sun yi wa Tinubu mubaya’a

Daga BASHIR ISAH Gwamnoni 36 a faɗin ƙasa, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da batun cire taffin mai. Gwamnonin sun bayyana haka ne yayin ganawar da Shugaban Ƙasar ya yi da Ƙungiyar Gwamnoni (NGF), ranar Laraba a fadarsa da ke a Abuja. Gwamnonin ƙarƙashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, sun bayyana farin ciki da gamsuwarsu game da matakin cire tallafin mai da Shugaba Bola ya ɗauka. Kazalika, sun bai wa Tinubun tabbaci tare da ɗaukar masa alƙawarin za su yi aiki tare a kan haka. Tun farko da yake jawabi, Shugaba Tinubu ya…
Read More
Shigowar gwamnati da ‘yan kasuwa zai kawo bunƙasar rubutun adabi – Shamsiyya Manga

Shigowar gwamnati da ‘yan kasuwa zai kawo bunƙasar rubutun adabi – Shamsiyya Manga

"Marubuta ku tsaftace alƙalaminku ko don goben ku ta yi kyau" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Cigaba da tumbatsar da ake samu ta marubuta a kafafen sadarwa na zamani, bai hana waɗanda suka yi fice kuma suka goge da sha'anin rubutu, samun nasarori da ɗaukaka ba. Wasu marubuta na ganin yawan masu rubutu a onlayin ba ya hana su samun masoya da masu bibiyar littattafansu, duk kuwa da cewa da ake yi, idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Shamsiyya Usman Manga, na daga cikin matasan marubuta da tauraruwarsu ke haskawa. Kuma bayan kasancewarta marubuciya har wa yau Ungozoma…
Read More
Kotu ta haramta wa EFCC bincikar Bello Matawalle da jami’an Gwamnatin Zamfara

Kotu ta haramta wa EFCC bincikar Bello Matawalle da jami’an Gwamnatin Zamfara

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a A. B. Aliyu, ta haramta wa hukumar EFCC gayyata ko tsare tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle. Alƙali Aliyu ya yanke hukuncin haka ne yayin zaman Kotun a ranar Laraba, 31 ga Mayu, 2023, biyo bayan ƙarar da Farfesa Mike Ozekhome, SAN, ya shigar mai lamba FHC/GS/CS/30/2021 BETWEEN THE GOVERNMENT OF ZAMFARA STATE & 1 ANOR V. EFCC & 1 ANOR, a madadin Gwamnatin Zamfara. Ya shigar da ƙarar ce inda yake ƙalubalantar hukumar EFCC game da gayyata, ko tsarewa, ko riƙewa, ko bincikar jami'an gwnatin jihar…
Read More