Editor

9513 Posts
Shugaba Tinubu na ganawa da gwamnoni

Shugaba Tinubu na ganawa da gwamnoni

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kira muhimmin taro a ranar Laraba in yake tattauna da Ƙungiyar Gwamnoni. Ganawar ta haɗa da duka gwamnonin jihohi 36 inda suka haɗu a zauren Majalisar Zartarwa da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja. Karin bayani na tafe…
Read More
Jirgin Nigeria Air da aka ƙaddamar na haya ne, cewar Shugaban Kamfani

Jirgin Nigeria Air da aka ƙaddamar na haya ne, cewar Shugaban Kamfani

Daga WAKILINMU Shugaban kamfanin Nigeria Air, Captain Dayo Olumide, ya bayyana cewa jirgin kamfanin da aka ƙaddamar kwanaki kaɗa kafin ƙarewar wa’adin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, hayarsa aka yi daga ƙasar Habasha domin nuna wa ‘yan Nijeriya. Olumide ya bayyana haka ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin sufurin jiragen sama. Ya ƙara da cewa, muddin jirgin mallakar Nijeriya ne, ya zama dole a yi wa jirgin rijista da sunan Nijeriya. Yayin da ya rage wa gwamnatin Muhammadu Buhari kimani sa’o’i 72, aka ga gwamati ta shigo da jirgin wanda ya sauka a…
Read More
Akume ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya

Akume ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya. Ƙwarya-ƙwaryar bikin rantsawar ya gudana ne ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, inda taron ya shaida yadda Akume ya sha rantsuwar kama aiki. Mahalarta taron sun haɗa da: Mataimaki Shugaban Ƙasa Kashim Shettima; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan; Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, Shugaban Ma’aikatan Tarayya, Dr FolasadeYemi-Esan da sauransu. Rantsarwa na zuwa ne kwana biyar bayan da Shugaban Ƙasa ya naɗa Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da kuma Sanata…
Read More
APC na zargin Kwankwaso da sayar da kadarorin Jihar Kano

APC na zargin Kwankwaso da sayar da kadarorin Jihar Kano

Daga BASHIR ISAH Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bayyana cewa, tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya sayar da wasu filayen gwamnati da sauran kadarori sa’ilin da yake riƙe da jihar tsakanin shekarar 1999 da 2003 da kuma 2011 zuwa 2015. Kazalika, APC ta ce baya ga filayen gwamnati da aka sayar a sassan Kano, gwamnatin Kwankwaso ta sayar da wasu kadarorin gwamnatin jihar da ke Abuja da Legas. Jam’iyyar ta yi zargin haka ne a wani taron manema labarai da ta shirya ranar Talata a sakatariyar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya reshen Jihar Kano. Da yake jawabi…
Read More
Sana’a ga mace na wanzar da zaman lafiya a aurenta – Farida Musa Kalla

Sana’a ga mace na wanzar da zaman lafiya a aurenta – Farida Musa Kalla

"Rashin sana'a ga matasa babbar illa ce ga al'umma" Daga AISHA ASAS Har zuwa yanzu ba a daina samun al'ummar da ke nuna ƙyara da tsangwama ga matan da suka yunƙura don neman na kansu a Ƙasar Hausa ba. Wasu kan la'ance su don irin sana'ar da suka zaɓa, wadda suke ganin bata dace da su ba a matsayin 'ya'ya mata ba, yayin da wasu ke yin kuɗin goro kan mata masu neman na rufa wa kai asiri, wato matan da ba su da kamun kai ne kawai ke fita nema. Duk da wannan matan da suka san ciwon kansu…
Read More
Gwamna Lawal ya nemi haɗin kan NADDC don horar da matasan Zamfara

Gwamna Lawal ya nemi haɗin kan NADDC don horar da matasan Zamfara

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya nemi haɗin kan cibiya ƙirƙire-ƙirƙire tsarin motoci ta ƙasa, wato NADDC da ke Abuja, domin horar matasan Jihar Zamfara da zimmar kyautata rayuwarsu. Lawal ya buƙaci hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar cibiyar a ranar Talata, inda ya samu tarba daga Shugaban cibiyar, Jelani Aliyu tare da wasu manyan jami’ansa. Gwamnan ya ce a shirye Jihar Zamfara take don haɗa kai da cibiyar NADDC wajen bai wa matasan jihar ilimin da za su iya dogaro da kansu a rayuwa. Wannan bayani na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labaran…
Read More
Mu shiryawa ganin canje-canje a sabuwar gwamnati

Mu shiryawa ganin canje-canje a sabuwar gwamnati

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Babu shakka dimukraɗiyyar Nijeriya tana ƙara samun gindin zama da bunƙasa sosai. A tsawon shekaru 23 da komawa kan turbar dimukraɗiyya daga shekarar 1999, Nijeriya ta samu sauye-sauye da dama a ɓangarorin tafiyar da sha'anin mulki, harkar tsaro, manyan ayyukan raya ƙasa, da bunqasa harkokin lafiya da ilimi, da kuma uwa-uba cigaban walwalar jama'a. Ba za a ce komai ya tafi daidai ba, an fuskanci ƙalubale iri-iri da suka haɗa koma bayan tattalin arzikin ƙasa da tsadar rayuwa, rikice-rikicen ƙabilanci da ta'addanci, da cin hanci da rashawa, amma duk da haka za a ce kwalliya tana…
Read More
Gwamnan Lawal ya bai wa hukuma umarnin gaggauta magance matsalar ƙarancin ruwa a Gusau

Gwamnan Lawal ya bai wa hukuma umarnin gaggauta magance matsalar ƙarancin ruwa a Gusau

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya bai wa Ma'aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar umarni a kan ta gaggauta samar da ruwa a Gusau, babban birnin jihar domin ceto al'ummar yankin daga matsalar ƙarancin ruwan da suke fuskanta. Dauda ya ba da umarnin haka ne ta bakin wakilinsa Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Hon. Mukhtar Lugga, yayin da ya kai ziyarar ba-zata a ma'aikatar a ranar Talata. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Sadarwa, Nuhu Salihu Anka ya raba wa manema labarai a birnin. A cewar sanarwar, "Ana sanar…
Read More
An kashe Gwamnan Afghanistan a harin bom

An kashe Gwamnan Afghanistan a harin bom

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga yankin Arewacin Afghanistan sun ce, an kashe gwamnan riƙo na yankin a wani harin bom da aka kai ta hanyar amfani da mota. Wannan shi ne makamancin harin da aka yi amfani da shi wajen kashe wani babban jami'in ɗan sanda a yankin, harin da mayaƙan ISIL (ISIS) suka ɗauki alhakin kaiwa. An ce maharin ya shigi motar Nisar Ahmad Ahmadi da motarsa mai ɗauke da bom wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar muƙaddashin gwamnan Arewacin Badakhshan a ƙasar. Bayanai sun ce direban motar ya mutu yayin da wasu mutum shida sun jikkata. Ya zuwa…
Read More
Tarihin rayuwar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu

Tarihin rayuwar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haife shi a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1952 cikin birnin Legas. Bola Tinubu Musulmi ne kuma ya halarci makarantar firamare mai suna St. John's Primary School, da ke Aroloya da ke birnin Legas, sai sakandiren Children's Home School da ke Ibadan. Tinubu ya samu tafiya ƙasar Amurka domin ƙaro karatu a shekarar 1975, inda ya fara karatu a Kwalejin Richard J. Daley College da ke Chicago, Illinois kafin daga bisani ya koma jami'ar jihar Chicago mai suna Chicago State University. Ya samu kammala digirinsa a shekarar 1979 daga wannan jami'ar inda ya…
Read More