Editor

9513 Posts
Gwamnan Zamfara ya ba da tallafin N2m ga waɗanda harin ta’addanci ya shafa

Gwamnan Zamfara ya ba da tallafin N2m ga waɗanda harin ta’addanci ya shafa

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Zamfara ta ba da tallafi na kuɗi Naira miliyan biyu ga waɗanda harin 'yan bindiga ya shafa a ƙauyukan Janbako da Sakkida da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a jihar. Kakakin Gwamnan jihar, Nuhu Salihu Anka, ya ce gwamnati ta ba da tallafin domin rage wa waɗanda lamarin ya shafa raɗaɗin harin da suka fuskanta kafin gwamnati ta tattara bayanan abin da ya auku. A cewar Salihu Anka, “Gwamnati ta ba da tallafin Naira miliyan biyu ga ahalin waɗanda harin ya shafa, kuma nan ba da jimawa ba jami'ai za su fara tattara bayanai kan ɓarnar…
Read More
Haushin kaza: Kishin matar uba ga ‘ya’yan miji

Haushin kaza: Kishin matar uba ga ‘ya’yan miji

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanku da jimirin karatun jaridarku ta Manhaja, mai farin jini. A wannan mako za mu tattauna ne a kan yadda kishin mata yake zarcewa daga kan kishin miji zuwa kishi a kan yaran da suka haifa. Zan yi matashiya a kan wannan karin magana: "haushin kaza huce kan dami". Wato yadda idon kishiyoyi yake rufewa ruf a kan kishi har ma su dinga ramuwa da fanshe haushin kishinsu a kan 'ya'yan miji. Haka ma wasu 'yan mijin sukan ɗauki matar uba a matsayin kishiya wadda suke kishi da gasa da ita a kan duk wasu abubuwa…
Read More
An cafke tsohuwar shugabar makaranta da laifin yi wa ɗalibai fyafe

An cafke tsohuwar shugabar makaranta da laifin yi wa ɗalibai fyafe

An samu wata tsohuwar shugabar makaranta, 'yar asalin Isra’ila da laifin cin zarafin wasu ɗalibanta biyu a wata makarantar Yahudawa da ke Australia. Kotu a birnin Melbourne na Australia ta samu Malka Leifer da laifin cin zarafin wasu yara mata guda biyu Dassi Erlich da Elly Sapper tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007. Sai dai, ba a same ta da laifin yin lalata da yarinya ta uku da aka tuhume ta a kai ba, Nicole Meyer. Leifer, mai shekara 56 ta musanta zarge-zargen da aka yi mata tun da farko, kuma ta kwashe shekaru tana ƙoƙarin ganin ba a mayar da…
Read More
Lagbaja: Mawaƙin da ba a taɓa ganin fuskarsa ba

Lagbaja: Mawaƙin da ba a taɓa ganin fuskarsa ba

Daga AISHA ASAS Bisade Ologunde, wanda duniya ta fi sani da suna Lagbaja, mawaƙin Nijeriya ne da Allah Ya wadata da baiwar waƙa. Mawaƙi ne da ke da hikimar rera waƙa da mabambantan kiɗa, domin ya ƙware ƙwarai wurin sarrafa waƙz'a mai amfani da kifan zamani da kuma na al’adarsu, wato Yarbanci. Kamar yadda muka sani, kaso mai rinjaye na masu harkar nishaɗantarwa, kama daga waqa, kixa zuwa wasan kwaikwayo ko wasannin barkwanci zuwa na wasan motsa jiki, za ka tarar da a layin farko ko na biyu na burukansu akwai shahara, duniya ta san da su, duk inda suka…
Read More
Ƙarin Farashin Fetur: NLC reshen Zamfara ta goyi bayan yajin aikin uwar goyonta

Ƙarin Farashin Fetur: NLC reshen Zamfara ta goyi bayan yajin aikin uwar goyonta

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Zamfara ta yi alƙawarin shiga yajin aikin da ƙungiyar NLC ta ƙasa ta shirya shiga a faɗin ƙasa. Da yake jawabi a wajen taron da suka shirya ranar Litinin, Shugaban NLC na jihar Zamfara, Sani Haliru, ya ce an kammala duk wani shiri da tuntuɓar juna domin samun nasarar yajin aikin a jihar. A cewarsa, ma’aikatan jihar Zamfara na bayan shugabancin NLC ta ƙasa wajen zanga-zangar nuna rashin yarda da cire tallafin man fetur. Ya ƙara da cewa, "Mun lura da sanarwar da shugaba Tinubu ya yi a…
Read More
Cire Tallafin Mai: Kotu ta daƙile aniyar NLC na shiga yajin aiki

Cire Tallafin Mai: Kotu ta daƙile aniyar NLC na shiga yajin aiki

Daga BSHIR ISAH Kotun Ma'aikata mai zamanta a Abuja ta daƙile shirin Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) na shiga yajin aiki sakamakon cire tallafin mai. Alƙali Olufunke Anuwe ne ya bai wa NLC da rassanta umarnin dakatar da ƙudirin shiga yajin aikin yayin zaman kotun a ranar Litinin. NLC ta shirya fara yajin aikin ne ya zuwa ranar Laraba domin nuna rshin goyon bayanta kan matakin cire tallafin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka.
Read More
Kotu ta hana EFCC, ICPC, SSS tsare tsohon Gwamna Yari

Kotu ta hana EFCC, ICPC, SSS tsare tsohon Gwamna Yari

Daga BASHIR ISAH Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta hana hukumar EFCC da takwararta ICPC masu yaƙi da laifuka masu nasaba da almundahana, tsare Sanata Abdul’aziz Yari har zuwa lokacin da kotun za ta saurari ƙarar da ya shigar. Mai Shari'a Donatus Okorowo ne ya ba da umarnin haka yayin hukuncin da ya yanke kan ƙarar da Michael Aondoaaa ya shigar a madadin Yari. Kazalika, umarnin kotun ya buƙaci hukumar SSS da ta dakatar da tsare zaɓaɓɓen sanatan. Alƙali Okorowo ya umarci waɗanda ake ƙara (EFCC, ICPC, SSS) da su gabatar da hujja a zama mai zuwa kan dalilin…
Read More
Ba a saida Asibitin Hasiya Bayero ba – Tsohon Kwamishinan Kano

Ba a saida Asibitin Hasiya Bayero ba – Tsohon Kwamishinan Kano

Daga BASHIR ISAH Tsohuwar Gwamnatin Jihar Kano ta ce karkatar da hankalin 'yan jihar ne iƙirarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kan cewa an sayar da asibitin yara, wato Hasiya Bayero, da ke birnin jihar. Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya faɗa a ranar Litinin cewar an dakatar da harkoki a asibitin ne na wucin-gadi biyo bayan sake masa matsuguni bayan kammala asibitin yara na Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu, ɗaya daga cikin ayyukan da Gwamnatin Ganduje ta gada. Ya ƙara da cewa, asibitin wanda aka faɗaɗa tare da inganta shi fiye da da zai…
Read More
Gwamnan Kano ya ƙwace asibitin Hasiya Bayero da Gwamnatin Ganduje ta sayar

Gwamnan Kano ya ƙwace asibitin Hasiya Bayero da Gwamnatin Ganduje ta sayar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya ƙwace fitaccen asibitin yara ɗaya tilo da ke cikin birnin Kano wanda aka fi sani da Hasiya Bayero. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ziyarar da ya kai asibitin a ranar Lahadi inda ya duba halin da asibitin ya ke ciki. Asibitin na Hasiya Bayero dai ya shafe shekaru 33 yana aiki, wanda ya shahara wajen karɓar yara marasa lafiya daga ilahirin ƙananan hukumomin jihar da kuma maƙwabtan jihohi. Engr Abba ya bayar da umarnin a gyara asibitin nan take, a mayar da shi na zamani…
Read More
Ƙalubalen da sabon Shugaba Ƙasa Bola Tinubu zai fuskanta

Ƙalubalen da sabon Shugaba Ƙasa Bola Tinubu zai fuskanta

Ana yawan bayyana Nijeriya a matsayin uwa ma ba da mama a Afirka saboda yawan al'ummarta da kuma ƙarfin tattalin arzikinta sai dai tana fama da wasu gagaruman matsaloli - da za su tunkari Bola Tinubu yayin da yake shirin karvar mulki ranar Litinin. Ba lalle bane Tinubu mai shekara 71 ya damu da ƙalubalen. A matsayinsa na wanda ya jagoranci jihar Legas a matsayin gwamna sau biyu, ya farfaɗo da cibiyar kasuwancin ta Nijeriya - wani lamari marar sauƙi kuma ya san da batutuwan. Sai dai 'yan Nijeriya, da waɗanda ma ba su jefa masa ƙuri'a ba, za su…
Read More