05
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata ƙungiya a ƙarƙashin ƙungiyar Masu Kishin Jihar Filato, ta zargi shugaban ƙungiyar masu ba da shawara kan tattalin arziki a gwamnatin Simon Lalong, Cif Ezekiel Gomos da gazawa. Ƙungiyar ta yi zargin cewa tasirin Gomos a matsayin ƙwararre kan tattalin arziki ba a ji daɗinsa ba a jihar. Ƙungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Mista Gofwen Amos Gofwen da Nengak Musa Nathaniel, sun bayyana cewa babban abin takaicin da jihar ta Filato ta fuskanta a tsawon shekaru shi ne na koma-baya zuwa wata jiha.…
