04
Jun
Daga BASHIR ISAH Ya zuwa ranar Litinin ake sa ran Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, zai gana da zaɓaɓɓun 'yan majalisun taraya na jam'iyyun hamayya domin cimma daidaito dangane da shugabancin Majalisar Tarayya. Zaɓaɓɓun sanatoci da 'yan Majalisar Wakilai na jam'iyyun hamayya da suka haɗa da PDP, Jam'iyyar Labour, NNPP da sauransu, na daga cikin waɗanda Shugaba Tinubun zai gana da su. Majiyarmu ta ce, za a yi zaman ne ranar Litinin, 5 ga Yuni a Fadar Shugaban Ƙasa tsakanin ƙarfe 3:00 zuwa 5:00 na yamma. Takardar gayyatar wadda majiyarmu ta samu leƙawa, na ɗauke ne da sa-hannun Babban Sakataren Fadar…
