03
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya sake naɗa Sakataren gwamnatin jihar a ƙarƙashin gwamnatin Nasir El-Rufai Balarabe Lawal a muƙaman gwamnatinsa. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Gaɗa Labaran Gwamnan, Mohammed Shehu, ya fitar a ranar Talata, inda ya ce, Lawal ya ci gaba da riƙe muƙamin a bisa la’akari da gogewarsa aikinsa a harkokin mulki domin ya taimaka wajen tafiyar da sabuwar gwamnati cikin sauƙi. Uba Sani ya kuma amince da naɗin Shuaibu Gimi a matsayin Babban Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Sadarwa da kuma Nasir Abdulkadir a matsayin…
