Editor

9513 Posts
Sababbi da tsofaffin gwamnoni sun kai wa Buhari ziyarar ban-gajiya

Sababbi da tsofaffin gwamnoni sun kai wa Buhari ziyarar ban-gajiya

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata ƙasaitacciyar tawaga da ta ƙunshi gwamnoni masu ci da kuma tsofaffi, ta kai wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ziyarar ban-gajiya a mahaifarsa dake Daura ta Jihar Katsina a jiya Alhamis, 1 ga Yuni, 2023. Daga cikin gwamnonin akwai sabon gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, Dapo Abiodun na Jihar Ogun, Babajide Sanwo Olu na Jihar Legas, Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, Bala Muhammad na Jihar Bauchi, Hope Uzodinma na Jihar Imo da mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam. A sanarwar da ofishin babban mataimaki na musamman akan kafafen yaɗa labarai na zamani ya fitar,…
Read More
Sevilla ta lashe kofin Europa bayan doke Roma

Sevilla ta lashe kofin Europa bayan doke Roma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sevilla ta doke Roma a bugun fenariti tare da lashe kofin Europa karo na 7 yayin wasansa ƙarshe cikin daren Laraba a filin wasa na Puskas Arena da ke Budapest. Tun farko Dybala ya fara zurawa Roma ƙwallonta a minti na 34 da taimakon Mancini amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Sevilla ta farke sakamakon kuskuren zura ƙwallon da Mancini ya yi a ragarsu, dalilin da ya sa kenan har aka kai ƙarshen wasa ana ƙwallo 1-1. Bayan ƙarƙare hatta ƙarin lokacin da aka yi wa karawar ta jiya ne kuma aka tafi bugun fenariti…
Read More
Mu tsare martabar aure don kiyaye makomar mu

Mu tsare martabar aure don kiyaye makomar mu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A makon da ya gabata akwai wani muhimmin batu da ya ɗauki hankalin jama'a a zaurukan sada zumunta dangane da batun wata matashiya ’yar gwagwarmaya Malama Layla Ali Othman wacce a wata hira da ta yi da wani shiri na tashar BBC Hausa ta bayyana halin da mata zawarawa ke fuskanta, tare da labarin irin halin da ita ma ta samu kanta a ciki bayan rabuwar aurenta da wasu mazaje. Babu shakka jama'a da dama sun yi tsokaci iri-iri a kai, gwargwadon fahimtar da suka yi wa jawabin nata. Akasari martani masu zafi ya fi fitowa…
Read More
Mawaƙiya Tina Turner ta kwanta dama

Mawaƙiya Tina Turner ta kwanta dama

Daga AISHA ASAS Fitacciya kuma shahararriyar mawaƙiyar Tina Turner, wadda ta kafa tarihi a duniyar waƙa ta mutu tana da shekara 83. Mawaƙiyar, wadda aka haifa a Tennessee da ke Amurka, ta rera waƙoƙi da dama kamar, 'Mountain High', 'What's Love Got to Do With It', 'River Deep' da dai sauransu. Za mu iya cewa, matsalolin rayuwar aure da mawaƙiyar ta fuskata ne suka zama sanadin ɗaukakar ta, domin kamar yadda aka tabbatar kusan duk waƙoƙin da ta ke rerawa na ɗauke da kukan zuci na daga rashin jin daɗin zamantakewarta da tsohon mijinta mai suna IkeTurner. Turner daɗaɗɗiyar mawaƙiya…
Read More
Na yi kuka da aka ce Sanata Binani ta faɗi zaɓe – Aisha Gombe

Na yi kuka da aka ce Sanata Binani ta faɗi zaɓe – Aisha Gombe

"Mata 'yan siyasa na shan tsangwama a tsakanin al'umma" "Soyayyar Buhari ce ta sa na shiga siyasa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mata a kowanne mataki suna ba da gagarumar gudunmawa wajen harkokin raya ƙasa da cigaban dimukraxiyya. Ana iya ganin mata a ko'ina yayin da aka ce an buga gangar siyasa, inda za a yi ta faɗi tashi tare da su da sauran ýan ƙasa wajen neman goyon baya ga ýan takarar su da jam'iyyunsu na siyasa. Hajiya Aisha Usman Ahmad na daga cikin waɗannan jajirtattun mata da suke taka rawar gani a siyasar Jihar Gombe da ma Nijeriya bakiɗaya.…
Read More
Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga sassan Nijeriya sun ce, a halin da ake ciki farashin fetur ya ƙaru zuwa Naira 700 kan kowace lita a wasu sassan ƙasar. Wannan ya biyo bayan sanar da cire tallafin mai baki ɗaya da sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawbinsa ga ‘yan ƙasa jim kaɗan da rantsar da shi a ranar Litinin da ta gabata. Binciken Manhaja ya gano cewar, matakin cire tallafin da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya haifar da ƙarin farashin mai da kashi 100 zuwa 250, inda a yanzu ake sayar da lita guda na fetur tsakanin…
Read More
Katsinawa sun roƙi ‘yan Nijeriya a kan su yafe wa Buhari

Katsinawa sun roƙi ‘yan Nijeriya a kan su yafe wa Buhari

Daga UMAR GARBA a Katsina Al'ummar jihar Katsina sun roƙi 'yan Nijeriya da su yafe wa tsohon Shugaban Ƙasar, Muhammadu Buhari, a kan kura-kuran da ya aikata lokacin da yake kan mulki. Majiyar Manhaja ta ce, Katsina sun yi wannan roƙo ne a wajen taron hawan daushe na musamman da suka shirya wa Buhari s ranar Talata don karrama dawowarsa gida. Taron wanda Masarautar Daura ta shirya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Daura, Umar Faruq Umar, don maraba da dawowa gida ga Buhari bayan shafe shekara takwas yana mulkin ƙasar. A zantawarsu da manema labarai, Lawal Ado da Umaru Yusuf sun nuna…
Read More
HOTUNA: Yadda aka shirya wa tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari hawan daushe a Daura

HOTUNA: Yadda aka shirya wa tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari hawan daushe a Daura

Daga SANI MAIKATANGA Masarautar Daura a Jihar Katsina, ta shirya hawan daushe na musamman domin karrama dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, gida. Bikin ya gudana ne a ranar Talata tare da samun dandazon mahalarta. Buhari ya koma mahaifarsa Daura bayan kammala wa'adin mulkinsa a matsayin Shugaban Ƙasar Nijeriya a ranar 29 ga Mayu, 29. Ga ƙarin hotuna daga wajen taron:
Read More
Sabon Gwamnan Sakkwato ya soke naɗe-naɗen da Tambuwal ya yi gab da saukarsa

Sabon Gwamnan Sakkwato ya soke naɗe-naɗen da Tambuwal ya yi gab da saukarsa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Sa'o'i 24 shan rantsuwa Gwamnan Jihar Sakkwato, Dr. Ahmad Aliyu ya soke naɗe-naɗen da gwamnatin Aminu Tambuwal ta yi da ƙarin girma ga ma'aikatan jihar bayan 19 ga watan Maris, 2023. Bayan haka, Gwamna Ahmad ya soke dukkanin canza sunayen manyan makarantun jihar da duk abin da ke da alaƙa da shugabannin gudanarwar makarantun, kamar yadda bayanin ya ce dukkaninsu, sun koma sunayensu da aka sansu da su a baya. A bayanin da ya yi wa manema labarai, kakakin gwamnan, Abubakar Bawa, ya ce, Gwamnan ya ce za a sake wewayar naɗe-naɗen sarautun da tsohon…
Read More
Gwamnan Zamfara ya yi sabbin naɗe-naɗe na muƙamai 13

Gwamnan Zamfara ya yi sabbin naɗe-naɗe na muƙamai 13

Daga BASHIR ISAH Sabon Gwamnan Jihar Zamfara, Dokta Dauda Lawal Dare, ya yi sabon naɗe-naɗe na mutum 13 a gwamnatinsa. Wannan shi ne karo na biyu da Gwamnan ke yin naɗi tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki na jami’an da za su yi aiki tare a sabuwar gwamnatin Zamfara. A karon farko, Gwamnan ya naɗa Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Mukhtar Muhammad Lugga, a matsayin Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Jihar, sai kuma Abubakar Nakwada a matsayin Sakataren Gwamnati. Ga jerin sunayen waɗannan sabbin naɗe-naɗen ya shafa: 1) Imran Ahmad Rufai(Personal assistant P.A) 2) Aminu Almajir(Deputy chief of…
Read More