Editor

9513 Posts
Da na ga dama sai in saka jami’an tsaro su kama Obi a Kaduna, inji El-Rufa’i

Da na ga dama sai in saka jami’an tsaro su kama Obi a Kaduna, inji El-Rufa’i

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad Elrufai, ya ce da ya ga dama sai ya saka jami'an tsaro su kama ɗan takarar Shugabancin Ƙasa a ƙarƙashin inuwar LP, Peter Obi. El-Rufa'i, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron zuba jari na Kaduna karo na 7.0, wato Kadinvest da ya gudana ranar Asabar a Kaduna. Gwamnan na Kaduna ya ce wani lokaci a baya da ya kai ziyarar bibiyar lamuran zave a jihar Anambra, sai da Peter Obi ya sa aka tsare shi awanni 48, saboda shine gwamna a jihar. Ya…
Read More
Muna ƙoƙari don shawo kan tsadar abinci – Shugaba Buhari

Muna ƙoƙari don shawo kan tsadar abinci – Shugaba Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta duƙufa kan ƙoƙarin magance tsadar farashin abinci a ƙasar. Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake buɗe taron bita kan ayyukan ministocinsa karo na uku don tantance irin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da ƙudurorin da gwamnatinsa ke bai wa fifiko. Jaridar Daily Trust ta ambato shugaban ƙasar na cewa: “Muna yin gagarumin ƙoƙari don warware matsalar tashin farashin abinci mai alaƙa da hauhawar farashin da ake fama da shi a faɗin duniya.” Alƙaluman baya-bayan nan, inji shi daga Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya sun…
Read More
A karon farko Jihar Kogi ta samu kasonta a matsayin jihar da ke da arzikin man fetur a Arewacin Nijeriya

A karon farko Jihar Kogi ta samu kasonta a matsayin jihar da ke da arzikin man fetur a Arewacin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A karon farko Jihar Kogi ta fara samun kasonta a matsayin jiha mai arzikin man fetur a Arewacin Nijeriya. Jaridar yanar gizo ta Intelregion, ta rawaito Gwamna Yahaya Bello yana bayanin cewa gwamnatin jiharsa ta karɓi kaso daga cikin kashi 13 da ake ware wa jihohi masu mai. Yahaya Bello ya yi wannan bayani ne a wajen taron Majalisar Zartarwa na jiha wanda aka saba yi duk mako a gidan gwamnati na Lugard House. Gwamna Bello ya ce gwamnatinsa ta yi abubuwan a-zo-a-gani, inda ya ce samun arzikin mai zai taimaka wajen cigaba da…
Read More
Hukumar FCTA ta gargaɗi masu gudanar da sana’ar kanikanci a gefen hanyoyin jirgin ƙasa

Hukumar FCTA ta gargaɗi masu gudanar da sana’ar kanikanci a gefen hanyoyin jirgin ƙasa

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar gudanar da al'amuran Birnin Tarayyar Abuja (FCTA), a ranar Lahadin da ta gabata ta yi jan kunne ga masu buɗe shagunan kanikanci a gefen hanyoyin jirgin ƙasa a Abuja. Daraktan kula da cigaba na FCTA, Director Muktar Galadima, shi ya bayyana wannan gargaɗin. Kuma a cewar sa nan gaba hukumar za ta dinga kama waɗanda suka yi kunnen ƙashin a game da dokar tare da ƙwace ababen hawan da suke aikin a kai. Galadima ya ƙara da cewa, waɗancan kanikawa za a gurfanar da su a gaban kotun tafi da gidanka. Sannan ya ƙara da…
Read More
Minista Sadiya ta gargaɗi wasu jihohi kan hasashen ambaliyar ruwa da ke tafe

Minista Sadiya ta gargaɗi wasu jihohi kan hasashen ambaliyar ruwa da ke tafe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwar Al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta faɗakar da gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi da ma shugabannin jama'a, musamman a jihohin Anambara, Delta, Kuros Riba, Ribas da Bayelsa, cewa ambaliyar ruwa na nan tafe a cikin makwanni masu zuwa, sannan ta yi kira a gare su da su shirya wa aikin kwashe jama'ar da ke zaune a yankuna da hanyoyin da ruwan ke bi. Ministar ta faɗi haka ne a taron da ta yi da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja domin bayyana masu ƙoƙarin da…
Read More
Babban ɗan Sanata David Marka, Tunde Mark ya mutu

Babban ɗan Sanata David Marka, Tunde Mark ya mutu

An haife shi a Oktoba, ya mutu a Oktoba Daga BASHIR ISAH Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya yi rashin babban ɗansa, Tunde David Mark. Manhaja ta kalato cewar, Tunde ya rasu ne da safiyar Juma'a a London bayan fama da cutar daji. Ana sa ran ɗauko gawar marigayin zuwa Nijeriya nan da 'yan kwanaki don yi mata jana'iza. An haifi marigayin ne a ranar 13 ga Oktoban 1971 inda ya bar duniya yana da shekara 51. A halin rayuwarsa, marigayin ya yi karatu a gida da waje. Kuma ya mutu ya bar mata da ɗa ɗaya.
Read More
FIFA U17: Flamingos ta kai mataki na kusa da ƙarshe

FIFA U17: Flamingos ta kai mataki na kusa da ƙarshe

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Mata ta Nijeriya (Flamingos) ta samu nasarar tsallakewa zuwa mataki na kusa da ƙarshe na gasar Kofin Duniya na FIFA na mata 'yan ƙasa da shekara 17 wanda ke gudana a Indiya. Flamingos ta samu wannan nasara ne bayan da ta lallasa takawararta ta Amurka da ci 4-3 a bugun fenariti. An buga wannan wasa ne a ranar Juma'a, 21 ga Oktoba, 2022.
Read More
A karo na biyu, NLC ta sake ƙin amincewa da yin rajista ga ƙungiyoyin CONUA da NAMDA

A karo na biyu, NLC ta sake ƙin amincewa da yin rajista ga ƙungiyoyin CONUA da NAMDA

Daga AMINA YUSUF ALI Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta sake yin watsi da ƙudirin Ministan Ƙwadago na Nijeriya a kan yin rajistar sabbin ƙungiyoyin malaman makaranta a jami'o'in Nijeriya. Wannan bayani yana ƙunshe ne a wata takarda wacce shugaban ƙungiyar NLC Ayuba Wabba ya gabatar ga Ministan Ƙwadago da ayyuka, Chris Ngige. Wannan takarda tana a matsayin wasiƙar da ministan ya aiko yana neman ƙungiyar NLC ɗin ta ba da shaidar rajista ga ƙungiyoyin Ƙungiyar Jami'o'in Nijeriya (CONUA) da kuma Ƙungiyar Malaman koyar da likitan da likitancin haƙori na Nijeriya (NAMDA)., Wabba ya bayyana cewa, akwai ayar tambaya a…
Read More
Ƙasar Sin na adawa da yin shisshigi cikin harkokin gidan ƙasashe masu tasowa bisa hujjar kare haƙƙoƙin ɗan Adam

Ƙasar Sin na adawa da yin shisshigi cikin harkokin gidan ƙasashe masu tasowa bisa hujjar kare haƙƙoƙin ɗan Adam

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, ƙasarsa tana adawa da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan ƙasashen dake tasowa, bisa hujjar kare haƙƙoƙin bil’adama, matakin da kuma ya samu goyon-baya daga sassan ƙasa da ƙasa, musamman ma ƙasashe masu tasowa. Wang ya yi wannan furucin ne, yayin da yake gabatar da manyan nasarorin da ƙasar Sin ta samu a fannin raya sha’anin kare haƙƙoƙin ɗan Adam. Ya ce tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 18, kwamitin ƙolin jam’iyyar dake ƙarƙashin…
Read More
Taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar na 20 da muhimmancinsa

Taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar na 20 da muhimmancinsa

Daga LAWAL SALE A ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba ne aka buɗe taron wakilai karo na 20 na jam’iyyar kwaminis da ke kan karagar mulkin ƙasar Sin (JKS) a Beijing, babban birnin ƙasar Sin, taron dake da muhimmancin gaske, wanda har ya jawo hankalin ƙasa da ƙasa. A wannan karon dai an samu halartar wakilai, gami da waɗanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300. Babban sakataren kwamitin ƙolin JKS, kana shugaban ƙasar ta Sin, Xi Jinping ya bayyana yayin buɗe taron cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu wasu manyan nasarori 3 masu…
Read More