Editor

9513 Posts
Nijeriya na da kyakkyawar makoma a hannunmu – Buhari

Nijeriya na da kyakkyawar makoma a hannunmu – Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, duk da ƙalubalan tattalin arziki da duniya ke fuskanta da faɗuwar farashin mai wanda hakan ya haifar wa ƙasa ƙarancin kuɗin shiga, gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin ɗora Nijeriya kan turbar cigaba. Buhari ya ce duba da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu ƙarƙashin Jam'iyyar APC, jami'yyar na da dukkan dalilan da za su ta yin alfahari da hakan. Shugaban ya bayyana haka ne a Juma'ar da ta gabata, sa'ilin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe Shugaban Ƙasa (PCC) da sauran tsare-tsaren yaƙin neman zeɓe na…
Read More
Dubai ta dakatar da bai wa ‘yan Nijeriya biza

Dubai ta dakatar da bai wa ‘yan Nijeriya biza

Daga BASHIR ISAH Hukumomin Dubai sun ba da sanarwar dakatar da bai wa 'ya Nijeriya biza ta shiga ƙasar har sai abin da Allah Ya yi. Bayanin dakatawar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da suka aika wa abokan kasuwancinsu na Nijeriya. Dubai ta ce ta dakatar da dukkan yakardun da aka tura mata don neman biza daga Nijeriya. Bayanai sun ce wannan mataki da Dubai ta ɗauka na da nasaba da matsayar da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Haɗaɗɗiyar Dular Larabawa ta cimma, tare da cewa dakatarwa ta shafi dukkan 'yan Nijeriya ne. Sanarwar ta ƙara da…
Read More
APC a Zamfara ta yi Allah wadai da harin da PDP ta kai wa mutane a Gusau

APC a Zamfara ta yi Allah wadai da harin da PDP ta kai wa mutane a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen Jihar Zamfara, a cikin kakkausar murya ta yi Allah-wadai da harin da wasu ‘yan bangar siyasa na jam’iyyar suka kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a Gusau babban birnin jihar. Sakataren yaɗa labaran Jam’iyyar APC na jihar Yusuf Idris ya yi wannan martanin a wani taron manema labarai. “Dukkanmu muna sane da munanan abubuwan da ke faruwa a jihar mu abar ƙauna, inda a jiya Asabar wasu ‘yan bangar Jam'iyyar PDP suka far wa wasu matasanmu da ba su ji ba ba su…
Read More
Matsalar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa a Nijeriya

Matsalar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa a Nijeriya

Likitocin masu taɓin hankali a Nijeriya sun yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don daƙile wannan mummunan matsala a ƙasar. A kiyasin su, ɗaya daga cikin ’yan Nijeriya huɗu, wato sama da miliyan 50, na fama da tavin hankali. Likitocin masu tavin hankali ne suka bayyana hakan a zaman wani viangare na ayyukan bikin Ranar Kiwon Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Duniya (WMHD) na 2022. Ana tunawa da WMHD kowace shekara a ranar 10 ga Oktoba don wayar da kan jama'a game da lafiyar ƙwaƙwalwa a duk faɗin duniya da kuma haxa kai don tallafawa waɗanda ke da matsalar tavin hankali.…
Read More
An rufe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin na 20

An rufe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin na 20

Daga CMG HAUSA Yau Asabar aka rufe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin (JKS) na 20 a birnin Beijing. A yayin bikin rufe taron, wakilai 2338 mahalarta taron sun zabi kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20, da kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin ƙolin. Kana an zartas da ƙuduri game da rahoton kwamitin ƙolin jam’iyyar JKS karo na 19, da ƙuduri game da rahoton ayyukan kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin ƙolin karo na 19, da kuma ƙuduri kan gyararren kundin ƙa’idojin jam’iyyar. Taron ya amince da shigar da sabbin nasarorin nazari…
Read More
Juncao, ciyawar da ke Rungumar makomar ɗan Adam ta bai ɗaya

Juncao, ciyawar da ke Rungumar makomar ɗan Adam ta bai ɗaya

Daga LUBABATU LEI Jama, ko kun taba jin sunan Juncao? Wannan wata nau'in ciyawa ce da ake iya amfani da ita wurin noman laimar kwaɗo da ake iya mai da ita abinci ko magani, wadda ake kiranta ciyawar ƙasar Sin ko ciyawar samar da arziki a ƙasashe da dama. A shekarun 1980, noman laimar kwaɗo ya zama muhimmin aiki da manoma ke dogara a kai wajen sauƙaƙa fatara a lardin Fujian da ke Kudu maso gabashin ƙasar Sin. Sai dai hakan ya haifar da matsala a sakamakon yadda manoma suke yawan saran bishiyoyi don yin amfani da su wajen noman…
Read More
Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da shugaban jam’iyyar mai mulkin ƙasar Abdullahi Adamu

Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da shugaban jam’iyyar mai mulkin ƙasar Abdullahi Adamu

Daga CMG HAUSA Kwanan baya, jakadan ƙasar Sin dake Nijeriya Cui Jianchun, ya gana da shugaban jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar Sanata Abdullahi Adamu. A yayin ganawar, Cui Jianchun ya bayyana cewa, babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20, wani muhimmin lamari ne a tarihin harkokin siyasar jam'iyyar da jama'ar ƙasar Sin. A cikin shekaru kusan 10 da suka gabata, ƙarƙashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, ƙasar Sin ta cimma nasarar gina al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, kuma ta samu sakamako mai kyau wajen kawar da talauci, da yaki da cin hanci da…
Read More
Zan ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu na soke takara ta – Binani

Zan ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu na soke takara ta – Binani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohuwar 'yar takarar kujerar gwamna ƙarƙashin Jam'iyyar APC a Jihar Adamawa, Sanata Aisha Dahiru Binani, ta sha alwashin ɗaukaka ƙarar hukuncin kotu da ta soke nasarar da ta samu a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar. A wata tattaunawa da Binanin ta yi da wata kafar yaɗa labarai mai suna Muryar Arewa a jihar, ta ce Nuhu Ribadu kamar ɗan uwa yake gareta kuma yana da damar ƙalubalantar nasararta a kotu. Binani ta ce ta ɗauki hukuncin na kotu a matsayin ƙaddara saboda a cewarta Allah ne ke ba da mulki ga wanda ya so.…
Read More
Hukumar NDLEA ta cafke mace mai goyo, mai juna-biyu, da wasu 26 da muggan ƙwayoyi

Hukumar NDLEA ta cafke mace mai goyo, mai juna-biyu, da wasu 26 da muggan ƙwayoyi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Hukumar yaƙi da sha, da fatauci da miyagun ƙwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewar, ta yi nasarar cafke mutane 28, cikin su har da mace mai juna biyu, da wata mai goyo, haɗi da wani ɗalibin jami’a ɗan aji biyu a makaranta da buhunan tabar wiwi waɗanda aka ƙiyasta nauyin su akan kilogiram dubu tara da ɗari huɗu da talatin da bakwai, da ɗigo shida haɗi da ƙwayoyi opioids guda 138, 053, da ma wasu ƙwayoyin daban-daban. A cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahdi da ta gabata, mai magana da yawun hukumar,…
Read More
Likitocin asibitin ATBU sun duba lafiyar direbobi 180 a Yankari Express

Likitocin asibitin ATBU sun duba lafiyar direbobi 180 a Yankari Express

Daga MU'AZU HARDAWA a Bauchi A ƙoƙarin su na tallafa wa direbobi da ma'aikatan kamfanin sufuri na Yankari Express, da ke Bauchi, ƙwararrun likitoci kan harkar ido sun duba mutane 180 a ƙarƙashin shirin bikin ranar gani ta duniya wato World Sight Day na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ke kasancewa a ranar kowace Alhamis ta biyu a cikin watan Oktoba, inda a bana ya kasance ranar 13 ga Oktoba. Likitoci daga Asibitin Koyarwa na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi sun duba lafiyar idon direbobin kamfanin sufara na Yankari Express inda suka ba mutane 90 tabarau da magani wa…
Read More