Editor

9513 Posts
Matashi ya bada kwangilar kashe mahaifinsa a Yobe

Matashi ya bada kwangilar kashe mahaifinsa a Yobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sandan Jihar Yobe a yau Laraba ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna Yahaya Sai’du, ɗan shekaru 20 da haihuwa, wanda ake zargi da bada kwangilar kashe mahaifinsa, Saidu Oroh. Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya shaida wa manema labarai a Damaturu cewa an kama wanda ake zargin ne a Gujba, a ranar Litinin. Ya ce wanda ake zargin ya ɗauki hayar wasu mahara uku da suka harbe Oroh har lahira a gidansa da ke ƙauyen Pompom, a ranar 20 ga watan Agusta. “Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya…
Read More
An zaɓi Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin ƙolin JKS

An zaɓi Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin ƙolin JKS

Daga CMG HAUSA An zaɓi Xi Jinping, a matsayin babban sakataren kwamitin ƙolin Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20, yayin zaman farko na kwamitin da ya gudana Lahadin nan, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwar bayan taron. Zaman wanda Xi ya jagoranta, ya samu halartar mambobi 203 na kwamitin kolin JKS na karo na 20 da kuma mambobi masu jiran gadon wani muƙami 168. Haka kuma a yayin wannan zama, an bayyana Xi a matsayin shugaban hukumar ƙolin sojojin kwamitin ƙolin JKS. Mambobin zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin ƙolin JKS da aka zaɓa a zaman taron,…
Read More
EndSars: An gudanar da zanga-zangar tunawa da kisan Lekki a Legas

EndSars: An gudanar da zanga-zangar tunawa da kisan Lekki a Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jiya Alhamis ne wasu ɗaruruwan mutane suka gudanar da zanga-zangar jimamin tunawa da kashe 'yan uwansu da suke zargin jam'ian tsaro sun yi a Ƙofar Lekki shekaru biyu da suka gabata a zanga-zangar ƙin jinin 'yan sandan SARS. Sai dai jami’an rundunar 'yan sandan jihar ta Legas sun ta harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da nufin daƙile shirinsu. Masu zanga-zangar dai sun yi tattaki ne a kan ƙofar a wani ɓangare na bukukuwan tunawa da zagayowar ranar, an ce sun yi arangama da 'yan sandan da ke ɗauke da makamai da aka…
Read More
Kotu ta bada umarnin bincikar shugabannin hukumomin tsara birane da na kadarorin Gwamnatin Kano

Kotu ta bada umarnin bincikar shugabannin hukumomin tsara birane da na kadarorin Gwamnatin Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Wata babbar kotu a Jihar Kano ta bai wa kwamishinan 'yan sandan jihar umurnin su binciki Shugaban Hukumar Tsara Birane, Abdulwahab da na Kula da Kadarorin Gwamnati na Jihar Jibrilla Muhammad bisa zargin da ake musu na ruguje wa 'yan kasuwar Bampai shagunansu da yin awon gaba da kayayyakinsu ba tare da sahalewar doka ba. Lauyan 'yan kasuwar Barista Abba Hikima Fagge ya bayyana hakan yayin da yake ƙarin haske ga manema labarai, inda ya ce wannan ya biyo bayan ƙunshin tuhuma da suka kai wa kotun. Ya ce kotun ta baiwa kwamishinan 'yan sanda…
Read More
Makarantar Almumtaz ta yi bikin yaye ɗaliban ta karo na biyar

Makarantar Almumtaz ta yi bikin yaye ɗaliban ta karo na biyar

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Makarantar Al’mumtaz dake kusa da masallacin Idi dake kan tsohuwar hanyar Nasarawa a garin Keffi, Jihar Nasarawa, ta yi bikin yaye ɗalibanta da suka kammala karatun Alƙur’ani da na zamani karo na 5 tare da karrama su da ba su kyaututtuka da sauransu.  Bikin wanda aka gudanar a harabar makarantar ya samu halarcin iyayen ɗaliban da ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da sauran shugabanni a duka matakai.  A jawabin shugaban makarantar kuma Darakta Dr. Musa Ahmad Isa ya faro ne da bayyana taƙaitaccen tarihin makarantar ta Al’mumtaz wanda a cewarsa aka kafa ne da…
Read More
Xi ya jaddada fa’idar babban taron wakilan JKS na 20

Xi ya jaddada fa’idar babban taron wakilan JKS na 20

Daga CMG HAUSA Yau ne, babban sakataren Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin Xi Jinping, da sauran mambobin zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS karo na 20 da suka haɗa da Li Qiang da Zhao Leji, da Wang Huning, da Cai Qi, da Ding Xuexiang da Li Xi, suka bayyana a gaban ‘yan jaridu a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin. Babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, babban taron wakilan JKS na karo na 20, shi ne babban taro na ƙara ɗaga tutar jam’iyyar, da…
Read More
Gidan Arewa da siyasar 2023

Gidan Arewa da siyasar 2023

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Gidan arewa wato ‘AREWA HOUSE’ da ke titin Rabah a anguwar Sarki a Kaduna garin gwamna nan ne gidan gwamnatin Arewa inda marigayi firimiya Sir Ahmadu Bello Sardauna ya zauna kuma har ma a nan ɗin ne masu kisan gilla ƙarƙashin Manjo Nzeogwu Kaduna su ka yi ma sa gillar. Alamun gidan inda nan ne Sardauna ya ke kuma a nan a ke da cibiyar kayan tarihi ciki da wasu kayayyaki da marigayin ya yi amfani da su na nuna alfaharin Arewa da ma kai tsaye a ce kishin arewa mai jihohi 19. Haƙiƙa gidan na…
Read More
Masanan Afirka sun bayyana ra’ayoyinsu kan tasirin da taron wakilan JKS karo na 20 Zai haifarwa Sin da duniya

Masanan Afirka sun bayyana ra’ayoyinsu kan tasirin da taron wakilan JKS karo na 20 Zai haifarwa Sin da duniya

Daga CMG HAUSA A cikin kwanakin da suka gabata a jere, taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Sin karo na 20 ya janyo hankalin ƙasa da ƙasa matuƙa. Yayin da aka rufe taron, masanan Afirka sun bayyana cewa, taron yana da babbar ma’ana, wanda zai haifar da babban tasiri ga kasar Sin, har ma zai ƙara kuzari ga ƙasashen duniya wajen yin haɗin gwiwa don tinkarar ƙalubale da samun bunƙasuwa tare. Darektan cibiyar nazarin harkokin Sin dake Nijeriya Charles Onunaiju ya yi nuni da cewa, Sin tana son samar da gudummawa ga sauran ƙasashen duniya wajen samun ci gaba, kana bunƙasuwar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin sakin Nnamdi Kanu

Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin sakin Nnamdi Kanu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Biyo bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, wacce ta saki jagoran ƙungiyar ’yan ta'addan Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙoli. A ɗaukaka ƙarar da aka shigar a ranar 19 ga Oktoba, 2022, a gaban Kotun Ƙoli ta ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Gwamnatin Tarayya ta buƙaci Kotun Ƙoli ta dakatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a ranar 13 ga Oktoba, 2022, wanda ya saki shugaban na ƙungiyar 'yan awaren Biyafara. Gwamnatin Tarayya a cikin shaɗarar ɗaukaka ƙara ta bakwai, ta yi Allah-wadai da matakin da ƙaramar…
Read More
Abinda ya sa Buhari tsige Shugaban Hukumar Neja-Delta

Abinda ya sa Buhari tsige Shugaban Hukumar Neja-Delta

*Majalisar Dattawa ta gayyaci Ministan Neja-Delta bisa zargin almundahanar Naira Biliyan 480*An danganta tsige Shugaban NNDC da Ministan Daga MAHDI M. MUHAMMAD A jiya Alhamis ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya tsige Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (wato NDDC), Mista Effiong Akwa. Sanarwar da ta fito daga hannun mai magana da yawun Ma’aikatar Kula da Harkokin Yankin Neja Delta, Patricia Deworitshe, ta ce, tsige Akwa da Buhari ya yi ya soma aiki ne daga jiya, 20 ga Oktoba, 2022. Sanarwar ta qara da cewa, a baya an naɗa Mista Akwa shugaban NDDC ne na wucingadi tsawon wa’adin lokacin da…
Read More