Editor

9513 Posts
Sin da ke bin hanyar samun bunƙasuwa cikin lumana wata dama ce ga duniya

Sin da ke bin hanyar samun bunƙasuwa cikin lumana wata dama ce ga duniya

Daga CMG HAUSA A yayin buɗe babban taro karo na 20 na wakilan jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin, babban darektan jam’iyyar Xi Jinping ya bayyana a cikin rahoton da ya gabatar cewa, Sin na tsayawa tsayin daka kan manufofin wanzar da zaman lafiya da sa ƙaimi ga samun bunƙasuwa tare, da kuma duƙufa kan gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama. Ra’ayin dake jawo hankalin al’ummar duniya sosai. Manazarta na ganin cewa, rahoton da Xi Jinping ya bayar ya bayyana anniya da ƙwarin gwiwar Sin na nacewa ga bin hanyar zamanintar da kanta da samun bunƙasuwa cikin lumana, JKS…
Read More
Shugabanni ne ya kamata su bada misali wajen bin umarnin kotu – Alh. Hamisu Ƙarami

Shugabanni ne ya kamata su bada misali wajen bin umarnin kotu – Alh. Hamisu Ƙarami

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano An bayana cewa babu wanda ya kamata ya girmama doka da binta kamar shugabanni, domin aikin shugaba ne ya zama babban misali ga talaka mai ƙaramin ƙarfi wanda ba shi da wami zaɓi sai dai ya bi doka ko yana so ko ba ya so, wannan shi ne abin da doka ta sani. Alhaji Hamisu Ƙarami, wani matashi ne mai fashin baƙi a kan al'amuran yau da kullum, ya bayana haka ne a lokacin da yake hira da 'yan jarida a ofishinsa dake Kano a ranar Lahadi da ta gabata. Ya ce zargin da aka…
Read More
Yadda Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or na bana

Yadda Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or na bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A cikin makon nan ne fitaccen ɗan wasan ƙungiyar Real Madrid, Karim Benzema ya lashe kyautar Ballon d'Or ta Gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta duniya na 2022, yayin bikin da ya gudana a birnin Paris, inda ya gaji Lionel Messi wanda ya lashe kyautar a bara. A shekarar bana dai, Paris babban birnin Faransa ya zama na musamman ga ɗan wasan gaban na Real Madrid, domin kuwa a nan ne, suka lashe kofin gasar Zakarun Turai karo na 14, bayan doke Liverpool da 1-0 a watannin baya. Ƙididdiga ta nuna cewar, sau goma sha biyu…
Read More
Mun cika alƙawuran da muka ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Mun cika alƙawuran da muka ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A cikin jawabin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya yi a wurin taron bitar ayyukan da gwamnatin sa ta aiwatar wa 'yan Nijeriya, Shugaba Buhari ya ce an aiwatar da ayyuka masu tasiri a faɗin ƙasar nan, waɗanda suka cika buri da muradin 'yan Nijeriya. Wannan taro na musayin ra’ayoyi ne da kuma yin bitar ayyukan da gwamnati ta aiwatar a tsawon shekaru 7 a Nijeriya wanda ministoci da shugabannin ma’aikatu za su tattauna akai. Shugaba Buhari, ya ce, ”Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da ayyuka masu yawan gaske a ƙasar nan musamman na raya…
Read More
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Borno ta ɗauki sabbin jami’ai 1,800

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Borno ta ɗauki sabbin jami’ai 1,800

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Kimanin sabbin jami’am tsaro (Constables) guda1,800 rundunar ‘yan sanda ta Jihar Borno ta ɗauka aiki domin inganta tsaro a cikin jihar, a cewar kwamishinan ‘yan sanda Abdu Umar. Da yake bayyana wa manema labarai shirin rundunar, kwamishina Umar ya ce an ɗauki sabbin ma’aikatan ne domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro masu tsare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar, haɗi da wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma. Kwamishina Abdu Umar ya bayyana cewar, a yanzu haka sabbin ɗaukar ‘yan sanda suna samun horaswa dangane da ire-iren rawar da ya kamata su riƙa takawa ta fuskar…
Read More
Shugabancin NDDC: Buhari ya maye gurbin Akwa da Audu-Ohwavborua

Shugabancin NDDC: Buhari ya maye gurbin Akwa da Audu-Ohwavborua

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Injiniya Emmanuel Audu-Ohwavborua a matsayin Muƙaddashin Shugaban Hukumar Bunƙasa Neja Delta (NDDC). Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da Daraktar Yaɗa Labarai ta Ma'aikatar Kula da Harkokin Yankin Neja Delta, Patricia Deworitse ta fitar a ranar Alhamis. Naɗin Audu-Ohwavborua ya biyo bayan tsige shugaban NDDC mai barin gado, Effiong Akwa da Shugaba Buhari ya yi a ranar Alhamis. Sanarwar ta ce Audu-Ohwavborua ne zai ci gaba da riƙe hukumar ta NDDC har zuwa lokacin da za a tabbatar da Manajin Darakta da kuma Kwamitin Gudanarwa na hukumar. Kazalika,…
Read More
Putin ya kafa dokar yaƙi a wasu sassan ƙasarsa

Putin ya kafa dokar yaƙi a wasu sassan ƙasarsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin, ya ce zai kafa dokar yaƙi a yankuna huɗun da Rasha ta mamaye na Ukraine wanda Moscow ta yi iƙirarin cewa yankunanta ne. Putin ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da yake yi wa Majalisar Tsaron ƙasar jawabi. Haka nan, Shugaban ya umarci gwamnatin ƙasar ta kafa kwamiti na musmaman ƙarƙashin Firaminista Mikhail Mishustin don yin aiki tare da yankunan Rasha don ƙarfafa wa ƙoƙarin yaƙin Moscow a Ukraine. Wannan yunƙuri da Putin ya yi na zuwa ne kimanin watanni takwas da ɓarkewar yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine wanda…
Read More
Cutar kansa na mayar da yara miliyan guda marayu kowacce shekara – Bincike

Cutar kansa na mayar da yara miliyan guda marayu kowacce shekara – Bincike

Daga AISHA ASAS Wani binciken masana kimiya ya ce, yara kusan miliyan guda ne a duniya ke rasa iyayensu mata kowacce shekara saboda cutar kansa ko sanqara, abinda ke mayar da su marayu kai tsaye. Waɗannan alƙaluma an gabatar da su ne a wajen taron cutar sankara ta duniya da ke gudana a Geneva wanda ya nuna alƙaluman yaran da iyayensu mata ke bari a baya sakamakon illar cutar. Cibiyar Binciken Kansa ta Duniya mallakar Hukumar Lafiya da ke Lyon a Ƙasar Faransa ta gabatar da rahotan binciken da akayi a Afirka, wanda ya shafi mata sama da 2,000 da…
Read More
Aikin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Sin ya samu Cigaba sosai

Aikin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Sin ya samu Cigaba sosai

Daga CMG HAUSA Ma Zhaoxu, mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Sin, ya bayyana a yau Alhamis, a wajen wani taron manema labaru da ya gudana cikin cibiyar kafofin watsa labarai ta taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 cewa, aikin hulɗa da ƙasashen ƙetare na ƙasar Sin ya samu ci gaba matuƙa, cikin shekaru 10 da suka wuce, inda yawan ƙasashen da ta ƙulla hulɗar diflomasiyya da su ya karu daga 172 zuwa 181. Jami’in ya nanata babban maƙasudin aikin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Sin, wato ƙoƙarin kare zaman lafiya a duniya, da neman samun…
Read More
Ainihin ma’anar farfaɗo da ƙasar Sin a sabon zamani

Ainihin ma’anar farfaɗo da ƙasar Sin a sabon zamani

Daga CMG HAUSA Ga duk mai bibiyar yadda babban taron wakilan JKS na 20 ke gudana, ba zai gaza jin jimlar “farfaɗo da ƙasar Sin daga dukkanin fannoni a sabon zamani da ake ciki” ba, musamman cikin rahoton da shugaban ƙasar, kuma babban sakataren kwamitin ƙolin JKS Xi Jinping ya gabatar, wanda hakan buri ne na raya ƙasar da JKS ta sha alwashin cimmawa. A ƙarƙashin wannan manufa, akwai muhimman matakai masu dacewa da salon gurguzu mai sigar musamman da ƙasar Sin ke bi, wanda ya tanadi samarwa al’ummar Sinawa yanayin rayuwa mai cike da zaman lafiya da wadata, da…
Read More