08
Aug
Daga CMG HAUSA Kwanan nan ne, ƙasashen Amurka da Australiya da Japan, sun fitar da wata sanarwar hadin-gwiwa, inda suka gindaya sharaɗi game da aiwatar da “manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya”. Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin cewa, wasu ƙasashe ƙalilan sun ƙara gindaya wasu sharuɗɗa, game da aiwatar da manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, da zummar jirkita gaskiya, da ɓata wannan manufa, al’amarin da ya saɓa wa doka, wanda ƙasar Sin ta ki yarda da shi. Rahotanni sun ce, ƙasashen…
