09
Aug
Dubun wani mai gadi ta cika bayan ya saci wayoyin hannu da kuɗinsu ya kai Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar a kasuwar da ya ke aikin gadi. An gurfanar mai gadin, mai shekaru 25 a gaban kotun Mai Shari’a O. A. Taiwo, na kotun da ke Ikeja Jihar Legas. Ana tuhumar mai gadin da aikata laifuka huɗu, haɗin baki, sata, fashi, da shiga wuri ba da izini ba, amma ya musanta zarge-zargen. Ɗan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Raphael Donny, ya faɗa wa kotun cewa mai gadin tare da abokansa sun balla shagon wata ’yar kasuwa mai…
