Editor

9513 Posts
Sin ta fitar da takardar bayani dangane da batun Taiwan da dunƙulewar ƙasar a sabon zamani

Sin ta fitar da takardar bayani dangane da batun Taiwan da dunƙulewar ƙasar a sabon zamani

Daga CMG HAUSA Ofisoshin kula da harkokin Taiwan da na yaɗa labarai na majalisar gudanarwar ƙasar Sin, sun wallafa wata takardar bayani mai taken “Batun Taiwan da dunƙulewar ƙasar Sin a sabon zamani” a yau Laraba. An fitar da takardar ne domin jaddada Taiwan a matsayin wani ɓangare na kasar Sin, da kuma bayyana matsayin JKS da al’ummar Sinawa game da ƙudirinsu na dunkule kasar, tare da nanata matsayi da manufofin JKS da gwamnatin kasar a sabon zamani. A cewar takardar, tun asali, Taiwan yankin ne mallakar ƙasar Sin. kuma wannan batu ne dake da ingantaccen tubali na tarihi da…
Read More
Ƙasar Sin ta kasance ta biyu a duniya a yawan na’urorin makamashin nukiliya dake aiki da waɗanda ake ginawa

Ƙasar Sin ta kasance ta biyu a duniya a yawan na’urorin makamashin nukiliya dake aiki da waɗanda ake ginawa

Daga CMG HAUSA Mataimakin darektan hukumar tsaron makamashin nukiliya ta ƙasa, kana daraktan sashen sa ido kan makamashin nukiliya na ƙasar Sin, Tang Bo ya bayyana cewa, ya zuwa watan Yunin shekarar 2022, ƙasar Sin tana da rukunin tashohin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya 54 dake aiki, baya ga tashohin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya guda 23 da ake ginawa, abin da sanya ta zama ta biyu a duniya. Tang Bo ya gabatar da wannan bayani ne, a yayin bikin buɗe taron ƙasa da ƙasa kan fasahar nukiliya karo na 29 da…
Read More
Ƙasar Sin ta yi kira da a taimakawa ƙasashe masu tasowa don inganta ƙarfinsu na yaƙi da ta’addanci

Ƙasar Sin ta yi kira da a taimakawa ƙasashe masu tasowa don inganta ƙarfinsu na yaƙi da ta’addanci

Daga CMG HAUSA Jiya ne, zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD Zhang Jun ya yi jawabi a yayin taron bainar jama'a da kwamitin sulhu na MƊD ya kira kan "Barazanar ayyukan ta'addanci ga zaman lafiya da tsaron ƙasa da ƙasa”, inda ya bayyana matsayin ƙasar Sin, game da yaki da ta'addanci, kana ya yi kira da a mai da hankali kan taimakawa ƙasashe masu tasowa, musamman ƙasashen Afirka, wajen inganta ƙarfinsu na yaki da ayyukan ta'addanci. Zhang Jun ya ce, rahoton da babban sakataren MƊD ya fitar na nuna cewa, yankuna biyu cikin uku da masu da’awar kafa "Daular Musulunci"…
Read More
Amurka: “Moriyata ta fi gaskiya”

Amurka: “Moriyata ta fi gaskiya”

Daga CMG HAUSA Ƙasar Sin ta mayar da martani game da ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan. Amma, wasu ‘yan siyasar Amurka suna ganin matakai masu dacewa da Sin ta ɗauka a matsayin waɗanda suka tsananta halin da ake ciki a yankin. Yau “duniya a zanen MINA” na bayyana yadda ƙasar Amurka ke nuna girman kai a duniya. A haƙiƙa, ƙasar Sin ta sha bayyana adawarta da ziyarar Pelosi a yankin Taiwan ta hanyoyi daban-daban a matakai daban-daban. Kwanan baya, sakataren harkokin wajen ƙasar Antony Blinken ya bayyana cewa, Amurka ta nace ga kin…
Read More
Dauda Kahutu Rarara: Zakaran da Allah Ya nufa da cara

Dauda Kahutu Rarara: Zakaran da Allah Ya nufa da cara

Daga KWAARED ABDU ZANGO Haƙiƙa Allah shi ne gwani kuma mai ba wa kowa arziƙin da ya so ta hanyoyin da ɗan adam ya yanke ƙauna. Gaskiya ne akwai mawaƙa da yawa cikin duniyagga kuma ana ganin arziƙin da Allah Ta’ala yayi masu ta hanyar sana’ar waƙa. Bari kawai mu duƙufa kawai a Nijeriya ta Arewa inda take da mawaƙa shahararru waɗanda sun yi fice sosai a duniyar waƙoƙin Hausa, kususan na zaɓe da masu sa hikimar su kaɗaita kotso, molo, garaya, kuntigi, goge da dai sauransu kamar kiɗan ɗanmaraya da mai irin muryarsa ɗan zamfara Babangida Kakadawa. To cikin…
Read More
Wai haka za mu zauna?

Wai haka za mu zauna?

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI FAGGE Ka ga mutum ya zo nan ƙiri-ƙiri yana ta haƙilon tsine wa Obasanjo ko Buhari ko Jonathan da sauransu amma sai ka gan shi in ɗalibi ne, an zana masa NECO ko WAEC ta hanyar cuwa-cuwa a "miracle centre" ko kuma ba shi da takardu na gaskiya, duk babu ne, ya biya an yi masa na ƙarya. Ko kuma ka gan shi ko ka gan ta a jami'a tana satar amsa, ko kuma a haɗa baki da shi a ƙara kuɗin da za a amsa a wajen babansa. Idan magidanci ne yana koyarwa a jami'a…
Read More
Masanan Afirka da Sin: Ƙasashe masu tasowa suna ƙoƙarin tabbatar da tsarin duniya mai yaƙini

Masanan Afirka da Sin: Ƙasashe masu tasowa suna ƙoƙarin tabbatar da tsarin duniya mai yaƙini

Daga BELLO WANG A kwanakin baya ne, aka gudanar da taro na 11 na dandalin masanan ƙasashen Afirka da Sin CATTF, a birnin Beijing na ƙasar Sin, inda ɗimbin masana da jami’ai daga bangarorin Afirka da Sin suka halarci taron, tare da tattauna kan batun raya hulɗar dake tsakanin Afirka da Sin, da aiwatar da shirin tabbatar da ci gaban duniya. A ganin mahalarta taron, ƙasashen Afirka da ƙasar Sin, da sauran ƙasashe masu tasowa, za su iya taka muhimmiyar rawa a ƙoƙarin tabbatar da tsarin duniya a wannan zamanin da muke ciki. A yayin taron, wasu shahararrun masana na…
Read More
Matsalar rashin tsaro; ɗan leƙen asiri ya fi ɗan ta’addar daji iya ta’adanci…

Matsalar rashin tsaro; ɗan leƙen asiri ya fi ɗan ta’addar daji iya ta’adanci…

Daga MUHAMMAD AMINU KABIR Lamarin rashin tsaro yana ƙara ƙamari ne ta sanadiyyar wasu daga cikin Al'umma da har yanzu suke ɗaukar bayanan sirri ko dai na jama'ar gari, ko kuma na Jami'an tsaro suna kai wa varayin daji. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa lamarin nan ya ƙi ci, ya qi cinyewa. A kullum Jami'an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an magance wannan matsalar ta rashin tsaro, amma kuma wasu ɗaiɗaikun mutane da rashin tsoron Allah ya hana su barin wannan mummunar ɗabi'ar ta ɗaukar bayanai su kai wa 'yan ta'adda. Abin takaici baka iya…
Read More
Maza ba su cika kai ƙara kotu a kan cin zarafin da matansu ke musu ba – Barista Mariya

Maza ba su cika kai ƙara kotu a kan cin zarafin da matansu ke musu ba – Barista Mariya

"Mata su dinga neman haƙƙinsu a kotu kan cin zarafinsu" "Lauyoyi mata na ba wa mata gudunmawa mai yawa a karu" "Mu na bayar da gudunmawa wajen kare haƙƙin mata ba tare da karɓar kuɗi ba" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Aikin lauya aiki ne na kare haƙƙoƙin jama'a a gaban shari'a, don ƙwatowa mai haƙƙi haƙƙinsa da tabbatar da ganin an yi wa wanda aka zalunta adalci, an kuma hukunta wanda ya yi ba daidai ba. Ga duk ma'aboci bibiyar yadda ake gudanar da shari'a ko ganin yadda lauyoyi ke muhawara da bincike don kare wanda suke wakilta, ya san…
Read More
Giwa ta halaka mace, kuma ta bi gawar ta tattake ana tsaka da jana’iza

Giwa ta halaka mace, kuma ta bi gawar ta tattake ana tsaka da jana’iza

Ba ɓoyayye ba ne cewa giwaye suna daga cikin dabbobin da suka fi saurin shaƙuwa da mutane a duniyar nan, tare da samun shaidu da yawa na waɗannan halittun da ke nuna farin ciki, baƙin ciki, fushi, tausayi, har ma da ƙauna. Amma sai dai a Indiya wata giwa ta kashe wata mata mai shekara 70 sannan ta je ta tattake gawarta a yayin jana’izarta. Giwar ta tsere bayan ta yi wa matar mai suna Maya Murmu aika-aikar a lokacin da ta ke tara ruwa a ƙauyen Raipal da ke Gabashin Indiya, inji ’yan sanda. Matar ta rasu a asibiti…
Read More