Editor

9513 Posts
Cire ni daga sarautar Kano ba zai hana ni cigaba da faɗin gaskiya ba – Khalifa Sanusi II

Cire ni daga sarautar Kano ba zai hana ni cigaba da faɗin gaskiya ba – Khalifa Sanusi II

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Kano Murabus Muhammadu Sanusi ya bayyana cewa duk da an cire shi daga sarauta, zai ci gaba da bayyana gaskiya da faɗin ra’ayinsa wajen kare ƙasa da sake gina Nijeriya. Muhammadu Sanusi wanda shi ne Khalifan Tijjnaniya na Nijeriya, ya bayyana haka a Abuja yayin da ya ke magana a wurin da aka yi wata diramar dave, mai nuna bayanin cire shi daga sarauta zuwa lokacin naɗa shi Khalifan Tijjnaniya. Diramar mai suna “Emir Sanusi: Truth in Time”, an nuna ta ne a babban ɗakin taro na ‘Yar’Adua Centre, Abuja a ranar Asabar.…
Read More
Mutane uku sun mutu bayan da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita gidaje 495 a Kano

Mutane uku sun mutu bayan da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita gidaje 495 a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, SEMA, ta ce ambaliyar ruwa ta kashe mutane uku tare da raba iyalai 495 da muhallansu a Ƙaramar Hukumar Ajingi da ke jihar. Babban Sakataren hukumar, Dr. Saleh Jili ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Ajingi, yayin da yake raba kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa, ciki har da iyalan mutum uku da suka rasu. Jili ya lissafa yankunan da lamarin ya shafa da su ka haɗa da Toranke, Kara Malama, Chuna da Balare. Ya ce lamarin da ya faru bayan ruwan sama…
Read More
Babu wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Filato da bankin JAIZ – Gwamna Lalong

Babu wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Filato da bankin JAIZ – Gwamna Lalong

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa game da sake gina ƙonanniyar Babbar Kasuwar Jos, cewa gwamnatin Filato za ta bai wa Bankin JAIZ damar amfani da kasuwar har tsawon shekaru 40 har sai bankin ya cire kuɗinsa na aikin sake ginin. Gwamnan ya sake jaddadda cewa, ko da an sake gina kasuwar Hukumar Kula da Babbar Kasuwar Jos ce za ta cigaba da tafiyar da harkokin kasuwar, kuma daga kuɗaɗen da ake tattarawa daga hayar shagunan da za a biya shi ne za a biya bankin da shi,…
Read More
Fadar Shugaban Ƙasa ta koka bisa kisan dabbobinta

Fadar Shugaban Ƙasa ta koka bisa kisan dabbobinta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban Nijeriya ta bayyana damuwarta bisa kisan da ake wa namun dajin da ke cikin gandun dajinta a baya-bayan nan. Mahukunta Fadar Aso Rock, sun bayyana hakan ne ta bakin Sakataren Gidan Gwamnati, Tijjani Umar, a yayin da yake karɓar tawagar masu kula da Gandun Daji Na Ƙasa tare da takwarorinsu a Fadar Shugaban Ƙasa, waɗanda aka fi sani da ‘Royal Rangers’. Umar, wanda ya jaddada muhimmancin kariya da kiyaye tsirrai da dabbobi a muhallansu na asali, ya kuma yi alƙawarin inganta yanayin kiyaye muhalli ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace na…
Read More
Dole sojoji su yi bayani kan maƙudan kuɗaɗen da muka ba su – Osinbajo

Dole sojoji su yi bayani kan maƙudan kuɗaɗen da muka ba su – Osinbajo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin Shugaban Nijeriya Yemi Osinbajo ya buƙaci sojojin ƙasar da su yi wa jama’a bayani a kan irin maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ta ba su domin gudanar da ayyukan tsaro a ƙarƙashin shugabancin Muhammadu Buhari. Osinbajo ya ce jama’ar ƙasa na da hurumin sanin irin maƙudan kuɗaɗen da wannan gwamnati ta ware domin tunkarar matsalolin tsaron da suka addabi Nijeriya wanda ke kai wa ga rasa dubban rayuka, don kore shakku dangane da yadda gwamnati ke fuskantar ƙalubalen tsaro. Mataimakin shugaban ƙasar ya ce abin takaici ne kowanne lokaci idan an yi maganar tsaro,…
Read More
Ya kamata a bar Sinawa su yanke shawara kan al’amuran Ƙasar Sin

Ya kamata a bar Sinawa su yanke shawara kan al’amuran Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA A jiya ne, ƙasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken “Batun Taiwan da ɗinkuwar ƙasar Sin a sabon zamani”, inda aka bayyana cewa, kamata ya yi a bar jama’ar ƙasar Sin su yanke shawara kan al’amuran ƙasarsu. Wannan na nufin, batun Taiwan, harkokin gidan ƙasar Sin ne, wanda ya shafi babbar moriyar ƙasar, da kaunar da Sinawa suke nuna wa ƙasarsu, don haka ba su yarda da tsoma baki daga ƙasashen ƙetare ba. Kafin fitar da takardar bayanin, shugabar majalisar wakilai ta ƙasar Amurka Nancy Pelosi, ta ziyarci yankin Taiwan na ƙasar Sin, ba tare…
Read More
Tarihi ba ya mantuwa

Tarihi ba ya mantuwa

Daga CMG HAUSA Tun bayan fara cece-kuce game da haramtacciyar ziyarar da kakakin majalissar dokokin ƙasar Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na ƙasar Sin, masharhanta da dama ke ta bayyana mahangar su, don gane da burin Amurka na haifar da baraka ga ƙasar Sin, da lalata yanayin zaman lafiya da tsaro a zirin Taiwan. To sai dai kuma, ga dukkanin alamu Amurka ba za ta yi nasara ba a wannan mummunar manufa, ganin cewa tuni mahukuntan Sin din suka tsara dukkanin manufofi, na dinkuwar ɗaukacin sassan ƙasar cikin lumana, ciki har da yankin na Taiwan. Wannan manufa ce…
Read More
Yawan injina da Ƙasar Sin ta fitar da su zuwa ƙetare a farkon rabin bana ya ƙaru da kashi 10.41

Yawan injina da Ƙasar Sin ta fitar da su zuwa ƙetare a farkon rabin bana ya ƙaru da kashi 10.41

Daga CMG HAUSA A kwanakin baya ne, ƙungiyar hadin kan masana’antun ƙera injuna ta ƙasar Sin, ta fitar da ƙididdigar dake nuna cewa, a watanni 6 na farkon bana, yawan ƙarin kuɗin da aka samu a wannan ɓangare ya ƙaru da kashi 0.7% bisa na makamancin lokaci na bara, yayin da yawan kuɗin dake shafar cinikin fitar da injuna zuwa ƙetare na kasar Sin, ya kai dala biliyan 344.12, wanda ya ƙaru da kashi 10.41%. Daga cikinsu motoci da injunan injiniya sun kasance a kan gaba. Tun daga farkon wannan shekara, yankuna da sassa daban-daban na ƙoƙarin tinkarar mawuyacin halin…
Read More
Rubutu ne maganin ciwona, inji marubuciya Sandra Cisneros

Rubutu ne maganin ciwona, inji marubuciya Sandra Cisneros

Daga AISHA ASAS Wasu marubuta na kallon rubutu a matsayin hanyar yin abin da zai burge mutane, ko ya wa'azantar da su, ko nishaɗantarwa, wasu kuwa na kallon baiwar rubutu a matsayin hanya ta samun kuɗi, ko samun shuhura, ko kuma sha'awa kawai. Abin da na na ke ƙoƙarin faɗa shine, kowanne marubuci da irin fahimta da ma'anar da yake bai wa rubutunsa. Kazalika da irin rawar da yake takawa a rayuwarsa. Sai dai zai yi wuya ya tsallake waɗannan ababe da mu ka lissafo. Sai dai a ɓangaren marubuciya Sandra Cisneros sam ba haka zancen yake ba, domin ba…
Read More
Abinda ya kashe kasuwar littafai

Abinda ya kashe kasuwar littafai

Daga MUKHTAR ISA KWALISA A wajejen shekarar 2004 littafina ya soma shiga kasuwar, na samu kasuwar littafi a wani tsari na mulkin mallaka, galibi 'yan kasuwa ke da haƙƙin mallakar littafan da suka yi shuhura tun a waccan zamanin. Sannan manya 'yan kasuwar littafi guda uku ne, Garba da Sauki da kuma Jakara city Bookshop duk da a lokacin su Al'amin da Hassan Miga sun soma tasowa da yunƙurin amshe ƙarfin iko. A lokacin littafi kamar gwal ne, kowanne aka buga ana siya. Sannu a hankali, da yake duniya juyi-juyi ce sai hankalin masu karatu ya karkata zuwa ga marubutan…
Read More