Editor

9513 Posts
NDLEA ta cafke wani fasto da ke safarar ƙwayoyi a gangunan coci

NDLEA ta cafke wani fasto da ke safarar ƙwayoyi a gangunan coci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), sun kama wani mai fataucin miyagun ƙwayoyi, Fasto Anietie Okon Effiong da ganguna uku na 'crystal methamphetamine,' wanda ake kira Mkpuru Mmiri, wanda ake kyautata zaton an shigo da su ne daga ƙasar Indiya. Ƙwayoyin, waɗanda nauyinsu sun kai kilogiram 90, kuma aka loda su a cikin wata motar kasuwanci mai lamba RSH 691XC a Ojuelegba, Legas, an kama su ne a yayin da ake gudanar da bincike a kan babban titin Umuahia-Ikot Ekpene da ke Legas a ranar Asabar 6 ga…
Read More
‘Yan bindiga sun harbe babban jami’in Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya

‘Yan bindiga sun harbe babban jami’in Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu' 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe babban jami'in Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya (FIRS), Mohammed Kudu a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Lafiagi ta Jihar Kwara. Jaridar This Day ta ruwaito babban jami'in watsa labarai na shugaban hukumar, Johannes Wojuola yana tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai. Kudu, wanda shi ne babban jami'in hukumar da ke kula da jihohin Kebbi, Sakkwato da Zamfara, 'yan bindiga sun kashe shi ne ranar Lahadi. Sanarwar ta bayyana cewa, "Hukumar Tattara…
Read More
Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da Ministan Abuja da Ministan Sufuri

Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da Ministan Abuja da Ministan Sufuri

Daga CMG HAUSA Jakadan Sin dake Najeriya Cui Jianchun, ya gana da Ministan Abuja Muhammadu Bello da sabon Ministan Sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, inda suka tattauna game da haɗin gwiwar ƙasashen biyu. Taron wanda ya gudana a jiya, ya kuma samu halartar shugaban kamfanin CCECC mai ayyukan gine gine, dake ziyara a ƙasar, Liu Weimin. Yayin ganawa tsakankin Cui Jianchun da Muhammadu Bello, sun waiwayi ci gaban da ɓangarorin biyu suka samu na haɗin kai a yankin hedkwatar ƙasar da ayyukan da suka ciyar da haɓakar tattalin arziki da samar da ilmi. Kuma ɓangarorin biyu sun kai ga matsaya cewa,…
Read More
‘Yan bindiga sun sace amarya da ango tare da kashe mutum biyu a garin Katsina

‘Yan bindiga sun sace amarya da ango tare da kashe mutum biyu a garin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu mutane ɗauke da bindigogi sun sake yin dirar mikiya a cikin birnin Katsina a wata unguwa mai suna Shola Quarters dake maƙotaka da asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya dake jihar Katsina. Wani Mazaunin unguwar ya shaida wa Manhaja cewa 'yan ta'addar sun shigo unguwar ne da misalin ƙarfe 1 da rabi na ranar Lahadi wayewar garin Litinin. Ya ci gaba da cewa 'yan ta'addar sun afka gidan wasu sababbin amare bayan da suka fasa gidansu ta baya inda su ka sace amaryar da angonta su ka kuma gudu da su 'yan ta'addar waɗanda su…
Read More
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta buƙaci zama da Shugaba Buhari a kan tsaron jihar

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta buƙaci zama da Shugaba Buhari a kan tsaron jihar

Daga UMAR GARBA a Katsina Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta fusata akan matsalar rashin tsaro dake cigaba da ƙara ƙamari a ƙauyuka da ƙananan hukumomin jihar wadda yanzu ta game har da babban birnin jihar. Ɗaya daga cikin 'yan majalisar Abubakar Muhammad Total wanda ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Funtuwa ya bayyana cewar matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka ba su da wani amfani illa ƙara takura al'ummar jihar saboda a cewarsa matakan ba su hana 'yan ta'adda ci gaba da kai hare-hare ba. Ya bada misali da dokar katse layukan sadarwa a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar. "A ƙasa…
Read More
Ziyarar da Pelosi ta kai Taiwan tamkar zagon ƙasa ne ga dimukuraɗiyya

Ziyarar da Pelosi ta kai Taiwan tamkar zagon ƙasa ne ga dimukuraɗiyya

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya musanta kalaman kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi game da yankin Taiwan, a taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Jumma’a, inda ya nuna cewa matakin da Pelosi ta dauka na zuwa Taiwan, ba shi da wata alaka da dimokuraɗiyya, illa dai tauye tsarin dimokuradiyya, kuma hakan ya nuna yadda Amurka ta dora son kai sama da adalci na ƙasa da ƙasa. Rahotanni sun bayyana cewa, kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, da wasu 'yan majalisar da suka halarci ziyarar yankin Asiya, sun…
Read More
’Yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan ta sake kafa tarihi a wasan guje-guje

’Yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan ta sake kafa tarihi a wasan guje-guje

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ’Yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan ta yi nasarar kare kambunta na gasar tseren mita 100 na ƙasashe renon Ingila, wato Commonwealth, bayan da ta kai matakin farko a ranar Lahadi a filin wasa na Alexander da ke Birmingham. ’Yar wasan ta sake kafa sabon tarihi bayan da ta kammala tseren mita 100 cikin daƙiƙa 20 da sakan 30, wanda hakan ya ba ta damar lashe lambar zinare ga ƙasarta Nijeriya. Mai riƙe da kambun gasar ta duniya ta kawo ƙarshen tarihin tseren daƙiƙa 16 da sakan 65 da Brigitte Foster-Hylton ta Jamaica ta kafa a Melbourne,…
Read More
Akwai alamun ba gudu ba ja da baya a kan batun Taiwan

Akwai alamun ba gudu ba ja da baya a kan batun Taiwan

Daga LAWAL SALE Hausawa dai na cewa: "komai nisan jifa, kasa za ta dawo". A nan ina ma nuni da batun Taiwan a kan cewa ko ba daɗe, ko ba jima, Taiwan za ta dunƙule ko kuma za ta haɗe da jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, kasancewar Taiwan wani yanki ne ƙarƙashin ƙasar ta Sin. A kwanan nan ne ofishin kula da harkokin Taiwan da na watsa labarai na majalisar gudanarwa ta ƙasar Sin a Beijing suka fitar da wata takardar bayani ƙaƙƙarfa mai taken "batun Taiwan da dunƙulewar ƙasar Sin a sabon zamani". Takardar dai tana ƙunshe da gargaɗi da…
Read More
PADWO ta karrama Sanata Yahaya a Kebbi

PADWO ta karrama Sanata Yahaya a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ƙungiyar nan mai rajin taimaka wa marasa lafiya musamman marasa galihu (Patients and Destitute Welfare Organization (PADWO), da ke garin Argungu ta karrama Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa, tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa. Da ya ke jawabi a madadin Sanata Dokta Yahaya Abubakar, babban hadiminsa Alhaji Bilyaminu Bawale Sardaunan Matasan Kabi, ya yaba wa wannan ƙungiyar bisa ga zaƙulo mutanen da ke taka muhimmiyar rawa wajen bayar da gudunmawar cigaban al'umma, wanda ba shakka zai zaburar da waɗansu don su ma su bayar da nasu gudummawar. Haka…
Read More
Sarkin Musulmi ya jagoranci gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a Nijeriya

Sarkin Musulmi ya jagoranci gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a Nijeriya

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Mai Alfarma Sarkin Musulmi kana Shugaban Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a Nijeriya, Alh Muhammad Sa'ad Abubakar III ya jagoranci gudanar da addu'o'in samun zaman lafiya kan matsalar tsaro da ta addabi sassan Arewa da ma ƙasa baki ɗaya. A wajen taron gudanar da addu'o'in da aka gudanar a masalacin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, babban limamin masallacin Juma'a na Sarkin Musulmi Muhammad Maccixo, Dr. Muhammad Sani Ɗangwaggo ya gabatar da ƙasida mai taken: 'Muhimmancin Zaman Lafiya da Hanyoyin Tabbatar da Shi. Manyan malamai ne dai dake a Sakkwaton da suka haɗar da Sarkin Malaman Sakkwato, Limamin…
Read More