Editor

9513 Posts
Za a ƙaddamar da gasar Super League a Afirika

Za a ƙaddamar da gasar Super League a Afirika

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Afirika, Patrice Motsepe zai ƙaddamar da gasar Super League ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Afrika, tare da alƙawarin dala miliyan ɗari ga ƙungiyoyin nahiyar. Tun da shugaban hukumar ƙwallon ƙafar duniya, FIFA, Gianni Infantino ya bada shawarar gasar a farkon shekarar 2020 ne ake ta shiri tare da ƙoƙarin tsara gasar, kuma babu irin turjiyar da makamancin wannan yunƙuri ya gamu da shi a Turai cikin shekarar da ta gabata. Ƙungiyar ’yan wasa a Afrika ta Kudu ce kawai ta soki wanna shiri a wata sanarwa da ta fitar a wannan mako, inda…
Read More
An canja jadawalin fara gasar kofin duniya

An canja jadawalin fara gasar kofin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Za a fara gasar kofin duniya ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba, inda Ƙatar mai masaukin baƙi za ta kara da Ecuador. Tun farko an tsara karawar rukunin farko ranar 21 da ƙarfe 16:00 agogon GMT, kuma wasan Ƙatar shi ne na uku daga cikin wanda aka tsara yi. An shirya da buɗe gasar da wasa tsakanin Senegal da Netherlands ranar Litinin 22 ga watan Nuwamban. Daga baya FIFA ta karɓi ƙorafi daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Kudancin Amurka da ake kira Conmebol, wadda ta ce bisa al'ada ana bikin buɗe gasa ko dai da mai…
Read More
Ɗan Shugaba Buhari ya fice daga Jam’iyyar APC

Ɗan Shugaba Buhari ya fice daga Jam’iyyar APC

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Daura, Sandamu da Mai'Adu'a kuma ɗa ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wato Fatuhu Muhammad ya fice daga Jam'iyyar APC mai mulki. Bayanin haka yana ƙunshe ne cikin wata takarda da ɗan majalisar ya rubuta wa majalisar wakilai ta ƙasa don sanar da ita matakin da ya ɗauka. Takardar wadda aka rubuta tun 13 ga watan Yuli, 2022 amma ba a fitar ba sai ranar 7 ga watan Agusta, 2022. A takardar da aka raba wa manema labarai a birnin Katsina, Hon. Fatuhu ya bayyana cewar daga ranar 13…
Read More
Zaɓen 2023: Ban janye daga takarar Gwamnan Yobe a PDP ba – Hon. Shariff

Zaɓen 2023: Ban janye daga takarar Gwamnan Yobe a PDP ba – Hon. Shariff

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Ɗan takarar Gwamnan Jihar Yobe a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, a zaɓen 2023 mai zuwa, Hon. Shariff Abdullahi ya ƙaryata jita-jitar janye takararsa tare da mayar da martanin cewa wannan farfaganda ce maras tushe da makama. Ya jadada cewa babu wannan magana; ba a yi ta ba kuma babu alamarta, face kawai ƙarya ce tsagwaronta wadda wasu maras tunani suka ƙirƙira tare da yaɗa ta domin sanyaya gwiwar magoya bayansa. Hon. Shariff Abdullahi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labaru mai ɗauke da sa hannunsa, wadda aka raba wa 'yan jaridu ranar Litinin a…
Read More
Dariye da Nyame: Ya kamata Buhari ya san cewa dukiyar Nijeriya ba ta shi ba ce – Hajiya Naja’atu

Dariye da Nyame: Ya kamata Buhari ya san cewa dukiyar Nijeriya ba ta shi ba ce – Hajiya Naja’atu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohuwar 'yar a mutum Buhari, Hajiya Naja’atu Mohammed, ta caccaki Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba. Daily Nigerian ta ruwaito yadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a watan Afrilu ya yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke faɗin ƙasar nan. An yanke wa Dariye, wanda ya riƙe kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar Naira biliyan 1.16, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan…
Read More
Hisba ta aske gashin ɗaliban da suka yi askin banza don murnar gama makaranta a Kano

Hisba ta aske gashin ɗaliban da suka yi askin banza don murnar gama makaranta a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Hisba ta Jihar Kano, reshen Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta kai wani samame babbar Makarantar Sakandare ta Grammar da ke garin Dawakin Tofa, inda ta kama wasu ɗalibai da askin banza a kansu, domin murnar kammala karatun sakandire. Dakarun Hisba ɗin sun yi nasarar damƙe da dama daga cikin ɗaliban, waɗanda su ka yi askin da a ke wa laƙabi da "ba kwaɓa". Bayan dakarun sun kama ɗan na kamawa, wasu kuma sun tsere, sai su ka zaunar da su a harabar makarantar, inda su ka aske musu gashin tas. Wannan na ƙunshe ne…
Read More
Hukumar NAHCON ta kammala aikin hajjin bana

Hukumar NAHCON ta kammala aikin hajjin bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai (NAHCON), ta sanar da kammala aikin hajji na bana. Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta yi jigilar mahajjata na ƙarshe daga filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jiddah zuwa Nijeriya. Hajiya Fatima Sanda, Shugabar Sashin Hulɗa da Jama'a na Hukumar ne ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar. Ta ce, jirgin Nijeriya na ƙarshe na aikin Hajji na 2022, jirgin Azman Air mai alhazai 319 daga Kaduna da Kano da jami'ai daga jihohi daban-daban da NAHCON ya tashi daga filin jirgin sama na Sarki…
Read More
Fulaninmu na cikin wani hali a Jihar Edo, inji Sarkin Sarakunan Fulanin jihar

Fulaninmu na cikin wani hali a Jihar Edo, inji Sarkin Sarakunan Fulanin jihar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Sarakunan Fulanin Jihar Edo, Alhaji Muhammadu Sossa ya yi kira ga gwamnatin jihar Edo da ta yi wa Allah da AnnabinSa ta janye dokar da tasa na korar Fulani a jihar baki ɗaya nan da kwana biyar. Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai akan hukuncin kwana 5 da gwamnatin ta ba kowane Bafulatani ya bar jihar. Sarki ya ce a gaskiya ɗaukar wannan mataki zai cutar da Fulanin da ke zaune a dukkan faɗin jihar bisa ga yadda mafi yawan Fulanin dake zaune a jihar…
Read More
Makarantar Mariri Community ta shirya taron bankwana da ɗaliban zangon ƙarshe

Makarantar Mariri Community ta shirya taron bankwana da ɗaliban zangon ƙarshe

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A ƙoƙarin ta na buƙasa ilimi mai inganci da tarbiyya. Makarantar Mariri Community Nursery and Primary and Secondary School. Ta shirya wani gagarumin taro domin karramawa tare da Bankwana da ɗaliban da suka zo zangon Karatun su na ƙarshe a makarantar. Taron wanda aka gudanar da shi a ranar Asabar 5 ga Agusta, 2022, a harabar makarantar da ke Unguwar Mariri ta Ƙaramar Hukumar Kumbotso a cikin jihar Kano, ya samu halartar nanyan baƙi da ɗaliban makarantar. Tun da farko da ya ke gabatar da jawabi a game da shirya taron ɗaya daga cikin daraktocin…
Read More
DSS ta buƙaci ‘yan jarida da su tabbatar da ingancin labari kafin wallafawa

DSS ta buƙaci ‘yan jarida da su tabbatar da ingancin labari kafin wallafawa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta DSS, Kwamanda Hassan I. Muhammad ya buƙaci 'yan jarida da su haɗa kai da hukumar wajen samar da tsaro da haɗin kai da zaman lafiya a Nijeriya. Daraktan ya yi wannan kiran ne yayin da yke karɓar baƙuncin shuganni da mambobin ƙungiyar 'yan jarida masu yaɗa labarai a shafukan sadarwa na zamani wato Association of Kano Online Jounalist a ranar Laraba da ta gabata. Hassan I Muhammad ya ce kafar yaɗa labarai ta internet kafa ce mai sauƙi, da ake yaɗa labaran ƙarya da ke haddasa ruɗani da…
Read More