Editor

9513 Posts
Kawar da ciwon hanta kafin 2030

Kawar da ciwon hanta kafin 2030

A baya-bayan nan ne ƙasashen duniya suka gudanar da bikin ranar yaƙi da cutar Hepatitis wanda ake kira da ciwon hanta a Hausance, domin ƙara wayar da kan jama’a game da wannan mummunar cuta da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka haɗa da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta nau'in B da C a duniya. A yayin da ciwon hanta nau'in B kawai ke lashe…
Read More
Ɗan majalisa ya tallafa wa al’ummarsa don rage fatara

Ɗan majalisa ya tallafa wa al’ummarsa don rage fatara

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato A wani mataki na ƙarfafa wa da kuma tallaffa wa al'ummar ƙananan hukumomin Gwadabawa da Illela dake a Jihar Sakkwato, ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Gwadabawa da Illela a Majalisar Tarayya, Abdullahi Balarabe Salame ya raba kayayyaki ga al'ummar da yake wakilta na maƙudan nairori. A cewar ɗan majalisar wannan ya zama wajibi domin rage wa al'umma raɗaɗin talauci da suke fama da shi. Salame ya ƙara da cewa tallafi ba shakka ya zama tilas kasancewar matsalar talauci da kuma rashin aikin yi ya jefa al'umma cikin ayukkan assha. Shi ma da yake magantawa…
Read More
Addu’a ce takobin dukkan ayyukan ta’addanci – Falakin Ƙaraye

Addu’a ce takobin dukkan ayyukan ta’addanci – Falakin Ƙaraye

Daga DAUDA USMAN a Legas An bayyana cewar gudanar da addu'o'i na musamman kan zaman lafiya ita ce takobin kowane irin ƙalubale da ke addabar Nijeriya. Alhaji Bature Ƙaraye kuma Falaƙin Ƙaraye, mazaunin Legas shi ne ya bayyana haka bayan kammala ɗaurin aurensa a Kano, inda aka yi addu'ar nema wa Nijeriya zaman lafiya da yalwar arziki mai amfani. Taron ɗaurin auren dai ya gudana ne a Masallacin Sheikh Jaafar da ke Unguwar Ɗorayi a cikin birnin Kano, inda ya samu halarta manyan baƙi da nesa da na kusa, haɗi da shuwagabannin majalisar Kasuwar Mile 12 da ke Legas irinsu…
Read More
Uba da ɗansa sun rasa ransu bayan sun faɗa rijiya a Kano

Uba da ɗansa sun rasa ransu bayan sun faɗa rijiya a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wani magidanci ɗan shekara 60, Malam Bala tare ɗan sa Sunusi Bala, mai shekaru 33 sun faɗa wata tsohowar rijiya da ke Sabon Garin Bauchi, a ƙaramar hukumar Wudil, da ke cikin garin Kano, inda suka rasa rayukansu kafin a kai ga cetosu. Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da mutuwar su ranar Laraba da ta gabata a Kano, inda ya ce uba da ɗan nasa sun rasu ne yayin da suke  ɗibar ruwa a rijiya. Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata da…
Read More
2023: Sarkin Musulmi da CAN sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

2023: Sarkin Musulmi da CAN sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) sun rattaba hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya gabanin babban zaɓen 2023. Yarjejeniyar dai ana sa ran ta samar da zaman lafiya da kawar da fitina ta fuskar addini a lokacin zaɓen na baɗi. Manyan masu faɗa a jin biyu sun sa hannu ne a wani taron ƙoli na qasa da ƙasa kan wanzar da ’yancin addini da wata gidauniyar samar da zaman lafiya da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama guda 70 suka shirya. An gudarnar da taron…
Read More
2023: Ba mu amince da saka sunayen Lawan da Akpabio a matsayin ‘yan takarar Sanata ba – INEC

2023: Ba mu amince da saka sunayen Lawan da Akpabio a matsayin ‘yan takarar Sanata ba – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan matsayin ‘yan takarar sanata a Yobe ta Arewa da Godswill Akpabio a matsayin ɗan takarar sanata a Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba. Hukumar INEC ta ce ba ta ɗauki ɗaya daga cikin mutanen biyu a matsayin 'yan takarar Sanata a zaɓen 2023 mai zuwa ba. Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar…
Read More
Yunƙurin tsige Shugaba Buhari abin takaici ne – Adamu

Yunƙurin tsige Shugaba Buhari abin takaici ne – Adamu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana yunƙurin tsige Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da wasu 'yan majalisun tarayya suka yi da wani lamari abun takaici ne. Adamu ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da kafar talabijin ta Trust TV ranar Talata, 9 ga watan Agusta, 2022 a birnin tarayya Abuja. Idan ba ku mance ba Manhaja ta kawo muku rahoton cewa 'yan majalisun tarayya sun yi barazanar fara bin matakan tsige Shugaban ƙasa daga kujerarsa a wani taron manema labarai jim kaɗan kafin tafiyar su hutun watanni biyu. Mambobin…
Read More
Ƙasar Sin ta miƙa wasu takardun amincewa da yarjejeniyoyi biyu ga ILO

Ƙasar Sin ta miƙa wasu takardun amincewa da yarjejeniyoyi biyu ga ILO

Daga CMG HAUSA Wakilin din-din-din na ƙasar Sin a ofishin MƊD dake birnin Geneva, da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa dake kasar Switzerland Chen Xu, ya mika wa babban darektan hukumar Ƙwadago ta Ƙasa da Ƙasa wato ILO a taƙaice, takardu guda biyu, game da amincewar da ƙasar Sin ta yi da Yarjejeniyar Aikin Tilas ta shekarar 1930 mai lamba 29, da ta Kawar da Yarjejeniyar Aikin Tilas ta shekarar 1957 mai lamba 105. Yarjejeniya ta 29 da ta 105, na cikin muhimman yarjejeniyoyi 10 na ILO, kuma su ne dokokin ƙasa da ƙasa mafi mahimmancin a fagen kawar da…
Read More
An buɗe bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa karo na 12 na birnin Beijing

An buɗe bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa karo na 12 na birnin Beijing

Daga CMG HAUSA A yau Asabar ne aka buɗe bikin nuna fina-finai na ƙasa da ƙasa karo na 12 a nan birnin Beijing. Shen Haixiong, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin faɗakar da al’umma na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban babban rukunin gidan rediyo da talabijin na ƙasar wato CMG, kana shugaban kwamitin shirya bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa karo na 12 na birnin Beijing, ya gabatar da jawabi, tare da sanar da buɗe bikin. Taken bikin fina-finan na wannan shekara shi ne "Zuciya ɗaya, aikata na haƙiƙa", wanda kuma ke gayyatar masu aikin shirya fina-finai daga duk…
Read More
Sin ta sanya wa Mataimakiyar Ministan Sufurin Ƙasar Lithuania takunkumi

Sin ta sanya wa Mataimakiyar Ministan Sufurin Ƙasar Lithuania takunkumi

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, ya sanar da ƙaƙaba wa mataimakiyar ministan sufuri da sadarwa na ƙasar Lithuania Agne Vaiciukeviciute takunkumi. Hakan dai ya biyo bayan ziyarar da jami’ar ta kai yankin Taiwan, lamarin da ya keta alfarmar manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, tare da tsoma baki cikin harkokin gidan ƙasar, da keta hurumin mulkin kai, da tsaron yankunan ƙasar Sin. Takunkumin da ƙasar Sin ta kakabawa Vaiciukeviciute, ya haɗa da dakatar da dukkanin wata musaya, tsakanin ɓangaren Sin da ma’aikatar da jami’in ke wakilta, da kuma jingine duk wata haɗin gwiwa da musaya…
Read More