Editor

9513 Posts
Ku daina ziyarar alƙalai cikin dare, inji Alƙalin Kotun Ƙoli

Ku daina ziyarar alƙalai cikin dare, inji Alƙalin Kotun Ƙoli

Daga AMINA YUSUF ALI Alƙalin Kotun Ƙolin Nijeriya, Mai Shari'a Inyang Okoro, ya bayyana cewa, Sashen Shari'a na ƙasar nan ba za ta taɓa yin aikinta yadda ya kamata ba har sai ta tsira daga matsalar tauye haƙƙi daga gwamnatocin jihohi. Wanda ya haɗa da kai ziyara zuwa gidajen alƙalai domin ƙara wa miyarsu gishiri.  Okoro ya bayyana haka ranar Juma'a a garin Abuja yayin taron laccar da ƙungiyar ma'aikatan Shari'a ta Nijeriya (NBA) ta shirya mai taken: 'Tauye ikon sashen Shari'a a mulkin demokraɗiyya: Dalilansa, sakamakonsa, da kuma mafita'. Mai Shari'ar ya ƙara da cewa, in dai wannan ta'adar…
Read More
Ma’aikatu da hukumomin gwamnati sun tsaya cak sakamakon rashin sakin kasafin 2022

Ma’aikatu da hukumomin gwamnati sun tsaya cak sakamakon rashin sakin kasafin 2022

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai ma'aikatu, sassa da kuma hukumomin gwamnati (MDA) da kuma kamfanonin gine-gine da sauransu sun shiga matsanancin ƙarancin kuɗi a sakamakon jinkirin sakin kasafin kuɗi na shekarar 2022 da ya sa maiakatun suka tsaya cak suka kasa gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa.  A yanzu haka Ma'aikatun da sassa da kuma hukumomin gwamnati (MDA) waɗanda su ne suka fi buƙatuwa da a saki waɗancan kuɗaɗe na kasafin wanda aka ware domin ayyukan raya ƙasa sayen kayan aiki, da sauransu, sun shiga guna-guni a kan jinkirin da aka samu na qin sakin kuɗaɗen bayan…
Read More
Badaƙalar kuɗi: Gwamna Atiku na fafutukar sasantawa da Amurka a bayan fage

Badaƙalar kuɗi: Gwamna Atiku na fafutukar sasantawa da Amurka a bayan fage

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya roƙi Gwamnatin Ƙasar Amurka da ta yi wa Allah ta bari a sasanta zargin badaƙalar Dalar Amurka milliyan ɗari da arba'in ($140,000,000:00), wanda ya yi daidai da Naira Billiyan Hamsin da Takwas da ɗigo Uku (#58.3b), waɗanda tsohon Shugaban Nijeriya, Marigayi Janar Sani Abacha, ya ƙetare da su zuwa ƙasashen waje, waɗansu masu bincike suka gano da hannun Gwamna Atikun dumu-dumu a ciki. Kamar yadda Jaridar Premium Times ta ruwaito a shafinta ta ce, shari'ar, wacce ke gudana tsakanin sashen shari'a na Ƙasar Amurka, (US Department of Justice, USDOJ)…
Read More
Hukumomi a Tunisia sun yi watsi da matakin gwamnati na sallamar alƙalai

Hukumomi a Tunisia sun yi watsi da matakin gwamnati na sallamar alƙalai

Hukumomin shari'a a Tunisia sun soke korar da shugaban ƙasar Kais Saied ya yi wa alƙalai kusan 50 a farkon watan Yuni. Matakin shugaban ƙasa na ranar 1 ga watan Yuni na sallamar alƙalai 57 a ƙasar da ke arewacin Afirka, na zuwa ne bayan ya zargi da dama da cin hanci da rashawa da sauran laifuka. Matakin nasa, wanda ƙungiyoyin kare hakkin bil-Adama suka kira "babban rauni ga 'yancin shari'a", ya haifar da yajin aikin alkalai a faɗin ƙasar. Hamsin da uku daga cikin waɗanda aka kora ciki har da wasu da ake zargi da neman matan da ba…
Read More
‘Yan cirani fiye da 50 sun ɓace a tekun Aegean na Italiya bayan tasowa daga Turkiya

‘Yan cirani fiye da 50 sun ɓace a tekun Aegean na Italiya bayan tasowa daga Turkiya

Jami’an tsaron gavar tekun Girka sun sanar da ɓacewar ‘yan cirani akalla 50 bayan kifewar kwale-kwalen da su ke ciki a tsakar tekun Aegean, akan hanyarsu ta shiga Italiya. Jami’an tsaron gaɓar tekun Girka sun sanar da gano kwale-kwalen a gab da tsibirin Karpathos da na Rhodes wanda ya taso daga birnin Antalya da ke kudancin Turkiya, gabanin igiyar ruwa ta kifar da jirgin. Jami’an agajin da suka yi nasarar ceto ‘yan cirani 29 sun ce jirgin ya taso daga Turkiya ne ɗauke da mutane fiye da 80 kuma ya na kan hanyarsa ta zuwa Italiya gabanin haɗarin inda zuwa…
Read More
Ɓarayi sun shiga Gidan Muhammadu Buhari sun ɗibga wa Gwamna Masari sata

Ɓarayi sun shiga Gidan Muhammadu Buhari sun ɗibga wa Gwamna Masari sata

Daga UMAR GARBA a Katsina Rahotannin da Manhaja ke samu yanzu na nuni da cewa wasu ɓarayi da kawo yanzu ba a san ko su waye ba sun sulala cikin gidan Muhammadu Buhari, wato Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, inda ake zargin sun sace maƙudan kuɗaɗe da suka kai har Naira Miliyan 31. Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da aka taɓa tafka sata a gidan gwamnatin, domin kuwa a shekara ta 2020 an sace kuɗin da suka kai Naira Milyan 16 a Ofishin tsohon sakataren gwamnatin jihar lamarin da masana ke ganin cewar wasu daga cikin jami'an…
Read More
’Yan bindiga sun fasa Jihar Jigawa, sun kashe jami’in tsaro

’Yan bindiga sun fasa Jihar Jigawa, sun kashe jami’in tsaro

*Mun fatattake su zuwa cikin daji, inji ACG Abba Daga Abubakar Muhammad Tahir  ’Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun halaka jami'in shige da fice tare da raunata guda biyu daga cikin jami'an hukumar. Cikin wata ganawa da manema labarai da Shugaban Hukumar na Jihar Jigawa, ACG Ismail Abba, ya yi da manema labarai a ranar Laraba a Dutse, Babban Birnin Jihar ta Jigawa, ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misali qarfe 11:20 na dare lokacin da ’yan bindigar suka nufo shingen bincike na hukumar da ke yankin Birniwa-Galadi. Ya ƙara da cewa, 'yan bindigar sun zo a babura…
Read More
Gwamna Buni zai jagoranci taron Kamfanin Blueprint

Gwamna Buni zai jagoranci taron Kamfanin Blueprint

*An tsayar da ranar Talata don gudanar da gagarumin taron*Za a karrama Atiku, Tinubu, Tambuwal, Yahaya Bello da sauransu*Janar Dambazau zai bajekoli a wajen taron Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Talata, 16 ga Agusta, 2022, ne Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe zai jagoranci bikin bayar da kyaututtukan yabo na Kamfanin Blueprint, wanda ke buga jaridun Bueprint da Manhaja, inda aka shirya gudanarwa a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa ‘International Conference Centre’, da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya. Babban Jami’in Gudanarwa na Blueprint (COO), Malam Salisu Umar, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin a wata…
Read More
Nasiha ga matan da za a yi wa kishiya

Nasiha ga matan da za a yi wa kishiya

Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabin Rahma, Muhammad (SAW). Ki zama mai mayar da al'amuranki ga sarki Allah, shi ne ya zama gatanki majiɓincin al'amuranki, in ki ka yi haka, kin tsira daga zuwa wajen bokaye da ’yan duba don ƙulla makirci. Ki kasance mai yarda da ƙaddara domin kuwa tuntuni Allah ya hukunta za ku zauna ƙarƙashin miji ɗaya. Ki sanya wa ranki cewar mijinki ya yi riƙo ne da sunnar Annabi SAW. Ki zama mai haƙuri saboda Allah, ba mai haƙurin tilas ba. Karki takurawa mijinki a kan…
Read More
Muhimmancin zama mutumin kirki

Muhimmancin zama mutumin kirki

Masu karatu, assalamu alaikum. A wannan makon za mu duba wani sabon maudu’in ne na daban. Wato bayani game da halayyar zama da abokai da ƙawaye. Dalili ke nan ma kanun madu’in namu ya yi tambaya, shin ko kana son zama mutumin kirki a rayuwarka? Ke ma ’yar uwa, ko kina son ki zama mutunniyar kirki a rayuwarki ta duniya? To ku biyo ni a cikin wannan madu’i, domin ganin matakan da suka kamata mu ɗauka, mu aiwatar a rayuwarmu ta yau da kullum, domin ganin mun cimma matsayin zama na kirki a rayuwa. A rayuwa, ɗan Adam ba zai…
Read More