15
Aug
Daga AMINA YUSUF ALI Babban Kotun Tarayyar ta Abuja ta ba da umarnin garƙame shalkwatar Bankin First Bank a kan bashi. Bankin ya kasance babban bankin Kasuwanci a faɗin Nijeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne dai jami'an kotun suka yi dirar mikiya a Shalkwatar bankin domin ƙwace wasu kayayyaki mallakin bankin. Hakazalika, rahotannin sun ƙara bayyana cewa, bijire wa umarnin kotun ne ya sa jami'an kotun suka fita a Shalkwatar dake Abuja da motocin janwai domin ƙwace wasu kayayyaki mallakin kotun kamar injin janareto da manyan motoci. A cikin kayan da aka ɗauka har…
