Editor

9513 Posts
Za mu samu kason ƙuri’un da muke buƙata a Kudu maso Gabas – Shugaban APC

Za mu samu kason ƙuri’un da muke buƙata a Kudu maso Gabas – Shugaban APC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa, jam'iyyar na sa ran samun sama da kashi 25 na ƙuri’un ’yan yankin Kudu maso Gabas. Ya yi magana ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da kwamitin sulhu na mutane takwas a jihar Abia ƙarƙashin jagorancin Sanata Chris Adighije. Adamu ya buƙaci shugabannin shiyyar da su tashi tsaye wajen kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su kuma yi ƙoƙarin ganin jam’iyyar ta samu nasara a babban zaɓe. Ya ce, “Bari Abia su je su daidai tare. Duk zavukan ƙasa – ‘yan majalisar wakilai, dattijai,…
Read More
Ya kamata gwamnati ta ƙara wa’adin rajistar zaɓe, cewar ’Yar takarar kansila a Sakkwato

Ya kamata gwamnati ta ƙara wa’adin rajistar zaɓe, cewar ’Yar takarar kansila a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato An bayyana buƙatar da ke akwai ga Gwamnatin Tarayya da ta duba yuwar ƙara wa'adin ci gaba da rajistar masu zaɓe, da hukumar INEC ta dakatar. Wata 'yar takarar kansila a mazaɓar Sanyinnan dake Ƙaramar Hukumar mulkin Tanmbuwal Hajiya Daraja Shehu Sanyinnan ce ta yi wannan kiran cikin wani bayani da ta fitar. Ta bayyana cewa ƙara lokacin rajistar masu zaɓen zai bayar da dama ga waɗanda suka kai munzalin jefa ƙuri'a yankar rijistar domin su samu damar jefa ƙuri'a a babban zaɓen gamagari da ke tafe. Haka ma Daraha Shehu ya yaba wa matar…
Read More
Sakkwato za ta kashe Naira biliyan 12 wajen sanya na’urorin kiwon lafiya a asibitin koyarwar jihar

Sakkwato za ta kashe Naira biliyan 12 wajen sanya na’urorin kiwon lafiya a asibitin koyarwar jihar

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa a mako mai zuwa ne za a soma sanya kayan aiki ga asibitin koyarwa ta Jami'ar jihar. Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato Dr. Ali Mohammad Inname ne ya sanar da haka a yayin gudanar da wani taro da wakilan kamfanin da aka bai wa aikin Thomat Company Nigeria Ltd, taron da ya gudana a harabar asibitin. Dr. Muhammad Ali Inname, ya ce wannan ya biyo bayan amincewar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na cefano kayakin tare da sanya su, kuɗin da suka kai kimanin Naira Biliyan 12. A cewarsa, za…
Read More
Matsalar tsaro: Sufeto Janar ya bada umarnin tattara bayanan babura

Matsalar tsaro: Sufeto Janar ya bada umarnin tattara bayanan babura

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja A cikin fargabar taɓarɓarewar tsaro a sassan Nijeriya da ke haifar da kashe-kashe da raunata ’yan ƙasa a kowace rana, Sufeto Janar na ’yan sanda Nijeriya, Usman Alkali Baba ya umarci mataimakin sufeto Janar na ’yan sanda na shiyoyin ’yan sandan Nijeriya da kwamishinonin ’yan sanda na jihohin ƙasar nan da su fara tattara bayanan duk wani babura da masu tuƙa babur mai ƙafa uku da ke yankunansu domin tsaron lafiyar ’yan ƙasa. Alkali ya kuma amince da gudanar da wani muhimmin taron ƙara wa juna sani kan harkokin tsaro na ɗaukacin sassan AIGs,…
Read More
’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 13 a kusa da Birnin Katsina

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 13 a kusa da Birnin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu gungun mutane ɗauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun sace mutane 13 a garin Natsinta da bai wuce nisan kilomita 5 ba tsakanin sa da babban birnin Jihar Katsina. ’Yan bindigar waɗanda suka yi ɓadda sahu don kuwa sun ajiye baburan su a kusa da wani ƙauye dake maƙotaka da garin na Natsinta inda suka ƙaraso a ƙafa zuwa garin da su ka yi ta'addancin. Wani Hamisu Ahmad da harin ya rutsa da ƙanwarsa ya shaida wa Manhaja cewar 'yan bindigar sun shigo garin da misalin ƙarfe 10:00 na…
Read More
Sokoto: Za a buɗe kwalejin da aka kashe Deborah

Sokoto: Za a buɗe kwalejin da aka kashe Deborah

*An umarci ɗaibai su sa hannu kan kundin hana rarzoma Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Watanni biyo bayan rufe Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari kan tarzoma da kisan ɗalibar da ake zarga da yin ɓatanci ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (SAW), mahukuntan kwalejin sun bayyana ranar sake dawo wa karatu. A zaman da ta yi karo na 79, Hukumar Gudanarwar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari ta amince da sake buɗe kwalejin daga ranar Litinin 8 ga Agustan, 2022. Deborah A bayanin da Magatakardan Kwalejin, Malam Gandi Muhammad Asara, ya fitar, ya bayyana buƙatar dake akwai ga dukkanin ɗaliban kwalejin da…
Read More
Harin jirgin ƙasa: Har yanzu ni masoyin Buhari ne, inji fasinjan da ya kuɓuta

Harin jirgin ƙasa: Har yanzu ni masoyin Buhari ne, inji fasinjan da ya kuɓuta

Daga SANI AHMAD GIWA Ɗaya daga cikin mutanen da suka kuɓuta daga hannun 'yan bindigar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, Barista Hassan Usman, ya ce har yanzu shi masoyin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne. A ranar 28 ga watan Maris, wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani jirgin ƙasa da ke kan hanyar Kaduna, inda aka kashe mutane da dama, aka kuma yi awon gaba da wasu. Hassan na daga cikin fasinjoji huɗu da aka sako daga hannun masu garkuwar a ranar 25 ga watan Yuli. Da yake magana a wata hira da ICIR, ya ce duk da cewa…
Read More
Ƙaranci da tsananin tsadar burodi a Nijeriya

Ƙaranci da tsananin tsadar burodi a Nijeriya

’Yan Nijeriya na fama da ƙaranci da kuma tsananin tsadar burodi bayan masu gidajen burodi sun fara yajin aiki a faɗin ƙasar. A safiyar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne Babbar Ƙungiyar Masu Gidajen Burodi ta fara yajin aiki, saboda abin da ta kira tashin gwauron zabon kayan haɗa burodi. Tun kafin fara yajin aikin nasu da zai ɗauki tsawon kwana huɗu, ’yan Nijeriya ke ta bayyana damuwa, bayan a wasu wuraren an ninka farashinsa. Shugaban Ƙungiyar Masu Gidajen Burodi da Dangoginsu ta Ƙasa, Emmanuel Onuorah tare da Kakakin ƙungiyar, Babalola Thomas sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da…
Read More
Tashin farashin baƙin mai da canji sun jawo min naƙasu a kasuwancina – Obasanjo

Tashin farashin baƙin mai da canji sun jawo min naƙasu a kasuwancina – Obasanjo

Daga AMINA YUSUF ALI Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya a Jamhuriya ta biyu, Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda tashin farashin baƙin mai da canji suke kawo masa naƙasu a kasuwancinsa. Shugaban ya ƙara da cewa, tashin farashin baƙin man yana da alaka da yadda ake gudanar da mulkin ƙasar nan ba yadda ya kamata ba. A cewar tsohon shugaban, tashin farashin yana jawo cikas sosai a kasuwancinsa na kifi. Mista Obasanjo wanda ya mallaki sashen kiwon kifi a gidansa dake Abeokuta ta jihar Ogun ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Talatar da ta gabata a yayin taron ƙungiyar daidaita…
Read More
Akwai sauran mutanen jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a daji

Akwai sauran mutanen jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a daji

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Za a ji ana sako fasinjojin da ɓarayi su ka sace a harin jirgin ƙasa kan hanyar Abuja zuwa Kaduna tun ranar 28 ga watan Maris ɗin bana 2022 miladiyya, amma har yanzu akwai sauran mutane da ke dajin cikin matuƙar takaici da rashin sanin tabbas. Duk haka su din ma masu nisan kwana ne don lokacin mummunan farmakin fasinjoji 9 su ka gamu da ajali. A wannan lokacin ko ma rai bai yi halin sa ba, ko ba a sace mutum ba, akwai mummunan tashin hankali na rugugin harbin bindiga da firgita marar misali. Waɗanda…
Read More