18
Jun
Daga CMG HAUSA Gomman mutane daga dukkan bangarorin rayuwa ne suka samu damar kallon yadda ƙasar Sin ta yi nasarar fatattakar talauci, a lokacin da aka nuna wani shirin bidiyo na documentary, wanda ya gabatar da baki ɗayan aikin yaƙar talaucin a Abuja, babban birnin Nijeriya. Bayan kammala kallon shirin, mutanen sun bayyana cewa, ya ƙarfafa musu gwiwa, inda suka yi kira da a aiwatar da aikin yaƙi da talauci a Nijeriya. Gidan talabijin na ƙasar Sin CGTN tare da haɗin gwiwar gidauniyar Kuhn ta Amurka ne suka gabatar da shirin mai taken “Voices From The Frontline: China's War On…
