Editor

9513 Posts
Sin za ta taimakawa Tanzania bunƙasa ilimin sana’o’in hannu

Sin za ta taimakawa Tanzania bunƙasa ilimin sana’o’in hannu

Daga CMG HAUSA Ƙasashen Sin da Tanzania, sun ƙaddamar da wani shirin hadin gwiwa dake da nufin bunƙasa ilimin sana’o’in hannu, ta hanyar samar da sabon mizani a ɓangaren, a ƙasar ta gabashin Afrika. Shirin kawance kan ilimin sana’o’in hannu tsakanin Sin da Afrika ne ya ɗauki nauyin sabon shirin na nazari da inganta mizanin ƙwarewar aiki da aka ƙaddamar a ranar Laraba, inda zai gudana ƙarƙashin kulawar majalisar kula da ilimin fasahohi da sana’o’in hannu ta ƙasar Tanzania (NACVET). A cewar Jiang Yilin, sakatare janar na shirin kawancen Sin da Afrika, jimilar kwalejojin koyar da sana’o’in hannu 43 na…
Read More
A bana ne Sin ta samu sakamako mai kyau wajen sa ƙaimi ga yin haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen BRICS

A bana ne Sin ta samu sakamako mai kyau wajen sa ƙaimi ga yin haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen BRICS

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, shekarar bana shekara ce da Sin ta samu sakamako mai kyau wajen sa kaimi ga yin haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen BRICS. Bisa goyon bayan ɓangarori daban daban, ƙasar Sin ta gudanar da taruka da bukukuwa fiye da 70 cikin nasara a matsayin ƙasar dake shugabancin BRICS a wannan karo, matakin da ya taimaka wajen yin haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen BRICS a fannoni daban daban. Wang Wenbin ya bayyana cewa, an samu sakamako mai kyau…
Read More
2023: Zaman ɗar-ɗar kan mataimakin da Tinubu ya zaɓa

2023: Zaman ɗar-ɗar kan mataimakin da Tinubu ya zaɓa

*Ganduje, Shettima da Masari na neman yin zarra*Dogara da Lalong na cigaba da tseren*Atiku ya bayyana dalilinsa na zaɓen Okowa maimakon Wike Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja A daren jiya Alhamis, kimanin awanni 24 kafin ƙarewar wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayar na miƙa ’yan takarar mataimakan Shugaban Ƙasa na jam’iyyun Nijeriya, zaman ɗar-ɗar ya ƙaru kan wanda ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai zaɓa a matsayin wanda zai take masa baya a matsayin ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa sakamakon yanayin yadda lissafin siyasar ƙasar ke…
Read More
Za mu iya sake katse layukan sadarwa a Zamfara – Matawalle

Za mu iya sake katse layukan sadarwa a Zamfara – Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da cewa idan buƙatar sake toshe layukan sadarwa ta taso za a aiwatar da hakan ba tare da wani ɓata lokaci ba. Gwamna Matawalle ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yana musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa za a rufe layukan sadarwa a Zamfara a karo na biyu. Sanarwar ɗauke da sa hannun mataimaki na musamman ga Gwamna Matawalle ya fitar, Zailani Bappa, na cewa duk da cewa kawo yanzu babu wannan maganar a ƙasar, kamar yadda ake yaɗa jita-jita, akwai yiwuwar faruwar hakan…
Read More
‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane takwas a Katsina

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane takwas a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Waɗansu mutane akan babura da ake kyautata zaton masu satar mutane ne don neman kuɗin fansa sun kutsa kai cikin birnin Katsina a wata unguwa mai suna Shola takwas inda su ka sace mutane 8 ciki hadda matar aure da yarta mai kimanin shekaru biyu. Ɓarayin waɗanda su ka yi dirar mikiya a unguwar mai maƙotaka da babban asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya sun yi ta harba bindigar AK47 tare da valle ƙofofin gidajen mazauna unguwar domin samun damar shiga daga ciki don aiwatar da ta'addanci. Wata Binta Abdulmumin ta bayyana wa majiyar Manhaja yadda…
Read More
Mun kashe Naira biliyan bakwai don samar da ingantaccen ilimi – Gwamnatin Kano

Mun kashe Naira biliyan bakwai don samar da ingantaccen ilimi – Gwamnatin Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta ce a wani ɓangare na sauke nauyin tabbatar da ingantacciyar hanyar koyo da koyarwa a makarantu, ta kashe Naira biliyan bakwai. Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka a ranar Talata yayin da ya buɗe taron zangon shekara na biyu da Hukumar Ilimin Bai-ɗaya, UBEC tare da shugabannin zartaswa na SUBEB na ƙasa a ɗakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin Kano. Ganduje ya bayyana cewa, magance ƙalubalen da ke tattare da matsalar rashin zuwan yara makarantu, na ɗaya daga cikin abin da ya sanya jihar Kano…
Read More
Yadda ’yan wasa da magoya bayansu suka fusata suka kashe alƙalin wasa

Yadda ’yan wasa da magoya bayansu suka fusata suka kashe alƙalin wasa

Wani alƙalin wasa ɗan ƙasar Salvadoriya ya gamu da ajalinsa sakamakon raunukan da ya samu a wani harin da ’yan wasa da magoya bayansu suka kai masa. Jose Arnoldo Amaya ya kasance yana jagorantar wani wasa a makon da ya gabata, kuma ya nuna katin gargai na biyu ga wani ɗan wasa, inda ya kore shi saboda rashin ɗa'a. Abin mamaki, wannan ya sa 'yan wasa da magoya bayansu suka yi wa ɗan shekaru 63 ɗin mummunan duka, daga bisani kuma ya mutu sakamakon zubar jini na ciki. Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Salvadoran dai ta yi gaggawar fitar da wata…
Read More
Ɗan takarar Gwamnan Bauchi a APC Farouq Mustapha ya fice daga jam’iyyar

Ɗan takarar Gwamnan Bauchi a APC Farouq Mustapha ya fice daga jam’iyyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Bauchi a zaɓen 2023, Farouk Mustapha, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, Mustapha ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar ne bayan kayen da ya sha a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar. Tsohon shugaban hafsan sojin sama, Sadiq Baba Abubakar ne dai ya lashe tikitin jam’iyyar mai mulki a zaɓen da aka yi na ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu. Sai dai kuma, ɗan siyasar wanda ya…
Read More
Jam’iyyar ADC ce mai manufofin taimakon talakawa – Kwamared Haruna Wakili

Jam’iyyar ADC ce mai manufofin taimakon talakawa – Kwamared Haruna Wakili

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ɗan takarar Majalisar Tarayya a ƙarƙashin Jam'iyyar ADC a Ƙaramar Hukumar Fagge, Kwamared Haruna Kabiru Wakili ya ce jam'iyyar na da kyakkyawar manufofi na kawo cigaba ga rayuwar talakawa. Ya ce tun farko su suka jago-jago da jam'iyyar suka raineta wajen wayar dakan jama'a suka ginata, inda ya kuma zama shugabanta na jiha mafi ƙarancin shekaru; shine kuma ya gayyato Sheik Ibrahim Khalil wanda yake mata takarar Gwamna a Jihar Kano. Ya ce jam'iyyu manya da ake da su sun lura ba sa bai wa matasa dama don kawo sauyi. Don haka suka ɗauki ADC…
Read More
Jama’ar mazaɓar Disina a Jihar Bauchi sun koka kan zaɓen ɗan takarar majalisar dokoki

Jama’ar mazaɓar Disina a Jihar Bauchi sun koka kan zaɓen ɗan takarar majalisar dokoki

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Jama’ar mazaɓar Disina wacce ke da kujerar majalisar dokoki ta jiha sun gabatar da koken su wa zaɓaɓɓen ɗan takarar gwamnan na Jam’iyyar APC, Shugaban rundunar mayaƙa sama na askarawar tarayyar Nijeriya mai ritaya Sadique Baba Abubakar da ya yi wa Allah da Annabi ya duba batun zaven fitar da ɗan takara da aka yi a mazaɓar Disina na shiga majalisar dokoki ta jiha, da zummar daidaita lamarin maguɗi da aka tafka a cikin zaɓen. A wani taron yin jaje da muryar gudanar da gurɓataccen zaɓen da aka yi a kwanakin baya a ranar Lahadi…
Read More