28
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Shugaban Rundunar Sojojin Sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, ya umarci hukumar binciken haɗurran da ta fara bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin ‘Super Mushshak’ na horar sojin sama da ya afku a sansanin sojojin saman Nijeriya (NAF) da ke Kaduna. Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai na Enugu ranar Laraba. Air Commodore Gabkwet ya ce, CAS, yayin ziyarar ta'aziyyar da ya kai ranar Laraba ga iyalan waɗanda haɗarin jirgin ya…
