Editor

9513 Posts
Yajin aikin ASUU: Gwamnatin Nijeriya za ta fara aiwatar da tsarin ‘ba aiki, ba albashi’

Yajin aikin ASUU: Gwamnatin Nijeriya za ta fara aiwatar da tsarin ‘ba aiki, ba albashi’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Alamu na nuni da cewa watakila Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da manufar ‘ba aiki, ba albashi’ domin daƙile yajin aikin da Ƙungiyar Malaman jami’o’i (ASUU) ta dade tana yi. Matakin da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan sanarwa da wasu wasiƙu da hukumar da ke yajin aikin ta aike wa da wasu ƙungiyoyin jami’o’in da suka haɗa da kwamitin haɗin gwiwa na JAC wanda ya ƙunshi NASU da SSANU. Majiyoyin da suka yi magana kan lamarin sun ce gwamnatin Nijeriya ta yi amfani da manufar tsayar da albashin ne a watan Maris ɗin 2022.…
Read More
Hajjin 2022: Maniyyaci zai biya kuɗin kujera sama da Naira miliyan biyu da rabi

Hajjin 2022: Maniyyaci zai biya kuɗin kujera sama da Naira miliyan biyu da rabi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Hukumar Jigilar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta ayyana cewar, kuɗin kujerar zuwa aikin hajji na wannan shekara ta 2022 zai haura Naira miliyan biyu da rabi, fiye da ƙarin kashi hamsin 50 cikin ɗari na Naira miliyan ɗaya da rabi da Alhaji ya biya a shekara ta 2019. Bisa wannan sabon tsari, maniyyata waɗanda suka biya kuɗaɗen ajiya wa hukumomin Alhazai na jihohi tun shekarar 2020, a taƙaice za su biya ƙarin fiye da Naira miliyan ɗaya domin samun damar sauke farali a ƙasa mai tsarki. Shugaban hukumar ta NAHCON, Dokta Zikirullah Hassan shine ya…
Read More
Zaɓen 2023: Hukumar NDLEA za ta yi wa ‘yan takara gwajin ƙwaya

Zaɓen 2023: Hukumar NDLEA za ta yi wa ‘yan takara gwajin ƙwaya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gabanin zaɓen gamagari na shekara ta 2023, shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Birgediya-Janar Buba Marwa ya rubuta wa shugaban jam’iyyar APC dake riƙe da madafun mulki, Sanata Abdullahi Adamu da buƙatar yin gwajin mutumtaka wa masu son tsayawa takarar neman zaɓe mai gabatowa. Marwa ya kuma bayyana cewar, zai rubuta wa shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP makamancin wancan buƙata na gwajin samfurin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi akan dukkan mamban jam’iyya dake sha’awar shiga takarar zaɓe, musamman masu harin riƙe manyan kujerun mulki. Da yake yin jawabi a wajen…
Read More
An ƙaryata rasuwar Raiola

An ƙaryata rasuwar Raiola

Daga MAHDI M. MUSA A halin da ake cikin yanzu, Mino Raiola dai yana fafutukar neman lafiyarsa ne a asibiti, inda wakilin ƙwallon ƙafar ya yi kakkausar suka ga labaran ƙarya da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na cewa ya mutu. Raiola yana wakiltar manyan mutane marasa adadi a manyan wasannin Turai kuma ya taimaka wajen ƙulla manyan yarjejeniyoyin da suka haɗa da Paul Pogba da Zlatan Ibrahimovic. An ruwaito cewa, ɗan ƙasar Italiyan ya rasu yana da shekaru 54 a duniya, inda Raiola ya fitar da wata sanarwa a dandalinsa na sada zumunta inda ya nuna rashin jin…
Read More
Yawan jarin ƙetare da aka zuba wa ƙasar Sin ya ƙaru sosai

Yawan jarin ƙetare da aka zuba wa ƙasar Sin ya ƙaru sosai

Daga CMG HAUSA Hukumar kula da kuɗin musanya ta ƙasar Sin, ta gabatar da wasu alkaluma a jiya Laraba, wadanda suka nuna cewa, an samu wani yanayi na daidaituwa tsakanin kuɗin musanya da kasar Sin ta samu, da wanda ta biya, cikin rubu’i na farko na bana. An ce cikin wannan wa’adi, yawan kuɗin musanya da aka zuba wa kasuwannin ƙasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 107, adadin da ya zama mafi yawa a tarihi. Wasu masana ilimin tattalin arziki sun nuna cewa, yayin da ƙasar Sin ke ci gaba da aiwatar da matakai don tabbatar da ƙaruwar tattalin…
Read More
Ana ƙara samar da guraben aikin yi yadda ya kamata a rubu’in farko na bana

Ana ƙara samar da guraben aikin yi yadda ya kamata a rubu’in farko na bana

Daga CMG HAUSA Bisa ƙididdigar da hukumar ƙwadago ta al’ummar Sin ta samar, mazaunen birane da garuruwa na samun guraben aikin yi yadda ya kamata a rubu’in farkon bana, ƙarƙashin nagartattun manufofi na samar da guraben aikin yi, ciki hadda kara ƙarfin ba da horaswa, da nuna goyon baya ga sana’ar ƙirƙire-ƙirƙire, da ƙara ba da hidimma a wannan fanni da sauransu, inda yawan ƙarin mutanen da suka samun guraben aikin yi ya kai fiye da miliyan 2.85, wanda ya kai kashi 26% na adadin burin da aka tsara. Hukumar ta nuna cewa, za a ci gaba da ingiza manufofi…
Read More
Jakadan Sin a Nijeriya ya halarci bikin ƙaddamar da aikin horaswa

Jakadan Sin a Nijeriya ya halarci bikin ƙaddamar da aikin horaswa

Daga CMG HAUSA Jakadan ƙasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya halarci bikin ƙaddamar da aikin horar da ƙwararrun ma’aikata a fannin aikin sadarwa, a ranar 25 ga watan da muke ciki. Aiki ne da kamfanin Huawei na ƙasar Sin, da ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani ta Najeriya suka yi hadin gwiwar gudanarwa. Sauran manyan ƙusoshin da suka halarci bikin ƙaddamarwar sun hada da ministan sadarwa da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani na Najeriya Isa Pantami, da wakilan wasu jami’o’i guda 8, da dai sauransu. Cikin wani jawabin da ya gabatar wajen bikin,…
Read More
Tasirin azumi a jikin ɗan adam (3)

Tasirin azumi a jikin ɗan adam (3)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ilmintarwa da ƙayatarwa, wanda ke kawo muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ke aiki.  Barkanmu da wannan lokaci na azumin watan Ramadan; fatan Allah ya karɓi ibadunmu, Amin.  Kusan mako biyu kenan ina magana akan tasirin azumin a jikin ɗan adam. Da fatan dai har yanzu kuna biye da ni. A rubutun satin da ya wuce, na kawo bayani game da yadda azumi…
Read More
Faɗuwar jirgi: Za mu ɗauki matakan kariya, inji Babban Hafsan Sojin Sama

Faɗuwar jirgi: Za mu ɗauki matakan kariya, inji Babban Hafsan Sojin Sama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babban Hafsan Sojin Sama na Nijeriya, Air Marshal Oladayo Amao ya kai ziyara wurin da hatsarin jirgin sojin sama mai ƙirar 401 ya faru don jajenta wa dangin mutane biyun da suka rasa rayukansu. Jirgin dai ya faɗo ne a Kaduna da yammacin Talata a wani sansanin sojan sama a Kaduna. a lokacin da ya ziyarci Kaduna ranar Larabar da ta gabata don jajenta wa iyalai, abokai da 'yan uwan matuqa jirgin saman da ya faɗo a Kaduna mai qirar 401 na makarantar koyon tuƙin jirgi, inda ya tabbatar da cewa an ɗauki dukkan…
Read More
Mataimakin Gwamnan Katsina ya ajiye muƙaminsa

Mataimakin Gwamnan Katsina ya ajiye muƙaminsa

Daga UMAR GARBA a Katsina Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu ya ajiye muƙaminsa na kwamishinan ma'aikatar aikin gona, muƙamin da yake riƙe da shi tun kimanin shekaru 7 da su ka wuce a bisa jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari. Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Musa Kalla ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai jiya Alhamis. Kalla ya bayyana cewar mataimakin gwamnan ya ajiye muƙamin nasa ne don bin umarnin sabuwar dokar zave da shugaban ƙasa ya saka wa hannu mai lamba 84(12) ta shekarar 2022 wadda aka gyara. Ya ƙara…
Read More