Editor

9513 Posts
Mace na neman takarar wakiltar Gusau da Tsafe a Majalisar Tarayya

Mace na neman takarar wakiltar Gusau da Tsafe a Majalisar Tarayya

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMMAD Wata mata kuma 'yar gidan sarauta, Hajiya Fatima Muazu Mayana, ta firto neman a zaɓe ta a zaɓen fidda gwani na Jam'iyyar APC, don ta wakilci Mazaɓar Gusau da Tsafe a Majalisar Wakilai ta Tarayya da ke Abuja. A cewar 'yar siyasar, "Ni haifaffiyar Gusau ce, ɗiyar Alhaji  Muazu Mayana. An haife ni ranar 3 ga Maris, 1982. Mu na da yawa, kuma gidanmu gidan sarauta ne mai dogon tarihi da ya kai shekaru 300. "Na yi karatun islamiya, na halarci Makarantar Ibrahim Gusau, na zarce zuwa Makarantar Sakandare ta Nana da ke Sokoto, sannan na yi…
Read More
Hisbah ta kama masu ƙwacen waya a masallaci a Kano

Hisbah ta kama masu ƙwacen waya a masallaci a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Hizba a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, ta kama wasu matasa takwas da ake zargi da ƙwacen waya a masalallacin al-Fur'an da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa da ke jihar. Kwamandan Hizba Sheikh Harun Ibn Sina, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata. Ya ce an kama waɗanda ake zargin da ranar Allah suna shan muggan ƙwayoyi da sauran ababen maye a kusa da masallacin. Ibn Sina ya bayyana ɗabi'ar matasan da haramtacciya da ba ta dace ba a wannan wata mai alfarma na Azumin Ramadan. Ya yi kira ga jama'a…
Read More
An cafke dillalin ƙwayar da ke da alaƙa da badaƙalar Abba Kyari

An cafke dillalin ƙwayar da ke da alaƙa da badaƙalar Abba Kyari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja NDLEA ta cafke Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, ƙasurgumin dillalin ƙwayoyi, wanda shi ne ummul-aba-isi na cinikin ƙwayar Tramadol ta Naira biliyan 3, wacce a ke tuhumar dakataccen ɗan sandan nan, Abba Kyari.  Ukatu, wanda shine Shugaban Rukunin Kamfanin Mallison, dubun sa ta cika ne bayan watanni a na fakon sa kuma ana ta kulli-kurciya da shi. An dai cafke shi ne a cikin jirgin sama a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a kan hanyarsa ta zuwa Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Afrilu. Binciken hukumar NDLEA ya bayyana cewa…
Read More
Bikin Sallah: Gwamnati ta ba da hutun gama-gari na yini 2

Bikin Sallah: Gwamnati ta ba da hutun gama-gari na yini 2

Daga BASHIR ISAH Domin bai wa al'ummar musulmin Nijeriya musamman ma'aikata, damar gudanar da shagulgulan bikin Sallah Ƙarama cikin nishaɗi da annashuwa, Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun gama-gari na yini biyu, Litini 2 zuwa Talata 3 ga watan Mayu, 2022. Sanarwar hakan na ƙunshe ne cikin sanarwa da ta fito ta hannun Babban Sakataren Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Shuaib Belgore a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola a ranar Alhamis. Ministan ya yaba wa ƙwazo da sadaukarwar da ma'aikatan gwamnati ke nunawa a bakin aiki wanda a cewarsa, hakan ta ƙara wa Nijeriya tagomashi a idon duniya. Sanarwar…
Read More
Shekara 52 na mulkin Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, sun ƙayatar – Buhari

Shekara 52 na mulkin Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, sun ƙayatar – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya jajenta wa gwamnatin Jihar Oyo da al'ummar jihar kan rasuwar Sarkin Yarabawa Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, ranar Juma'a. Buhari ya bayyana shekara 52 da sarkin ya shafe a karagar mulki da "masu ƙayatarwa ta hanyoyi da dama" cikin wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ƙasa Femi Adesina ya fitar. A ranar Asabar aka yi jana'izar sarkin a tsohon garin Oyo, inda aka binne shi a farfajiyar masarautarsa. Masarautar Oyo ta ce ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekara 83 bayan ya yi jinya a…
Read More
Ofishin Jakadancin Sin a Saliyo ya bai wa Musulmi kyautar kayan abinci

Ofishin Jakadancin Sin a Saliyo ya bai wa Musulmi kyautar kayan abinci

Daga CMG HAUSA Ofishin jakadancin Sin dake ƙasar Saliyo ya miƙa kyautar kayayyakin abinci ga al’ummar musulmi, albarkacin watan azumin Ramadan, da kuma bikin cikar ƙasar shekaru 61 da samun ’yancin kai, wanda ya fado ranar Laraba. Yayin mika kayan tallafin a jiya Alhamis a birnin Freetown, fadar mulkin ƙasar, jakadan Sin a Saliyo Hu Zhangliang ya ce, kayayyakin sun ƙunshi shinkafa, da man girki, da fulawa, da sikari. Ya ƙara da cewa, "Ina miƙa saƙon murna ga shugaba Julius Maada Bio, da gwamnatin Saliyo, da ɗaukacin al’ummar ƙasar, don gane da ƙoƙarinsu wajen bunƙasa fahimtar juna tsakanin mabiya addinai…
Read More
Hajojin Afirka na matuƙar jawo hankalin jama’ar ƙasar Sin

Hajojin Afirka na matuƙar jawo hankalin jama’ar ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA An buɗe bikin sayayyar hajojin Afirka ta yanar gizo karo na hudu a jiya, inda aka sayar da kayayyakin Afirka ga jama’ar ƙasar Sin ta yanar gizo. Manazarta suna ganin cewa, bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19, bikin ya sa ƙaimi ga yin sayayya a cikin kasar Sin, kana zai taimakawa raya haɗin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka. Tun daga shekarar 2019, an riga an yi irin wannan biki har sau uku, wanda ya jawo kamfanoni da masu kashe kuɗi da dama, waɗanda suka halarci bikin, kuma hakan ya sa ƙaimi ga yin…
Read More
Tunisiya da Sin sun yi bikin miƙa Kwalejin Diflomasiyya da Sin ta gina

Tunisiya da Sin sun yi bikin miƙa Kwalejin Diflomasiyya da Sin ta gina

Daga CMG HAUSA Ƙasashen Tunisiya da Sin sun gudanar da bikin miƙa sabuwar kwalejin diflomasiyya ta Tunisiya ta kafar intanet, wanda ƙasar Sin ta taimaka wajen ginawa. Mataimakin ministan kasuwancin ƙasar Sin, Qian Keming, ya bayyana a lokacin bikin cewa, duk da mummunan tasirin annobar COVID-19, ƙasar Sin ta yi nasarar kammala aikin mai matuƙar inganci kuma cikin hanzari, lamarin da ya bada gagarumar gudunmawa wajen zurfafa hulɗar dake tsakanin ƙasashen da kuma ƙarfafa hadin gwiwa a tsakanin ƙasashen biyu. Qian ya ce, Sin da Tunisia abokan hulɗar juna ne, wajen gina “shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya,” kuma ƙasar…
Read More
Ku nemi watan Shawwal ranar Asabra, Sarkin Musulmi ga Musulmin Nijeriya

Ku nemi watan Shawwal ranar Asabra, Sarkin Musulmi ga Musulmin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli na Harkokin Musuluncin Nijeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga Musulmin Nijeriya da su nemi jinjirin watan Shawwal a ranar Asabar, 30 ga Afrilu. Sarkin Musulmi ya buƙaci a nemi watan ne biyo bayan shawarar da Kwamitin Neman Wata (NMSC) ya bayar, kamar dai yadda darakta a NSCIA, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ya bayyana. Basaraken ya ce, duk inda aka samu ganin jinjirin watan Shawwal, a hanzarta a sanar da sarakuna da ‘yan kwamitin duban wata (NMSC) don a sanar da al’umma. A cewar Usman, “Muddin…
Read More
Har yanzu Ina nan daram a APC, inji Al-Makura

Har yanzu Ina nan daram a APC, inji Al-Makura

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, wanda ya fito takarar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, ya ce, har yanzu yana nan a jam’iyyarsa APC daram ba gudu ba ja da baya, duk da bai yi nasarar zama shugaban jam’iyyar na ƙasa ba.  Sanata Umaru Tanko Al-makura ya sanar da haka ne a wat takardar sanarwa na musamman ɗauke da sanya hannunsa wadda mai taimaka masa a fannin labarai, Mista Danjuma Joseph ya raba wa manema labarai a garin Lafiya, babban birnin jihar da wakilinmu ya samu kwafi.  Ya ce jim kaɗan da…
Read More