Editor

9513 Posts
Ƙaramar Sallah: Sojojin Nijeriya, ku ruvanya ƙoƙarinku na kawar da ‘yan ta’adda, ya ishe ni goron Sallah – Babban Hafsah Sojojin ƙasa

Ƙaramar Sallah: Sojojin Nijeriya, ku ruvanya ƙoƙarinku na kawar da ‘yan ta’adda, ya ishe ni goron Sallah – Babban Hafsah Sojojin ƙasa

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Hafsah Sojojin Ƙasan Nijeriya, (COAS), Laftana Janar Faruk Yahaya ya yi kira ga dukkan kwamandojin rundunar sojoji da su ƙara ruɓanya ƙoƙari wajen kawar da 'yan ta'adda. Inda ya ƙara da cewa, babban goron sallar da yake tsammani daga gare su shi ne, su kawar da ɓata-gari, masu garkuwa da mutane, da 'yan ta'adda masu yawan gaske. Sannan su ƙwato bindigogi da alburusai masu yawan gaske daga hannun ɓata-gari. Laftana Janar Faruk Yahaya shi ya bayyana haka a cikin saƙonsa na Barka da Sallah ga dukkan kafatanin jami'an sojin Nijeriya. Daraktan hulɗa da jama'a na…
Read More
NLC za ta shiga yajin aiki na ƙasa don nuna goyon baya ga ASUU

NLC za ta shiga yajin aiki na ƙasa don nuna goyon baya ga ASUU

Daga AMINA YUSUF ALI Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi wa gwwmnati kashedin cewa, za ta shiga yajin aiki na ƙasa, har tsahon kwanaki uku, idan har Twamnatin Tarayyar ba ta daina yin buris da buƙatun ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ba. Hakan yana ƙunshe ne a wata takardar bayani da kwamitin tafiyar da ƙungiyar NLC ya wallafa bayan wani taron da suka gudanar a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata a Abuja. a cikin takardar mai ɗauke da sa hannun Shugaban NLC na ƙasa, Ayuba Wabba da na Sakatarenta ba ƙasa, Emmanuel Ugboaja, NLC ta bayyana cewa, ta…
Read More
Da dumi-duminsa- Da yammacin yau Asabar Gawar Tahir Fadlallah za ta iso Kano

Da dumi-duminsa- Da yammacin yau Asabar Gawar Tahir Fadlallah za ta iso Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano A yau ne ake shirin aiwatar da Jazaizar babban dan kasuwan nan Tahir Fadlallah mamallakin Hotal ɗin Tahir da ya rasu jiya Juma'a, rasuwar Marigayin dai ta girgiza al'ummar Kano da ma duniya baki ɗaya, Marigayi Tahir Fadilallah ya rasu ne a wata cibiyar lafiya da ke birnin Beirut na kasar Labanon. Rahotanni sun ce tun a ranar 15 ga watan Afrilun da muke ciki ne aka kwantar da shi a sashen kulawa da wadanda ciwonsu ya yi tsanani na cibiyar, A wani sako da iyalan mamacin suka aikewa Freedom Radio sunce a na sa ran…
Read More
Harin jirgin ƙasa: Kanar Ɗangiwa ya nemi agajin ƙungiyoyi wajen ceto rayuka

Harin jirgin ƙasa: Kanar Ɗangiwa ya nemi agajin ƙungiyoyi wajen ceto rayuka

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Tsohon gwamnan mulkin soji na Jihar Kaduna, Kanal Abubakar Ɗangiwa Umar (ritaya), ya miƙa kokensa na bara ga al’ummomin duniya, musamman kwamitin ƙasa da ƙasa ta ‘Red Cross’ (ICRC) da ta taimaka ta shiga cikin shawarwari na wakilci da zummar ceto fasinjoji dake cikin jirgin ƙasa wanda yau kimanin wata guda kenan yana kan hanyar sa zuwa garin Kaduna ‘yan ta’adda suka yi masa farmaki. Wannan kira na tsohon gwamnan, ya biyo bayan kasancewar sa dangi kuma ɗan uwa ga wasu daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan da aka kai wa farmaki, kamar yadda ya zayyana…
Read More
Matar da aka sace a harin jirgin ƙasa ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Matar da aka sace a harin jirgin ƙasa ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗaya daga cikin fasinjojin da 'yan fashin daji suka sace daga jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.Tashar talabijin ta AriseTV, wadda ta wallafa wannan labarin, ta kuma ce wani ɗan uwan matar ne ya sanar da su haka. Ɗan uwa nata ya sanar cewa an kai wani likita wurin da ake riƙe da ita wanda ya taimaka mata wajen haihuwa. "Matar na da tsohon ciki wanda ya kai wata takwas yayin da aka sace ta da sauran gwamman…
Read More
Sojoji sun ceto mutum 848 daga masu garkuwa, yayin da ‘yan ta’adda 1,158 suka miƙa wuya a Borno – Hedikwatar Tsaro

Sojoji sun ceto mutum 848 daga masu garkuwa, yayin da ‘yan ta’adda 1,158 suka miƙa wuya a Borno – Hedikwatar Tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ) ta ce, sojojin Nijeriya sun samu nasarar kuɓutar da mutane 848 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su, kana sun kashe ‘yan ta’addan guda 85 sannan sun cafke 119, yayin da wasu ‘yan ta’addan sama da dubu 1,158 su da iyalansu suka mika wuya a tsawon shekaru uku da suka wuce a shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma. Daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar, Benard Onyeuko, shi ne ya shaida hakan a ranar Alhamis yayin da ya ke bayyana nasarorin da sojojin suka samu zuwa yanzu,…
Read More
Matasan Bade/Jakusko za su saya wa Hon. Kaitafi fom don yin takarar Majalisar Wakilai

Matasan Bade/Jakusko za su saya wa Hon. Kaitafi fom don yin takarar Majalisar Wakilai

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu  Biyo bayan kiran da matasan ƙananan hukumomin Bade/Jakusko a Jihar Yobe su ka yi na kira ga hadimin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya fito takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya, wanda hakan ya jawo a makonnin da suka gabata hadimin ajiye muƙamin shi, kamar yadda doka ta tanada, tare da bayyana gamsuwarsa kan wannan buƙata ta al'ummar yankin. Bugu da ƙari kuma, a wannan makon uwar jam'iyyar APC ta ƙasa ta shelanta fara sayar da fam ga yan takara a kowane mataki na neman tsaya wa takara, wanda ganin haka, matasan…
Read More
An gudanar da taron sasancin jam’iyyu a Nijeriya don samun fahimta

An gudanar da taron sasancin jam’iyyu a Nijeriya don samun fahimta

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano A ranar Talatar da ta gabata ne aka gudanar da taron sasanci ga wasu jam'iyyun siyasar Nijeriya don samun cikakkiyar madogara da za ta kawo cigaba a siyasar ƙasar. Taron wanda Gidauniyar Action Aids ta ɗauki nauyin gudanarwa ya samu halartar wakilan jam'iyyun siyasa daban-daban daga faɗin ƙasar nan, don ba matasa da mata damar yin shugabanci don su ma su samu tunani mai kyau. Wasu daga cikin jam'iyyun da suka halarci taron sun haɗa da jam'iyyar ADC da ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano Hon. Balarabe Rufa'i ya wakilta, sai jam'iyyar PRP Nasara…
Read More
NDLEA ta shafa jan fenti a gidaje da gine-ginen Abba Kyari a garin Maiduguri

NDLEA ta shafa jan fenti a gidaje da gine-ginen Abba Kyari a garin Maiduguri

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Shugaban Hukumar Hana Ta’ammali da Fatauci da Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya (NDLEA), Mohammed Buba Marwa, ya tabbatar da yin lambar shaida wa kadarorin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda, Abba Kyari a cikin garin Maiduguri, yana mai nuni da cewar, dukkan kadarorin da jami’in ɗan sandan ya tara ta hanyar haram za su kasance mallakar gwamnati. Da yake yin tsokaci kan wasu gidaje guda shida da wani katafaren kasuwar zamani da ya ƙunshi shaguna masu yawa mallakin Kyari, shugaban hukuma ya bayyana cewar, ba tare da yin nuni ga wani ɗan Nijeriya ma’abucin aikata ire-iren wannan laifi…
Read More
Aisha Buhari ta roƙi ’yan takarar Shugaban Ƙasa na APC su zaɓi mace a matsayin mataimakiya

Aisha Buhari ta roƙi ’yan takarar Shugaban Ƙasa na APC su zaɓi mace a matsayin mataimakiya

Daga AMINA YUSUF ALI A ƙarshen makon da ya gabata ne dai mai ɗakin Shugaban Ƙasar Nijeriya A'isha Buhari ta yi wani taron ganawa da masu zawarcin kujerar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023.  A yayin taron ne A'isha ta isar da roƙon ta ga 'yan takarar shugabancin ƙasar nan gabaɗaya da su zaɓi mata a matsayin abokan takarar tasu. 'Ya takarar Su ne, Bola Ahmad Tinubu, sai mataimakin shugaban ƙasa mai ci a yanzu, Farfesa Yemi Osinbajo, sai Dakta Chris Ngige da sauransu.  Chris Ngige ya yi kira ga takwarorinsa 'yan takara da su yi biyayya ga abinda A'isha Buhari…
Read More