01
May
An ɗauki kimanin wasu 'yan shekaru da iyakokin ƙasar nan ta ɓangaren Arewaci suke a garƙame, jim kaɗan bayan ɗaukar matakin yin hakan daga Shugaban ƙasa Mal. Muhammadu Buhari. A kuma makon da ya gabata ne, aka ga takardar sanarwar buɗe wasu daga cikin iyakokin da a da aka rufe su bisa dalilai kamar haka; 1- Don magance shigo da makamai zuwa ga 'yan ta'adda. 2- Don havaka tattakin arzikin cikin gida, da rage dogaro da kayan ƙetare. 3- Don inganta noma da samar da abincin da zai ishe mu har mu baiwa maƙofta, da sauran wasu dalilai dai gasu…
