Editor

9513 Posts
Kwamitin zakka ya raba kayan abinci karon farko ga mabuƙata a Lafiya

Kwamitin zakka ya raba kayan abinci karon farko ga mabuƙata a Lafiya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Sama da al’ummar Musulmi 100 da waɗanda ba Musulmi ba ne suka amfana da wani shiri na musamman na raba kayayyakin abinci da kuɗaɗe ga ɗimbin mabuƙatan dake Lafiya, Babban Birnin Jihar Nasarawa.  Taron rabon kayayyakin wanda aka gudanar a fadar Maimartaba Sarkin Lafiya, Alhaji Sidi Bage ranar Talata 26 ga watan Afrilun shekarar 2022 da ake ciki, ya samu halarar Maimartaba Sarkin da manyan ‘yan siyasa da ƙungiyoyin addinai da malamai da sauransu.  Da yake jawabi jim kaɗan kafin a fara rabon kayayyaki da kuɗaɗen, shugaban kwamitin zakka wanda ya gudanar da rabon,…
Read More
Sharhi: Amurka, ki mayar da kuɗin al’ummar Afghanistan

Sharhi: Amurka, ki mayar da kuɗin al’ummar Afghanistan

Daga CMG HAUSA Abdul Sabir dan ƙasar Afghanistan ne da ke rayuwa a birnin Kabul, babban birnin ƙasar, a kwanakin baya, ya je kasuwa don sayo wa yaransa busassun ‘ya’yan itatuwa da riguna domin Ƙaramar Sallah da za a fara nan da wasu kwanaki, amma ya koma gida cikin baƙin ciki, ya ce, “Ban iya sayen kome ba, ko riguna na kasa sayo wa yarana, dukkanin kayayyaki ciki har da busassun ‘ya’yan itatuwa, farashinsu sun wuce ƙarfinmu. Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasarmu takunkumi, tare da haramta mu yi amfani da kuɗaɗenmu.” Alkaluman ƙididdigar da hukumomin ƙasa da ƙasa suka fitar…
Read More
Muhyi Magaji Rimingado ya shaƙi iskar ‘yanci

Muhyi Magaji Rimingado ya shaƙi iskar ‘yanci

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Bayan tataɓurza da aka samu tsakanin tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado da lauyoyinsa da kuma lauyoyin gwamnati, daga ƙarshe dai an cimma matsaya inda aka bayar da Belinsa, 'Yan sanda ne dai suka gurfanar da Muhuyi a gaban kotu mai lamba 56 a ƙarƙashin mai Shari'a Aminu Gabari bayan da suka kamo shi a Abuja bayan da suke masa zargin gabatar da takardun lafiya na bogi ga majalisar dokokin Kano, tun a wancan lokacin anyi ta musayar yawu ta bayan fage, sannan har…
Read More
Wajibi ne Afirka ta yi shirin tunkarar yunwar da za ta kunno kai – Adesina

Wajibi ne Afirka ta yi shirin tunkarar yunwar da za ta kunno kai – Adesina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Bankin Bunƙasa Afirka (ADB), Akinwumi Adesina ya gargaɗi ƙasashen Afirka cewa su gaggauta bazama wajen bunƙasa noma, domin su samu abincin da za su tunkari yunwar da za ta buwayi Duniya, nan ba da daɗewa ba. Adesina ya ce, “tilas Afirka ta yi shirin tunkarar gagarimar yunwar da babu makawa sai ta darkako duniya.” Da ya ke amsa tambayoyin wasu fitattun manema labarai a Babban Taron Cibiyar Afirka ta Atlantic Council, ya ce ƙasashen Afirka da za su fi jin jiki su ne Waɗanda rikice-rikice da tashe-tashen hankula suka fi yi wa katutu,…
Read More
Elon Musk ya saye Tiwita kan fiye ninkin dukiyar Ɗangote

Elon Musk ya saye Tiwita kan fiye ninkin dukiyar Ɗangote

Daga AMINA YUSUF ALI Mutumin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, ya samu damar mallakar kamfanin Tiwita akan farashin Dalar Amurka biliyan $44, fiye da ninkin biyu na dukkan arzikin da ma fi kuxi a Afirka, Aliko Dyangote ya mallaka.  Kamar yadda jadawalin biloniyoyi na jaridar Ingilishi ta Bloomberg ya bayyana, a yanzu haka dai ƙarfin arzikinsa da ke Amurka biliyan $20.4 ne. Kuma shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Afrika, kuma na 72 a Duniya. A hannun guda kuma shi Elon Musk shi ne na ɗaya a arziki a Duniya kuma ƙarfin arzikinsa…
Read More
Umurnin Buhari na sake buɗe iyakoki

Umurnin Buhari na sake buɗe iyakoki

A yau ma shawara ce wacce ba bu tilas a ciki. A makon jiya ne umurni ya zo daga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a kan sake buɗe wasu iyakokin ƙasa wadda ta raba iyakokin jamhuriyar Nijer da ƙasarmu Nijeriya. Tun rufe ta wasu ke ta ƙorafe-ƙorafe iri iri tare da fatan a sake buɗe ta. An ce a sake buɗe ta amma har yau wasu na cewa siyasa ce. Tabbas iya ma mutane sai Allah amma kar mu manta duk abinda shugaba zai aiwatas ba dole yai ma kowa daidai ba kuma ita doka idan ba a binta kai da…
Read More
Manema labarai bakwai suka rasa rayukansu tsakanin 2015 zuwa 2022 – Gidauniyar MFWA

Manema labarai bakwai suka rasa rayukansu tsakanin 2015 zuwa 2022 – Gidauniyar MFWA

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Manema labarai bakwai ne suka halaka, yayin da aka ci zarafin waɗansu guda 300 a cikin tashin-tashina da suka jivanci ‘yan jarida guda 500 a Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa Afrilun 2022, kamar yadda rahoton Gidauniyar Kafafen Watsa Labarai ta Afrika ta Yamma (MFWA) da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) suka fitar. Zamani ko lokacin wannan nazari ya haɗa da wa’adin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, la’akari da cewar wa’adin mulkin sa ya fara ne tun daga shekara ta 2015, domin ya sava rantsuwar kama aiki a watan Mayu na wancan shekarar. Rahoton, wanda aka…
Read More
A ina masallacin Al’aƙsa ya ke?

A ina masallacin Al’aƙsa ya ke?

A wani yanayi da ya ke faruwa a gabas maso yammacin Asiya, wanda ana samun rashin jituwa tsakanin ƙasashen Larabawa ta Falastin da kuma Yahudawa an Isra'ila. Mutane da dama suna rasa rayuwarsu, musamman yara ƙanana da mata, da kuma tsofofi da likitoci sai kuma ’yan jaridu. Massallcin Al'aƙsa an gina shi ne akan wani tsauni a Jerusalem ko Ƙuds da Larabci. Wuri na uku kenan a duniya da suka fi tsariki a duniyar musulunci. Wanda daga Ƙa'aba da ke Makka sai kuma Masallacin Annabi (S) da ke birnin Madina. Al'aƙsa yana kudu maso gabashin tsohuwar birnin Kudus. Ana wa…
Read More
Zan bada gudunmuwa wajen kawo cigaban ‘yan Arewa mazauna Legas – Hajiya Amina

Zan bada gudunmuwa wajen kawo cigaban ‘yan Arewa mazauna Legas – Hajiya Amina

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugabar mata ta ƙungiyar 'Arewa Community' da ke jagorantar shiyya yammacin Legas, Hajiya Amina ta sha alwashin yin iyakacin ƙoƙarinta tare da bada gudunmuwa wajen kawo cigaba mai ma'ana ga al'ummar Arewacin Nijeriya mazauna Jihar Legas. Hajiya Amina ta tabbatar da hakan ne yayin ziyarar gaisuwar azumi da ta kai wa shugaban ƙungiyar na jihar, Alhaji Sa'adu Yusuf Dandare Gulma a ofishin sa ranar Lahadin da ta gabata. Ta ce za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta haɗa kan al'ummar shiyyar da take shugabanta, musamman wajen kawo zaman lafiya da fahimtar juna a…
Read More
Aisha Buhari ta yi wa ’yan Zamfara addu’a

Aisha Buhari ta yi wa ’yan Zamfara addu’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Uwargidan Shugaban Nijeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wani saƙo a shafinta na Facebook inda a ciki ta yi wa al'ummar Jihar Zamfara taddu'ar zaman lafiya. Aisha Buhari ta wallafa saƙon ne da misalin ƙarfe 12:09 na daren Laraba, inda ta roƙi Allah ya samar wa mutanen jihar da sauran 'yan ƙasar mafita daga matsalar tsaron da ta addabe ta, musamman a lokacin da Musulmi ke raya dare domin neman falalar Lailatul Ƙadri: "Allah ya fitar da mu da mutanen Jihar Zamfara daga chikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Ƙadri, Ameen!" Baya ga saƙon,…
Read More