Editor

9513 Posts
Bikin sallah: ’Yan ta’adda na shirin tada bomabomai – DSS

Bikin sallah: ’Yan ta’adda na shirin tada bomabomai – DSS

•Za su kai hari a masallatai da wuraren shaƙatawa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A daidai lokacin da ya rage kwana kaɗan al'ummar Musulmi su gudanar da shagulgulan bikin Ƙaramar Sallah a Nijeriya, Hukumar 'Yan Sandan Farin Kaya (DSS) ta ankarar da 'yan Nijeriya kan wani makirci da suka gano da wasu ɓatagari ke shirin aikatawa a lokacin bukukuwan sallah da bayan sallah. Hukumar DSS ɗin da kanta ta ce ta gano cewa, wasu miyagu suna haɗin gwiwa domin saka bama-bamai a wuraren ibada, wuraren shaƙatawa da wasu gine-gine masu muhimmanci yayin bikin sallah. Don haka hukumar ta buƙaci…
Read More
Sallah: Masu sayar da kaji a Kaduna sun koka da rashin ciniki

Sallah: Masu sayar da kaji a Kaduna sun koka da rashin ciniki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu daga cikin masu sayar da kaji, talo-talo da agwagi a Kaduna sun koka kan rashin cinikin kajin gabanin bikin ƙaramar Sallah ta bana. Masu sayar da kajin sun nuna damuwarsu a hira mabanbanta da Kamfanin Dllancin Labarai na Ƙasa (NAN) ta yi da su a ranar Talata a Kaduna. Sun ce lamarin abin damuwa ne matuƙa, duk da cewa suna da kyakkyawan fatan ganin canji da zarar ma'aikata sun samu albashin watan Afrilu. Wakilin NAN wanda ya ziyarci fitacciyar kasuwar sayar da kaji a Kantin Koli a Babbar Kasuwar Kaduna, ya hangi mutane…
Read More
Ƙaramar Sallah: Yadda jama’a ke kokawa a Gombe

Ƙaramar Sallah: Yadda jama’a ke kokawa a Gombe

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Yayin da ake shirin yin ƙaramar sallah a jibi Lahadi ko kuma Litinin idan Allah ya kaimu, al’ummar kuma sai kururuwar rashin wadata suke ta fama da shi: “Mu dai wannan sallah sai dai a hankali. za mu dai gode wa Allah kawai da Ya kawo mu lafiya. Amma mu talakawa, a wurin mu ba mu da wata, gwamnati ta cuce mu”,  a ta bakin wani bawan Allah kenan a cikin garin Gombe a lokacin da wakilin mu ya yi zagaye don jin yadda jama’a suke shirin sallah ƙarama. Wani malamin makarantar LEA dake Unguwar…
Read More
Gwamnan Zamfara ya warware rawanin sarakunan Zurmi da Ɗansadau saboda ta’addanci

Gwamnan Zamfara ya warware rawanin sarakunan Zurmi da Ɗansadau saboda ta’addanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello, Matawallen Muradun, ya sanar da sauke wasu manyan sarakunan jihar guda biyu da Magajin Gari guda, saboda samun su da hannu wajen ayyukan ta’addancin da suka addabe jihar. Sanarwar da Gwamnan Jihar Bello Matawalle ya gabatar ta ce, an sauke Sarkin Zurmi Atiku Abubakar da na Ɗansadau Hussaini Umar saboda yadda rahotan binciken da aka yi ya tabbatar da laifi akan su. Sanarwar da ke ɗauke da sanya hannu Zailani Bappa, mai magana da yawun gwamnan ta ce an kuma sauke Suleiman Ibrahim Ɗanyabi a matsayin Magajin Garin Birni…
Read More
Babu abinda ya haɗa kuɗin fom na APC da rashawa – Abdullahi Adamu

Babu abinda ya haɗa kuɗin fom na APC da rashawa – Abdullahi Adamu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa babu abinda ya haɗa kuɗin fom ɗin takarar APC da rashawa. Adamu ya bayyana hakan ne cikin wata hirar bidiyo da Muryar Amurka ta yi da shi, inda yake mayar da martani kan cece-kucen da mutane ke yi dangane da ɗan karen tsadar da fom ɗin shiga takarar neman kujeru a jam'iyyar APC. A martanin shugaban, ya ce 'kujerar Shugaban Ƙasa ba abin wasa ba ce, ba kuma kujerar sarkin gari ba ne." Ya ce duk ɗan takarar da ba shi da masoyan…
Read More
Fom ɗin Naira miliyan 100 ba na sarkin ƙauye ba ne

Fom ɗin Naira miliyan 100 ba na sarkin ƙauye ba ne

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Gaskiya ne an shiga kakar siyasar zaɓen 2023 a Nijeriya inda kullum za aka iya jin sabon abu kama daga batun sauya sheƙa, fitowar 'yan takara, caccakar juna da ma batun Kudu da Arewa. Kuma ai ma abin da ya fi ɗaukar hankali zuwa yanzu shi ne zare Naira miliyan 100 don sayen fom ɗin neman tikitin takarar shugabancin Nijeriya a inuwar jam’iyyar APC mai gwamnatin taraiya. Tun da a ke a tarihin siyasar Nijeriya ba a taɓa samun fom mai tsadar wannan ba. Kazalika hakan ma ya fito a jam’iyya mai mallakar shugaba Buhari wanda…
Read More
Damina: Uwa ma-ba-da-mama

Damina: Uwa ma-ba-da-mama

Bahaushe na cewa ‘Damina Uwar Albarka!’ Wannan magana ta Malam Bahaushe haka ta ke, domin a lokacin damina ne ake samun albarkatu masu yawa, musamman a fannin abinci, a lokacin ne ake samun abincin da ake ci, wanda kuma abinci ne jigon rayuwar kowane halitta. Kuma alhamdu lillahi, ya zuwa yanzu za mu iya cewa damina ta kankama, sai dai fatan Allah ba mu dacewa. Duk da cewa a wannan zamani na damina, lokaci ne da ake samun albarkatu masu yawa, to haka kuma akwai wasu bala’o’i da sukan samu ɗan adam, waɗanda a lokuta da dama ma har abin…
Read More
Osinbajo ya yi wa Tinubu layar zana a taron buɗa bakin da Aisha Buhari ta shirya

Osinbajo ya yi wa Tinubu layar zana a taron buɗa bakin da Aisha Buhari ta shirya

Daga AMINA YUSUF ALI Mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wasan vuya da Asiwsju Bola Ahmad Tinubu a daren ranar Asabar ɗin da ta gabata. Wato cikin dabara ya ƙi amsa gayyatar taron buɗe bakin azumin da Matar Shugaban ƙasa A'isha Buhari ta gayyace su. Saboda gudun haɗuwa da Tinubu.  Tinubu, da Dave Umahi da Chris Ngige, da sauran 'yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC  sun halarci taron wanda 'yan takarar  PDP, Atiku Abubakar, Peter Obi da Bukola Saraki suka yi buris da shi. Kodayake, Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad shi ya kawar da gabar ya halarci…
Read More
Tsaro: ’Yan sanda sun kulle Mammy Market a Damaturu

Tsaro: ’Yan sanda sun kulle Mammy Market a Damaturu

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Sakamakon ci gaba da barazanar kai sabbin hare-hare a wasu sassan jihar Yobe, ranar Talata rundunar 'yan sanda a jihar sun ɗauki matakin kulle kasuwar sayar da barasa, wadda aka fi sani da Mammy Market a babban birnin jihar dake Damaturu, matakin da ke da nasaba da kaucewa salwantar da rayuka dangane da shirin da mayaqan Boko Haram/ISWAP ke yi na kai sabbin farmaki. Wannan wurin sayar da giya ta 'yan sanda kuma ita ce kasuwar barasa mafi girma a birnin, wuri ne wanda ake ginin zai iya tsole idon mayaƙan bisa ga yadda kai…
Read More
Hukumar Kwastom ta buɗe iyakar Kamba a Jihar Kebbi

Hukumar Kwastom ta buɗe iyakar Kamba a Jihar Kebbi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kwastom ta Ƙasa, NCS, a Litinin ta buɗe kan iyakar Kamba da ta haɗa Tarayyar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar akan hanyar Kebbi a hukumance. Gwamnatin Tarayya, ta wata sanarwa da hukumar NCS ta bayar a ranar Juma’a ta bada umarnin sake buɗe ofisoshin kan iyaka a Idiroko (Ogun); Jibiya (Katsina) Kamba (Kebbi) da kuma Ikom (Kuros Ribas). Gwamnati ta rufe manyan kan iyakokin ƙasar ne a wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile yaɗuwar annobar Korona da daƙile fasa-ƙauri domin bunƙasa noman shinkafa da sauran amfanin gona na cikin gida. Yayin da ya ke jawabi…
Read More