02
May
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano ta haramta liƙa hotuna da ɗaga tutocin siyasa a lokacin bukukuwan ƙaramar Sallah. Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya bayyana hakan ta cikin saƙonsa na barka da Sallah ga al’ummar Kano. Ta cikin saƙon barka da Sallar da Gwamnan ya fitar ta hannun Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Muhammad Garba, ya ce daga yanzu an hana saka tutoci, ko allunan 'yan siyasa yayin sallar idi da sauran bukukuwan sallah domin kauce wa rikici. Ya ce, Sallar idi ibada ce muhimmiya bayan azumin Ramadana da ake bin bayanta da bukukuwan bajakolin…
