Editor

9513 Posts
Bikin sayar da kayayyakin Afirka ya nuna burin Sin na tabbatar da cin moriyar juna

Bikin sayar da kayayyakin Afirka ya nuna burin Sin na tabbatar da cin moriyar juna

Daga CMG HAUSA Wasu mintuna 5 da suka wuce, na yi kai-komo tsakanin wasu nau’o'in waken gahawa na Kenya, da Habasha, da Rwanda, kafin na zaɓi ɗaya daga cikin su, na zabi waken da aka samar da shi daga yankin Muranga na ƙasar Kenya, don ya zama kyautar ƙaramar sallah, da zan ba kaina. Na sayi waken ne ta wani dandalin sayar da kayayyaki ta yanar gizo na ƙasar Sin. A kwanakin nan, ana gudanar da “bikin sayar da ingantattun kayayyakin ƙasashen Afirka” a dandali daban daban na ƙasar Sin. Kawai na danna wani link da ya bayyana a wayar…
Read More
Ranar Ƙwadago: Xi ya buƙaci ma’aikata da su ƙara zage damtse wajen cimma manyan nasarori

Ranar Ƙwadago: Xi ya buƙaci ma’aikata da su ƙara zage damtse wajen cimma manyan nasarori

Dag CMG HAUSA Albarkacin bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa a duk ranar 1 ga watan Mayu, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon gaisuwa da fatan alheri ga daukacin sassan ‘yan ƙwadagon ƙasar Sin. Cikin sama da shekaru 10 da suka gabata, shugaba Xi ya sha jinjinawa ƙwazon ma’aikata, dake kan gaba wajen ba da hidimomin da al’ummar Sinawa ke matuƙar buƙata. Mai fassarawa: Saminu
Read More
Gare ku mata

Gare ku mata

Daga ABDULLAHI YAHAYA MAIZARE Duk fushin da za ki yi da mijinki kada ki sake ki yi masa waɗannan abubuwan: Akwai matan da su ke wuce gona da iri a lokacin da suka samu matsala da mazansu. Dole ne a riƙa samun matsaloli a tsakanin ma'aurata, amma duk irin matsalar da za ki samu da mijinki kada ki kuskura ki masa waɗannan halayen: Duk irin matsalar da za ta faru tsakaninki da mijinki kada ki shigo da raini a tsakaninku. Ki ci gaba da masa biyayya koda ki na fushi da shi. Amma shigowa da raini ko ƙasƙanta shi saboda…
Read More
Khalifa Muhammadu Sanusi ya fitar da mutane 59 daga kurkuku a Kano

Khalifa Muhammadu Sanusi ya fitar da mutane 59 daga kurkuku a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gidauniyar Muhammadu Sanusi ll ta fitar da mutane 59 daga gidan yari, waɗanda su ka kasa biyan tara da kuma waɗanda a ka ɗaure su saboda basussuka da a ke binsu. Da yake zantawa da manema labarai a Laraba, Shugaban gudanarwar gidauniyar, Mujtaba Abba, ya ce Khalifa ya biya kuɗaɗen tarar da na basukan mutane 59 ɗin, kimanin Naira miliyan 16,820,370. Abba ya yi bayani cewa Khalifa ya bada umarnin a biya wa ɗaurarru 26 kuɗaɗen tara da basuka a gidan yarin Kurmawa, wanda adadin kuɗin ya kama Naira 4,466,500. A cewar shugaban gudanarwar, Khalifa…
Read More
Akwai buƙatar gwamnati ta sanar wa jama’a sharuɗɗan buɗe iyakar ƙasa da ta yi – Hon. Wada

Akwai buƙatar gwamnati ta sanar wa jama’a sharuɗɗan buɗe iyakar ƙasa da ta yi – Hon. Wada

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano An buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta bayyana ƙa'idojin da ya kamata al'ummar ƙasar nan su sani dangane da sake buɗe bodojin da ta bayyana ta yi cikin kwanakin nan. Wannan kiran ya fito ne daga bakin babban ɗan kasuwa kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan 'yan siyasa a Ƙaramar Hukumar Nasarawa dake Jihar Kano, wato Hon. Bashir Wada, shugaban kasuwar Sabuwar Singa dake kan titin 'Yan-kaba cikin garin Kano a wata zantawa da manema labarai. Hon. Bashir ya cigaba da shaida wa manema labarai cewa lallai wannan yunƙuri na Gwamnatin Tarayya abu ne mai kyau…
Read More
’Yan sanda sun yi wa Kwamandan ‘Civil Defense’ ɗanyen aiki har sun kashe dogarinsa

’Yan sanda sun yi wa Kwamandan ‘Civil Defense’ ɗanyen aiki har sun kashe dogarinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan sanda a Jihar Imo sun yi wa Kwamandan Civil Defence lilis, sa'ilin da wani rikici ya ɓarke tsakanin 'yan sandan da jami'an NSCDC sakamakon rashin jituwan da ya wakana tsakanin jami'an hukumomin tsaron biyu.  Manhaja ta ruwaito cewa 'yan sandan sun kai farmaki hedikwatar NSCDC da ke Owerri, ranar Litinin, kuma suka yi wa kwamandansu zindir kana suka kashe dogarinsa.  Rahoton ya ƙara da cewa rikicin ya fara lokacin da wani ɗan sanda sanye da kayan gida ya tare hanya, ya hana Kwamandan NSCDC wucewa yayin da yake hanyar komawa Owerri daga Abacheke,…
Read More
Tsaro: Za a fara ɗaure masu biyan ‘yan bindiga kuɗin fansa – Majalisa

Tsaro: Za a fara ɗaure masu biyan ‘yan bindiga kuɗin fansa – Majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattawan Nijeriya ta zartar da wani ƙuduri da zai tabbatar da hukuncin ɗaurin aƙalla shekara goma sha biyar ga masu biyan kuɗin fansa don kuɓutar da wani da aka sace. Ƙudurin dokar ya kuma amince da hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin satar mutane. Ƙudurin, wanda gyaran fuska ne ga dokar yaƙi da ta'addanci, ya ƙunshi ɗaurin rai-da-rai ga masu satar mutanen da kotu ta kama da laifi, kuma matuƙar satar ta kai ga mutuwar mutum, masu laifin za su fuskanci hukuncin kisa. Ɓangaren…
Read More
Yadda muke ƙoƙarin sauya halayyar ’yan daba a Jos – Malam Nura Tela

Yadda muke ƙoƙarin sauya halayyar ’yan daba a Jos – Malam Nura Tela

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato, yana ɗaya daga cikin manyan biranen arewacin Nijeriya, waɗanda suke fama da matsalar taɓarɓarewar tsaro, wanda ya shafi yadda ƙungiyoyin matasa ’yan daba suke ɗaukar makamai suna shiga unguwanni suna sare-saren kan-mai-uwa-da-wabi da ƙwacen wayoyi. Yawaitar wannan masifa ne ta zaburar da mutane irin su Malam Nura Alhassan Abdullahi, wanda aka fi sani da Malam Nura Tela, Shugaban Ƙungiyar 'Jos Peace Vanguard', tare da masu ra'ayi irin nasa suka tashi-tsaye, don ganin yaran da suke wannan aika-aika a garin, sun dawo kan hanya da samar da tsaro a cikin al'umma.…
Read More
Jahilai ke ganin kuskuren shigar malamai siyasa – Sheikh Ibrahim Khalil

Jahilai ke ganin kuskuren shigar malamai siyasa – Sheikh Ibrahim Khalil

Daga MUHAMMADU MUJTABA USMAN a Kano Blueprint Manhaja ta samu zarafin zantawa da Shugaban Majalisar Malamai na Arewa, Sheikh Ibrahim Khalil akan wasu muhimman alamura da suka shafi siyasa kai-tsaye, har ma da addini da kuma dalilinsa na daɗewa bai je umara ba da kuma dalilinsa na neman zama Gwamnan Jihar Kano a jamiyarsa ta ADC a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023. Sannan kuma ya faɗi dalilin da ya sa ake ce wa mutanan kirki su shigo siyasa da gaskiyar lamarin da sauran batutuwa da wakilinmu, Muhamadu Mujitaba bin Usman, ya tattauna da shehin malamin a gidansa da ke…
Read More
Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya ‘Barka Da Sallah’

Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya ‘Barka Da Sallah’

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa saƙon barka da sallah ga ɗaukacin al'ummar musulmin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya. Buhari ya miƙa saƙon nasa ne ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, yana mai cewa bayan kammala azumin bana ana da dukkan wata dama na maraba da bikin sallah. Haka nan, Shugaban ya bai wa 'yan Nijeriya tabbacin "yaƙin da ake yi da ɓatagarin da suka fake da Musulunci suna cutar da jama'a ya kusa zuwa ƙarshe." Ya ce, “Yaƙi ne mai wahala wanda ya ɗauki tsawon lokaci, kuma a ƙarshe mun soma ganin nasara.…
Read More