Editor

9513 Posts
Matashi ya kammala digirinsa bayan shekara 10

Matashi ya kammala digirinsa bayan shekara 10

Daga WAKILINMU Wani bawan Allah mai suna Abba Abubakar Santalee ya bayyana farin cikinsa yayin da ya kammala karatun digirin farko a jami’ar ABU Zaria. Abba Abubakar Santalee ya fito ya bayyana wannan abin alheri ne a shafinsa na Tuwita a ranar Talata. Inda farin cikin Pharm. Abba Abubakar Santalee ya ke shi ne, ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin samun takardar shaidar Digiri a wannan babbar jami’a. Da ya ke bayanin abin da ya sa ya daɗe bai gama karatun ba, Abba Abubakar Santalee ya ce, yajin-aikin aungiyar ASUU ya vata masa aƙalla shekara ɗaya. Haka zalika, Abba Santalee…
Read More
Mutumin da ya hau babur daga Landan zuwa Legas ya shigo Afrika

Mutumin da ya hau babur daga Landan zuwa Legas ya shigo Afrika

Wani ɗan Nijeriya mai suna Kunle Adeyanju wanda ya ke tattaki daga Landan zuwa Lagas, ya isa nahiyar Afrika. Mutumin wanda yana tafiyar ne a kan babur ɗinsa ya sanar da hakan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Tuwita a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu. Da ya ke sanar da isowarsa nahiyar Afrika, jarumin mazan ya wallafa wani hotonsa kusa da wata alama da ke nuna cewa lallai yana kusa da birnin Casablabca na ƙasar Moroko. Moroko na arewacin Afrika. Wannan ce rana ta shida da fara tafiyar tasa, kasancewar ya fara ta ne a ranar…
Read More
Lantarki ta tsalo matashi har lahira yana tsaka da cajin wayarsa

Lantarki ta tsalo matashi har lahira yana tsaka da cajin wayarsa

Wani matashin sauryai ɗan kimanin shekara 18, Chibuike Emmanuel, ya rasa rayuwarsa sanadin wutar lantarki a yankin Ozoro, ƙaramar hukumar Isoko North, jihar Delta. Rahotanni sun bayyana cewa, wutar ta lantarke matashin ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Talata yayin da ya ke cajin wayarsa ƙirar iPhone 8 a tushen wayar lantarkin. A cewar wata majiya ranar Laraba, ƙawar mahaifiyar matashin yaron ta kai rahoton abin da ya afku ofishin 'yan sanda, wacce ta ɗauko mamacin daga jihar Legas domin ya yi hutunsa a tare da su. Rahoto ya nuna cewa, matashin ya kwanta a kan siminti a…
Read More
Mutum uku sun rasa rayukansu kan wata tsaleliyar budurwa a Kwara

Mutum uku sun rasa rayukansu kan wata tsaleliyar budurwa a Kwara

Daga WAKILINMU Mutum uku sun rasa rayuwarsu, wasu da dama sun jikkata a ƙaramar hukumar Offa ta Jihar Kwara sanadin wata budurwa. Rahotanni sun nuna cewa, ƙungiyoyin ’yan daba biyu ne suka gwabza da juna biyo bayan wani saɓani da suka samu kan mace. Rahoto ya nuna cewa, rikicin ya soma ne ranar Asabar. Wani mazaunin yankin, Alhaji Abdurrahman, ya shaida wa manema labarai cewa, rikicin ya kaure ne tsakanin ’yan daban tsagin Isale Oja da na tsagin Oja Oba a Offa.A cewarsa, shugaban ɗaya daga cikin ƙungiyar ’yan daban ne ya kwace budurwan mamban ɗaya ƙungiyar 'yan daban da…
Read More
Abubuwan da suke yi wa zaman aure ƙamshin mutuwa!

Abubuwan da suke yi wa zaman aure ƙamshin mutuwa!

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a filin zamantakewa na wannan makon. Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Manhaja!  A wannan mako muna tafe da alamommin da suke nuna cewa aurenku yana da masassarar mutuwa, wato kwanansa yana gab da ƙarewa.  Kamar yadda Hausawa kan ce aure rai ne da shi, duk ranar da wa'adin ajalinsa ya zo, labudda ba ya ƙara kwana. Wannan batu haka yake. Idan ajalin aure ya zo, za ka ga alamomi suna ta nunawa. An san dole da ma a zaman aure zama ne na zo mu zauna, zo mu saɓa…
Read More
Kwamishinan Zamfara ya yi murabus

Kwamishinan Zamfara ya yi murabus

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Zamfara kuma babban limamin masallacin Juma'a na Muslim Foundation da ke Gusau, Dr. Sheik Tukur Sani Jangebe ya yi murabus daga muƙaminsa. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 1 ga Mayu, 2022 wacce ya sanya wa hannu kuma Blueprint Manhaja ta mallaki kwafi ranar Litinin a Gusau. Sheik Jangebe ya miƙa godiyarsa ga Gwamna Bello Mohammed Matawalle bisa damar da aka ba shi na zama ɗaya daga cikin mambobin majalisar zartarwar jihar na tsawon shekaru uku. Sai dai, Dr. Sheik Tukur Sani Jangebe…
Read More
Nollywood ta shirya finafinai 541 a wata uku – Hukumar Tace finafinai

Nollywood ta shirya finafinai 541 a wata uku – Hukumar Tace finafinai

Daga SANI AHMAD GIWA Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa, NFVCB, ta ce, hukumar ta karɓa tare da tace finafinai 541 da masana’antar finafinan Nijeriya ta Nollywood ta shirya a farkon kwata ta shekarar 2022. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Adedayo Thomas, Babban Daraktan NFVCB ya fitar a Juma’ar makon jiya a Abuja. Ya ce sashen Tace Finafinai da Tantancewa na hukumar ne suka fitar da wannan ƙididdiga a cikin rahotonta na kwata ta farko na shekarar bana. Thomas ya ce, rahoton ya ɗauki dukkan finafinan da aka miƙa wa hukumar daga sassan ƙasar. Ya…
Read More
Na bai wa Ado Gidan Dabino kundin warware matsalolin Kannywood – Farfesa Abdalla

Na bai wa Ado Gidan Dabino kundin warware matsalolin Kannywood – Farfesa Abdalla

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), reshen Jihar Kano, ta gabatar da taron shan ruwan azumi da kuma ƙaddamar da sabbin shugabanni na Jihar Kano da ya gudana a Kannywood TV a Kano. A jawabinsa, Farfesa Abdullahi Uba Adamu, wanda shine baƙo na musamman a wurin, ya ce, a ra'ayinsa da ma babu wanda ya fi cancanta da ya riƙi shugabancin Kannywood, kamar Ado Ahmad Gidan Dabino, yana mai cewa, wannan ne dalilin da ya sa ya ba shi wani kundi, wanda idan ya bi…
Read More
Sharhin fim ɗin ‘Lamba’

Sharhin fim ɗin ‘Lamba’

Daga HABIBU MA'ARUF ABDU  Shahararren kamfanin shirya finafinai na Maishadda Global Resources Limited, wanda a baya-bayan nan ya zama kamfani mafi tasiri a masana’antar Kannywood, ya shirya finafinan barkwanci da dama tare da fitaccen Darakta, Ali Gumzak. Fim ɗinsu na ƙarshe "Ka yi na yi" shi ne wanda ya fi kowanne fim tattara kuɗi yayin haska shi a Sinima a shekarar da ta gabata.  A wannan sabuwar shekarar ma, sai ga shi sun shigo da wani fim ɗin barkwancin mai suna Lamba. Fim ne wanda, cikin barkwanci, ya ƙalubalanci yadda jama'a suke yin rayuwar ƙarya musamman a kafofin soshiyal midiya.…
Read More
Me ya sa ake rububin zuba jari a kasuwannin Sin duk da fama da annoba?

Me ya sa ake rububin zuba jari a kasuwannin Sin duk da fama da annoba?

Daga CMG HAUSA Masu hikimar magana na cewa, “ba a fafe gora a ranar tafiya,” kuma a wani ƙaulin akan ce, “tun ran gini ran zane.” Duk da irin yadda ake fama da yaɗuwar annobar COVID-19 a wasu daga cikin yankuna da biranen ƙasar Sin, ciki, har da ɗaya daga cikin manyan biranen kasuwancin ƙasar wato Shanghai, amma wani abin ban sha’awa shine, yadda ake ƙara samun masu sha’awar zuba jari dake ƙara rububin juba jarinsu a ƙasar. Alal misali, kamar yadda wani kwararren masanin harkokin kuɗi da aikin banki na ƙasar Swissland, Fiorenzo Manganiello ya bayyana cewa, kyakkyawar makomar…
Read More