27
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A farkon shekara ta 1496 miladiyya, Sarkin kano Muhammad Rumfa ya yi waɗansu baƙin fataken Turawa da suka ɓullo daga Kumasi ta ƙasar Gwanja (Ghana) can yamma da Ilorin.A harshen Hausa muna kiransu da suna Patoki, amma ainihin sunansu Portuguese, ma’ana mutanen ƙasar Portugal. Babban cinikin waɗannan Turawan shi ne fataucin bayi, sune Turawan farko da suka kawo gyaɗa garin Kano. Su kan sayi bayi maza da mata a kasuwa. Su kuma sukan sayarwa da Kanawa gyada. Yayin da suka kammala sayar da gyaɗar tasu, sai suka shirya bayin da suka saya, suka tashi suka koma…
